ย  ย  NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 155 of 172

magana sai kuma ta fasa, gani yai idanunta sun fara cicikowa yace "Menene kuma?" Ta fara kokarin shanye kwallar tace "ba saboda fitar dakai bane wani yama haka? Ko dad......" Kara jawota yai ya rungume yace "ki bani abinci, yunwa nake ji." Shiru tai cikin rada yace "mu biyu ne a gidan, na dauka Sageer zai shigo sai naga ya juya, kinga yau sai mu....." Sai ya kara matsowa kusa da kunneta yace "sai a biyani bashina duka." Dagowa tai ta kalleshi, kamar zatai magana kuma sai yaga tayi murmushi tace "ka dainajin yunwar ne?" Cikin shagwaba yace "ina fa? Ai ni yau a nan ma za'a bani indai anaso inci." Ya fada yana nuna bakinsa. Dariya tai, ya ja hannunta suka nufi kasa. #OneLuv๐Ÿ’•๐Ÿ—ฏ *JALILAH* ๐Ÿ—ฏ Written By : *AYUSHER MUHD* Wattpad: *Ayusher Muhd* *HASKE WRITER'S ASSOCIATION* *74* Haka ya jawo hannunta har kasa, dinning ya nufa ya zauna akan kujera yace "anan." Kai ta daga alamar to sannan ta nufi kitchen, tana zuba abinci tana tunanin abinda ya faru har aka bigemai baki dan kana gani kasan ba faduwa bane. Haka ta zuba ta nufi dinning, tana ajiye wa ya dagata ya daurata akan saman dinning din inda yake, kallansa tai tana dariya tace "karfa nai barna, inya fashe fa yaji nauyi." Baki ya bude alamar mamaki yace "kuma fa haka ne, kar muje muji abu ya fashe ba shiri." Fuska ta hade tace "yanzu ni har katuwa ce dazan fasa wannan table din?" Ta fada tana bubuga table din." Ya dan canza fuska yace "kuma fa haka ne, taya ma za'ace babyna guda zata karya wannan katan abin? Wai waye ma ya fada?" Ido ta kafeshi dashi, waige waige ya shiga yi yace "ni wai waye ya fara maganar nan?" Serving spoon ta mikamai tace "zubama da kanka." Kwanciya yai a kan cinyarta yace "ni kam in ba'a ban abinci ba nan da minti biyar Allah inaji za'a samu matsala." Dayake rigar karama ce daya kwanta sai ya zama kasansa kadan rigar ta tsaya, hannu yasa ta cikin cinyoyinta da sauri tace "zan zuba wallahi, ni wallahi tsoron zama anan nake, in wani ya shigo fa? Dauke kansa yai daga cinyarta yana dariya yace "in suka ganmu kinga sai suyi gaggawar bamu namu muhallin." Jalila ta kalleshi cikin mamaki tace "lalai yaya." Ta karasa da dariya tare da fara zubamai abincin. Shiru yai yana tunanin mahaifinta, Jalila ta kalleshi tace "Yayah!" Kallanta yai yace "yah?" Tace "me kake tunani?" "Me kika gani?" Tace "bakomai." Fork ta mikamai, ya kalleta sannan ya dan shagwabe yace "ni faduwar danai dazu ma kamar na bige hannuna." Murmushi tai sannan tace "ba sai kayi pretending ba." Ta karasa tana debo abincin. Murmushi yai sannan ya shiga karba, yaci sosai sannan yasha tea, kwantar da kansa ya sake yi a cinyarta tace "yaya....." Jitai cikin sanyin murya yace "Jalilah?" A hankali tace "Naam." "Ki dinga ma mahaifinki addu'a yayi nisan da sai dai a kwatoshi da addu'a, da fatan nemar masa shiriya agurin mahalicci." Jalila tai shiru tana kallansa, dago da kansa yai amma kan na kan cinyarta yace "bawai wani abun bane, kawai dai ina tunani addu'arku ita yafi bukata. Ya karasa da murmushi wai dan ya nuna mata bakomai. Yanda take kallansa ne yasa yace "ba wani abun bane kawai dai........" Katseshi tai tace "shi yama haka ko?" Ta fada tana taba gefen bakinsa." "Oh wai akan me babban mutum zai daki kamar ni? Ni ba dan yaro ba nima?" Jalila tace "abinda Mumy ta fada hakan ne ko?" "Name kenan?" Na Dady zai kwace musu company dinsu da gidansu?" Kai kawai ya juyar ya kara kwanciya yace "bansani ba." Hannu tasa ta dagoshi tace "Yayah?" Yanda ya kalleta yasa ta sakeshi tana murmushi tace "hakan ne , yanzu ya kukai?" Yace "mun samu an kwace company din daga gunsa yana gunmu yanzu sai dai bansan maganar gidansu ba." Jalila ta fara neman hadiye kwallarta tace "Yaya ta ina dan Adam zaiyi haka? Taya mutum zaiyi haka? Kuma mutum din ma wanda yake mahaifi? Miji?........" Hawayenta ne suka nemi fitowa yasa ta shiga motsa baki tana neman hadiye kukanta. Hassan ya jawota kan cinyarsa yana kallanta, kallansa tai sannan ta sunkuyar da kanta hawaye suka fara zubo mata. Yace "to ke yanzu kukan me kike a takaice? Ke kikai? Shifa yai sannan a yanda mahaifinki ya nuna kamar ba wanda ya isa ya....." Sai kuma yai shiru, hawayenta ta shiga sharewa suna sake zubowa tace "ni da wani ido zan kalli mutanen gidan nan? Da wani ido zan kalli wadanda suke jinina?" Hassan ya jawota jikinsa yana lalashi, yace "mubar kasar nan a dan kwanakin nan, naga alama in ba barin kasar nan mukai ba bazan daina ganin kina kuka akai akai haka ba." Dagowa tai ta kalleshi, yace "ni kila zan dan saki kuka amma kadan, dan haka." Ya fada yana nuna tsagun karamar dan yatsansa. Jalila tace "ashedai zaka sani kaima." Yace "kardai inyi karya ne ai. Murmushi tai sannan ta kalli gefenta da wayarta ke ta kara. Ganin sabuwar number yasa "ta daga jiki a sanyaye." Jalilah? Cikin mamaki tace "Safeenah" Safeena tana a
๐Ÿ