NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 148 of 172

shafeni ba." Shiru yai har saida ta sakemai magana sannan yace "Hajiya mijinki....." Sai kuma yai shiru, tace "Abubakar? Me ya sameshi?" Yace "ba wani abin bane ya sameshi." Ajiyar zuciya tai dan hankalinta yadan kwanta tace "to menene?" Iska yadan firzar kadan kafin yace "Kwace matsayin Hajiya zaiyi a gobe dan har ya zauna da Board members." Cikin rashin fahimta tace "ban gane kwace matsayin Inna ba, ta yaya? A kuma wani dalili? Bayan dama matsayin nashine nan gaba?" Yai shiru kafin yace "Ranki ya dade ki taimaka ki duba abinda yake a lulube da bargo, ki daina kallan abinda zuciyarki kesan gani, please ki duba reality." Tace "bangane ba." Cikin takaici yace "in bakiyi wasa ba san da kikema mijinki shine dalilin da zai halaka komai na rayuwarki, bakisan wanene mijinki ba, mutum ne dabaisan komai ba sai kansa, masan komai game dashi saboda Hajiya tasa inyi following dinsa dan ganin me yake aikatawa." Cikin tashin hankali tace "ni kasa na rasa me ma kake nufi da kalamanka." Yace "ba sai kin gane ba a wannan lokacin, saboda munacin crisis din da muke bukatar mafita cikin gaggawa, Anjima karfe 10 za'a sauke Inna daga matsayinta a bashi, bawai bashin bane matsala shi din ne matsala, dolene kizo ki kwace company din da mahaifinki da mahaifiyarki suka sha wahala gun ginashi." Hawaye ne ya cika a idanunta fal, tace "yanzu me ya kamata muyi? Sai dai inaji kamar ina betraying din mijina akan san zuciyata." Ya runtse ido yace "dan Allah na rokeki da Allah ki tashi daga baccin da kikeyi, ki duba sosai kiga wanene ke betraying din wani tsakanin ke dashi, sannan ki duba mahaifiyarki da mahaifinki." Mumy tai shiru kafin tace "yanzu me ya kamata muyi?" Yace "dolene a cikin dayan biyu mu zabi daya, ko dai kiyi amfani da shares dinki ki ja ra'ayin directors din, ko kuma mu nemi wanda yai investing a company din ya baki matsayin." Shiru tai tana tunani kafin tace "plan din farko ama cireshi dan na riga na bashi shares dina, plan na biyu kuma da matsala saboda investors din gidan mijin yarsa ne." Inalilahi wa ina ilaihi raji'un Sani ya hau fada kafin yace "ki taimaka ki hadani da Hajiya muyi magana ma tabbatar ita zatasan yanda za'ai." Mumy ta share kwallarta tace "Inna tana asibiti ba lafiya." Sani ya runtse ido yace "shikenan magana ta kare,haka Allah yai, ya jikin nata?" Mumy tace "gatanan dai a kwance." Yace "shikenan sai nazo dubata, da alama ba sai nake company din bama." Mumy tai shiru hakan yasa yace "sai anjima." Ya kashe wayar, Mumy ta dafa kanta dake sarawa, agoggo ta kalla karfe bakwai da rabi na safe, wayar Abubakar ta sake kira, bayan tayi kira biyu ma sai ma taji an kashe wayar gaba daya, shiru tai tana kallan wayar sannan ta kalli Inna, tunowa ta dingayi da kalaman Inna daya bayan daya tun kafin auranta da Abubakar yanda ta dinga neman hanata suna fada akan itafa sai shi, to itakam ai haryanzu tana sansa kuma ta tabbatar akwai wani misunderstanding ne a tsankaninsu dan Abubakar bazai mata haka ba, da kwacewa yakesan yi da ai tuntuni halayensa dake boye sun fito. Lalai ko saboda Inna tasan ba hakan bane gaskiya dolene ta binciko gaskiyar al'amari ko kuma kila dai da akwai wani abun. Sai dai ta ina? Taya zai nemi taje gidansu Jalila? Inna ta kalla wace ke kwance, yanda mahaifiyarta da mahaifinta suke kaunar company din yanda sukasha wahala gun kula dashi. Idanu ta runtse tana tunani, hawaye ne suka sake zubo mata, kukan Yasmeen ne ya dawo da ita hankalinta, mikewa tai da sauri tazo ta dauketa tace "Yasmeen ganinan." Yasmeen ta rungumeta sannan ta fara neman komawa bacci. Tana komawa Mumy ta kwantar da ita sannan tadau waya ta kira Safeena, tana dagawa tace "Mumy lafiya da safan nan?" Mumy tace "dubamin ko Dadynku na nan." Nan ta mike tai dakinsu wayar na kunnenta tana cewa "Mumy nikam meke damun Dady wai?" Tace "me kika gani?" Tace jiya sai barbaza takardu yake a daki na shiga kamar yana neman wani abun, sannan da na fito kai plate kitchen najishi yana waya yana cewa "nagode yallabai bazan manta da hallacin da akamin ba, kn dai na zama chairman i will definitely fulfil your wishes." Cikin tsananin mamaki Mumy tace "meyake nema?" Safeena tace "bansani ba." Ta karasa maganar tana knocking, jin ba amsa yasa ta tura kofar dakin, bakowa a ciki tace "Mumy ya fita." Mumy tace "shikenan kidanzo asibiti inasan fita ne." Tace "okay bari nai wanka dan naga har ma angama break din da za'a kawo." Mumy ta kashe wayar tare dayin shiru tana tunani, me yake nema? Sannan wanene yallabai? Ganin batada mafita yasa ta mike tana zarya a tsakiyar dakin. Safeena na shigowa ta zari mayafinta tace mata ina zuwa. Fita tai ta hau motar da aka kawo Safeena dan daka drivern ya shigo duba Inna, tace mai gidan Jalila. ************ Hannunsa yasa a cikin kasan rigarta tasa hannu ta rike hannunsa tare da cewa "Yayah?" Yace "wai abin haryanzu bai wuce ba?" Tace "menene bai wuce ba?" Yace "gas
🏠