ย  ย  NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 149 of 172

hinan gaba daya sai wani mazewa kikeyi, kindai san na fiki iya hade fuska ko?" Ta kalleshi tare da cewa "nifa ba hade fuska nake ba." "Ohh tafiya ne bakyasan yi dani ko me?" Tace "Allah ba haka bane Yaya kawai dai bansan yanda zan sauka kasa bane, nasan yanzu Abba ya fadawa Ummy." Yace "ikon Allah! To sai me? Ai ko bai fadaba ni zan fadamata." Cikin shagwaba tace "haba yaya?" Yace "to naji bazan fadaba, Abban ya fada mata shikenan?" Ta kalleshi kamar zatai kuka, da alama Yaya bazai gane ba, agoggo ta kalla tace "oh ya kamata na sauka kasa fa." Ta fada tana neman saukar da kafarta daga kan gado, Yaya ya jawota tare da cewa "yanzun ma fitar za'ai a barni?" Cikin zolaya tace "ko zamu tare? Sai ka tayani?" Ganin yanda ya tsaya yana kallanta yasa tai dariya tare da rufamai bargo ta mikomai littafi tace "malam mai karatu ai karatu dayawa." Ta mike ta fita tana dariya, Yaya kam birgeshi tai, gani nai ya mike ya zura doguwar riga kawai ya sauka. Jalila kam sam batai tunanin zai kawo wani abun a ransa ba, kitchen ta nufa, yau kam tai sa'a Ummy bata fito ba, dadi ne ya kamata ta wuce kitchen tare da tunanin abinda za'ai breakfast dashi. Jan nama ta dauko ta shiga wankewa, sannan ta fara yanka albasa tana dan kankane ido. Jin hannu ta bayanta yasa gabanta ya fadi, a tsorace ta juyo yanda ya riketa yasa tana juyowa ta juyo daf daf da fuskarshi, sumbatarta yai yace "na sauko, da me zan tayaki?" Kallan kofa tai sannan ta kalleshi cikin mamaki tana kokarin zamewa tace "Yaya!" Yace "da me zan tayaki?" Tace "tayani? Yaya in wani ya ganmu fa?" Ta fada tana dan zamewa, yace "ohoo naga ke kika ce na sauko?" Baki ta bude tace "wasa fa nake maka kaima ka sani." Yace "wasa? To ya akai ban sani ba? Sannan banaji kema kincemin wasan nan kikeyi." Baki ta bude tana kallansa tace "lalai yaya, me zance in su Ummy suka ganka anan?" Yace "me zakice kuwa? Kawai mijinki ne yake taimaka miki." Dariya tasa tace "a haka sauki fada." Yace "a can din ma sauki zai.....yi" Yai maganar yana kara jawota, tace "Yaya Allah kar Ummy ta fito." Sumbatar wuyanta yai yace " wasa wasa da ke matsoraciya ce." Tace "naji, nayi surrender, ayi hakuri, hanuna a sama." Ta fada tana daga hannayenta. Murmushi yai sannan ya saketa tare da bude fridge, sannan ya rufe yace "yanzu a haka zan tafi?" Tace "hmm dan Allah yaya jeka ko falo ne,wallahi bansan ya zanyi ba in wani ya ganmu anan." Baki ya tabe sannan yace "za'asan an koreni wallahi." Ya juyo tare da hade fuska. Da sauri tace "yaya?" Tsayawa yai fuska a hade, ta matso ta dan daga kafafunta ta sumbaci kuncinsa, tace "sorry!" Kallanta yai fuska a hade yace "wannan karan wannan bai isa ba." Ya fita, kallansa tai tana murmushi har batasan tasa wuka a kusa da bakinta ba sai dataji warin albasa sosai yasa tai saurin sauke hannunta tana dariya. Yaya ma yana fita yadan harari kitchen din sannan yace "chance din ramawa ya samu." Yana kokarin bakin falon Sageer na fitowa, kallansa yai yace "Yaya? Daga ina?" Yace "hmm na fito gaida Ummy ne naga batanan." Sageer Yace "oh wallahi da sassafe suka fita itada Abba, sunje Bauchi, ka duba wayarka har text ta maka kai da Jalila." Yace "Bauchi? Wani abun ya faru ne?" Yace "wallahi ban sani ba, inaji dai zasu je gun dangin Baffanane, sannan kila akwai abin aiki da ya kaisu daga nan." Hassan yace "Shine baka bisu ba?" Sageer yace "kasan halinsu, in Ummy taje sai sun mata gori, gwara ni naje daga baya." Hassan ya jinjina kai yace "Hakan yayi, kace kai kadai ne a gidan kenan?" Yace "hmm amma nima anjiman nan zan fita zanje office din Abba akwai abinda ya sani." Hassan a ransa yace "kenan sai mu kadai?" Amma a fili yace "hakan yayi, ya kamata ka dinga fita ko ka samoma Ummy wata surikar tunda dai kaga ni tafiya zanyi." Sageer yai dariya yace "kar ka damu an kusa." Hassan yace "haba? Ka gano wata ne?" Sageer ya matso sai tin kunnensa yace "na gano amma bansan ko inada chance ba." Hassan yasa dariya zaiyi magana sukaji ana knocking din kofa. Sageer ya karasa ya bude. Mumy ce tsaye a gun, Sageer ya kalli Hassan sannan ya kalleta. Ganin haka yasa Hassan din matsowa. Kallan mamaki ya mata kafin yace "Bismillah." Mumy ta shigo jiki a sanyaye. Abinda takeyi hakan ya dace kuwa? Anya kuwa ta kyautama Abubakar? Zama tai a kasa sannan ta kalli Hassann da Sageer. Hassan ya kalleta yace "lafiya?" Kallansa tai sannan ta hada hannayenta biyu tace "Hassan ku taimaki Inna ta da ni kaina da kuma Mijina, ku duba girman Allah. Bawai abinda muka aikata ba ku taimaki rayuwarmu." Yanda take magana da karfi yasa Jalila lekowa. Ganin Mumy yasa ta tsaya tana kallanta, Hassan ya kalleta sannan ya kalli inda Jalila take, Sageer ka ya kalleshi. #OneLuv๐Ÿ’• [12/30/2018, 10:07 PM] El-hajj: ๐Ÿ—ฏ *JALILAH* ๐Ÿ—ฏ Written By : *AYUSHER MUHD* Wattpad: *Ayusher Muhd* *HASKE WRITER'S ASSOC
๐Ÿ