NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 154 of 172

Shiru yai kamar ya sake magana sai kuma yace "to." Tana ganin ya fita kawai ta tsuguna tasa kuka, ba kowa a wajen sai ita dan mutanen ma sun tafi, itakam me tayi? Laifin me tayi da rana daya rayuwa ta juya mata haka? Hakkin bayin Allah da kukaitaci. Kuka ta sake sawa, ta dade tana kuka kafin ta mike ta tafi asibiti. Safeena na ganinta ta taso tace "Mumy menene?" Mumy hawaye ne yazubo mata tace "Safeena ya zamuyi?" Hankalin Safeena ne ya tashi tace "menene?" Nan mumy ta kwashe komai ta fada mata tana kuka, sam basu san kafin su fara labarin Inna ta farfado ba. Kuka sosai sukeyi itada Safeena, Safeena tana kuka tana cewa "yanzu Mumy haka Dady ya mana? Kema Mumy kamar baki da wayau kina ganin yanda ya banzatar da abinda ya haifa duk rashin mutuncin mutun ko duk mutuncinsa indai har bai daraja abinda Allah ya bashi ba banaji zuciyarshi a tsarkake take, kina ganin duk abinda za'ama Jalila bai taba sa baki ba, bai kuma taba nuna damuwa ba, tunda kikaga haka ai kema kinsan Dady ba mutumin kwarai bane." Mumy tana kuka tace "duk laifinane Safeena, Inna tasha nunamin gaskiya amma banaji, yanzu gashinan ai." Yanda Inna ke yi ne yasa suka juya inda take da sauri, hankalin Mumy ya tashi tace "Safeena kira likita." Da gudu ta fita, Mumy ta kamo hannunta kawai ta sa kuka. Inna ta fizge abin hancinta cikin wani irin murya tace "Fatima!" Mumy ta dago da sauri tana kuka, Inna tace "ki daina kuka, ni nasan tawa tazo karshe, ke nakeji Fatima bansan wace rayuwa zakiyi ba." Mumy tana kuka tana girgiza kai tana cewa "Inna ki daina fadar haka." Inna ta girgiza kai cikin tsananin ban tausayi tace " ki duba kasan katifa ta akwai key na safe dina akwai takardun gida dana siya kwanaki can da suka wuce, kisa Sani ya kaiku gidan. Fatima kiyi hakuri duk nice na cuceki, duk nice na dauraki akan rayuwar da kikeyi, san kaina da sanki yasa bana tunanin komai, Fatima bansan ya zakuyi ba, shares dina basuda yawa sai dai nasan zasu rage muku na cin abinci. Yanda numfashinta ke kara sama ne yasa hankalin Mumy ya kara tashi, Inna tace "karkima Abakar magana, kar kuma ki nemi kwatar gidan, ki barshi rayuwa ce, gashinan nima na gani dayawa sun gani shima kuma zai gani, sai dai ki taimakeni da abu daya. Mumy ta kara runtse ido hawaye na kara zubo mata "Jalila! Da Mamanta!" Idanunta ne suka shiga lumshewa tace "Fatima ki nemarmin yafiyar........." Yanda ta kara birkicewa ne abu na ta zubowa daga bakinta ne yasa ta kasa magana, Dr ne ta shigo da sauri ta matso kusa da Inna. Kafin ta yi wani abu har rai yayi halinsa. Wani irin kuka Mumy ta saka, Safeena ma ta sa kuka abin tausayi. *********** Abubakar kam yana zaune a dakin hotel din daya kama, idanunsa sunyi jaa in ya tuna abinda aka mai sai yajii zuciyarsa na kara tafasa, Fatima? Sai kaga ya naushi gefen da yake zaune, can ma sai gani nai ya mike a zuciye ya nude window kawai yana kallan waje. Bai taba tunanin wani abu zai kawo mai cikas ba a wannan lokacin, ihu ya saka tare da cizar lebe. ************ Goggo kam hankalinta ya kwanta dan yanzu kam taje taga yan uwanta data dade tana kewa, sun dan dade suna waya da yayanta wanda ta amshi numbersa sukai ta gaisawa da yan uwa suka mata ban gajiya sannan ta kashe, wai yanzu itace yan uwanta ke nuna mata kauna haka? Lalai duniya juye juye. *********** Suna shiga mota Sageer yace "Yaya wannan mutumin kansa daya kuwa?" Hassan yace "kansa daya kawai tsabar greediness ne ke damunsa." Sageer yai tsaki yace "ji fa abinda ya maka?" Murmushi yai yace "kar ka damu ba komai, sannan dan Allah mu bar abin nan mu biyu." Sageer yai dan tsaki sannan ya cigaba da tukinsa. Suna isa gida ya kalleshi ya mai alamar zip da bakinsa. Sageer ya bishi da kallo, shikam da sauri ya shiga ciki, Sageer kam juya kan mota yai ya fita dan dama akwai abinda zaiyi. Hassan na shiga ya wuce kitchen da sauri, ba kowa a ciki, da alama harta kammala yanda yaga har kitchen din ta gama gyarawa, juyowa yai ya wuce sama. Kallan kanta tai a madubi tace "kai inaa.... bazan iya sa kayan nan da Ameera ta ban ba." Rigace iya gwiwa, ba dogon wando, tace dama taban wando ne kila dana saka. Ta juya jikin wardrobe tana neman cirewa ya turo kofar dakin. Ta manta kayan dake jikinta, gani tai ya taho inda take da sauri, yana karasowa ya rungumeta tsam a jikinsa. Shiru tai a hankali yace "Baby wannan shigar fa?" Tunowa tai, ta kasa cewa komai, dagota yai ya kalleta daga sama har kasa, kunya tasa ta juya baya da sauri, kara juyo da ita ya rungumeta yace "saura kadan fa na fadi." Kallansa tai tace "kai Yaya." Sumbatarta yai zaiyi magana sai ya fasa yanda yaga ta kura mai ido. Yace "menene?" A hankali takai hannunta gefen bakinsa tace "me ya faru?" Hannunta yadan ture yace "ba wani abun bane ina sauri ne ban kula ba na danji." Idanunsa ta kalla sai dai ta rasa me yasa bata yarda ba. Kamar zatai
🏠