NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 152 of 172

Murmushi ta sakeyi tace “da alama bashin nan nawa karuwa yakeyi dayawa.” Sumbatar wuyanta yai yace “da alama zamu dan barki a gida ke kadai na dan wata awa daya.” Kai ta daga alamar gamsuwa ba tare da ta tambayeshi ba. Saketa yai sannan ya wuce sama, wanka yai yasa kananan kaya sannan ya sauko, Sageer ya tarar a falon Abba yana rike d wasu takardu yana kuma waya. Yana ganin Hassan yamai alama dayazo, nan sukai magana su biyu kafin su fito falo. A tare suka fita, Mumy ta shiga motarta suma suka shiga motar Sageer. Suna shiga Hassan yace “haka Abba yace?” Sageer ya shiga yimai bayani, Hassan ya jinjina kai alamar gamsuwa yace “shikenan.” ************* Ba wani kato bane main branch din nasu, sai dai dayake ajiyar kayan abinci sukeyi daga baya akwai wani tangamemen fili da akai gini inda ake aikin a ciki. Sani na ganinta ya taso da sauridan dama yana zaune a waje yana jiranta, tanna karasowa ya matso da sauri yace “sun shiga cikin meeting din kamar minti 5 da suka wuce.” Mumy ta matso ta sanarma Hassan. Dakin babban taro na hadaka suka nufa, suna zuwa Sani yasa aka bude dakin. A lokacin kuwa Dady ne tsaye yana bada speech dinsa na yanda company dinsu wai ke cikin matsalar da suke san akawo mafita dan a kwatota daga ciki, Babban director din yace “Bravo! Gaskiya duk company din nan ba wanda yake sanshi da kula dashi kamar kai, shiyasa nazo da babban shawara akan sauke Hajiya wacce girma ya kamata yasa take neglecting din aiyukanta, a baka kai sirikinta wanda ka sadaukar da komai naka akan company din mu.” Muryar Sani sukaji yace “Investors din da suka taimaki company dinmu sunzo.” Kowa kallan su ya juyo yai, Mumy ta zubama Dady ido wanda gaba daya shima idanunsa na kanta. Hassan ya matso inda Dady yake yace “will you please get down?” Dady ya kalleshi zuciyarsa gaba daya ta rage bugawa yanda ya kamata, Hassan ya kalli Sageer yamai alama dakai akan ya matso. Sageer ya kalli Dady wanda yake saukowa kamar wanda bashida ragowar laka a jikinsa. Sageer ya fara bayani kamar yanda Abba yamai. Takarda ya zaro ya daga sama yace “wannan shine contract din da mukai da company dinku akan za’a biyamu 50% na kudinmu a kwana uku da suka wuce. A cikin wannan contract din munyi bayani time da kuma kudin da za’a fara biyanmu. Sai dai jiya mun nemi Chaiwoman din company din me makon ta bamu sai ma taki daukan wayarmu, wannan dalilin ne yasa muka sauko kasan contract din wanda yace “in har ba’a biyamu kudin mu akan lokaci ba rabin company din zai dawo namu.” Nan fa kowa ya fara kananan maganganu, Sageer ya kallesu yace “ saboda haka daga rana tayau zan zama nine shugaban company din nan har zuwa ranar da za’a biyamu kudin mu.” Nan fa guri ya kachame da kananan maganganu. Hassan kam abin ya birgeshi wani irin dadi yakeji a ransa, lalai ilimi rahama ne. Hannu ya daga ya yima Sageer jinjina. Dady kam ji yai gaba daya wata muguwar zufa na ketomai ta ko ina. Wani daga cikinsu ne yace “ta ina zamu yarda da abinda ke faruwa?” Sageer yace “da farko ga signing din Chairwoman din nan sannan ga yartanan zatai duba, dan tana nan akai komai, sannan zan miko muku ku gani kuma.” Mumy wacce gaba daya dana sani ya gama kamata, jikinta duk ya gama yin sanyi, meke faruwa? Itakam ai ba haka sukai ba, ta dauka ko ita zasu barikon kwarya kafin ta samu Dady ya dawo hankalinsa, ya kamar take ganin anyi amfani dasu? Haka tace ai komai daya fada daidai ne sannan aka mikama kowa ma ya gani, nan fa ba yanda suka iya aka ba Sageer kujerar shigabanci ya zauna akai. Dady kam gaba daya ya koma mutum mara amfani dan jiyai ma dakin kamar ba kowa a ciki ba kuma abinda ake cewa a ciki. Sai zafi da kirjinsa yakeyi...... Mumy kallansa kawai takeyi...... Sageer ya kalli Hassan sukai murmushi, Sageer ne ya tuno kalaman Abba dayace akwai tsuhuwar contract din da suka farayi dama time din da akasa kenan, to shi bai yaga ta ba shine yasa Sageer ya nemo, Abba yace da Jalila tayi nisa a karatu da ita zai sa aba wannan matsayin ko dan mahaifinta ya hankalta. #OneLuv💕 [12/30/2018, 10:08 PM] El-hajj: 🗯 *JALILAH* 🗯 Written By : *AYUSHER MUHD* Wattpad: *Ayusher Muhd* *HASKE WRITER'S ASSOCIATION* *72* Gaba daya haka kowa ya fito daga dakin taron zuciyarsa a cunkushe da wannan al'amari. Ya rage daga Hassan, Sageer, Mumy, Dady sai Sani ne kadai a ciki. Mumy ta kalli Hassan tace "amma nikam ai ba haka mukai daku ba." Hassan ya mata wani kallo yace "ke wacece da zaki tsara mana abinda kikeso muyi? Na dauka farincikinki kawai a kwace company din ne daga gun wannan, ba kuma naji kinada wani iko na samu ko hanamu." Dady zuciyarsa takai makura dan dama daurewa kawai yakeyi, jin kalaman Hassann ya kara tunzuro shi, matsowa kawai yai naga ya daga hannu kamar zai gaurawa Mumy mari, sai kuma ya sauke hannunsa yana
🏠