n ba."
Yanda yai maganar ne ya bata dariya tace "dan Allah ka fadamin."
Yace "sai kin biyani tukunna."
Tace "ai ko aiki sai anyi ake biya, inka fadamin zan ma."
Yace "tam na yarda."
"Dana fadamai cewa yai zai duba yaga wacce kasa ce tafi dacewa dan kinsan na fadamiki ya zauna a Egypt muma kuma haka, yanda na kula dai yafisan nan din.
Sai dai kinsan ya dago mu."
Da sauri tace "a me kuma?"
Kuncinsa ya nuna mata yace "bani half fee."
Sumbatar kuncinsa tai tace "me ya dago?"
Yace " cemin yai wai zai fadawa Ummy ba saboda mu zauna mu kadai bane mukesan tafiya."
Ido ta zaro tace "haka yace?"
Yace "eh kinga da alama ya dagomu."
Tace "kai kuma me kace?"
Yace "cewa nai Abba na gode da fahimta."
Idanu ta zaro sannan ta ceji lebanta tace "mene? abba na gode da fahimta?"
Yace "Eh, ba fahimtata yai ba?"
Haushi ya kara kamata tace "oh ni naga ta kaina, yaya so kake na daina sauka kasa."
Yace "menene? Yanzun ma laifine wai?"
Kamar zatai kuka tace "ya za'ai kacema Abba haka?"
Yace "ikon Allah to me zance?"
Mikewa tai ta zauna tare da sa kanta cikin cinyoyinta tace "shikenan nikam bansan da wani ido zan kalli Abba ba."
Hassan yace "ban gane ba, da dawani ido kike kallansa? Nifa na kasa fahimtar ma abinda kike nufi kwata kwata."
Ya fara tare da neman kamota, mikewa tai tare da cilla mai pillow ta fito falo.
Da kallo ya bita yana cewa "baki biya ragowar fee din ba."
Juyowa tai ta kalleshi sannan ta fita cikin takaici.
****************
Wajen karfe biyu na dare hannunta ya fara motsawa, a hankali ta bude idanunta, tana kallan dakin.
A asibiti take? A hankali ta kalli Mumy dake kwance a kan kujera ta kwantar da Yasmeen a kusa da ita.
Abubakar!!!! Kokarin zare abin dake hancinta tai, hakan yasa Mumy ta bude ido.
Ganin Inna yasa ta taso da sauri tare da kara fitilar dakin, ta matso tare da rike hannunta tace "Inna! Inna kin ganeni?"
Kai ta daga alamar eh.
Alama ta mata akan ta cire mata abin hancinta, tace "bari na kira nurse."
Inna ta rikota da sauri tare da girgiza mata kai.
Cire mata tai sannan tace "Inna bai kamata ba, gwara a cire miki."
Inna a hankali cikin wata murya numfashinta na fita sama sama tace "bacci nakeji magana daya zan miki, ki kira Sani kice ya duba yaga mai Abakar yake shiryawa, cikin mamaki tace "wani irin zance ne wannan Inna? Me yake shiryawa kuwa?"
Tana lumshe ido tace "kiyi abinda nace sannan karki kuskura ki fadawa kowa na farka koda Doctor ne balle mijinki"
Mumy zatai maga taga inna na kokarin yin numfashi da kyar, da sauri ta maida mata sannan ta kurawa Inna ido, me Inna take nufi????
#OneLuv๐
[12/30/2018, 10:07 PM] El-hajj: ๐ฏ *JALILAH* ๐ฏ
Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *Ayusher Muhd*
*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*
*70*
Mumy tai zuru tana bin Inna da kallo, me Inna take nufi da abinda ya faru a dan kankanin lokacin nan?
Shiru tai tana kallanta waya rike a hannunta, ganin hankalinta ya kasa kwanciya yasa kawai ta kara kiran Dady, har ta katse ba'a dauka ba ta sake kira, yanzun ma sai data kusa katsewa aka daga.
Hankali a tashe tace "Dadyn Yasmeen, ina ka shiga inata
Shiru yai bai amsa mata ba, tace "kana ina? Dan Allah inkana gida kazo, Inna ce yanzu....."
Katseta yai cikin fada yace "me zaki cemin a cikin daren nan? Wai bakiga agoggo bane? Me yasa ne wai bazaku bar mutum yai bacci hankali a kwance bane?"
Tsananin mamaki ne ya kamata tace "Bakajin dadi ne?"
Dan karamin tsaki yai yace " koma ina jin dadi ko banaji inaso a sararamin haka nan, akan me za'a dinga damuna da kira ba gaira ba dalili?"
Tace "bangane mai kake........"
Jin kamar ma an riga an katse wayar ne yasa tace "Hello? Hello Dadyn Yas..."
Kallan wayar tai taga kuwa an riga an katse ta tsananin mamaki ne ya kamata, tace "lafiyarsa kalau kuwa? Ko stress ne?"
Shiru tai tana kallan Inna, kafin ta kamo hannunta cikin tausayawa tace "Inna dan Allah ki bude idanunki, gaba daya kaina ya daure."
Anan ta dan kwantar da kanta har safiya tai, sallah tai sannan ta gyarama Yasmeen kwanciya ta dau wayar Inna ta kira Sani.
Yana ganin kiran ko gama ringing din farko baiyi ba ya daga tare da cewa "Hajiya? Lafiya kuwa inata kira wayarki a kashe."
Mumy tace "Sani ina kwana? Fatima ce."
Yanayin maganarsa ne ya canza yace "Ina kwana ranki ya dade."
Tace "me kake neman Inna ka fada mata?"
Yace "a'a bakomai, bata kusa ne?"
Mumy tace "tana kusa sai dai bazata iya ko magana ba, menene? Ka sanar dani."
Yai shiru tare da jan numfashi kafin yace " Hajiya muna cikin matsala, dan tabbas yau akwai gagarumar matsala dazata afku a company dinmu."
Gabanta ne ya fadi kila hakan ne yasa hankalin mijinta ya tashi, jiki a sanyaye tace "meke faruwa?"
Yai shiru kafin yace "Hajiya ina tsoron sanar dake domin abin ya shafeki."
"Ni kuma? Ta yaya? Ni yanzu kiranka nai akan Inna ta bani sallahu gunka, ban fahimci kuma abin ya