farida Allah sai an dade."
Maman tai dariya tace "sanda zaki dau kafa ki tafi ina ina? Tunda yanzu ake hutu ai kuma sai a hankali."
Shiru tai tana tunani, wanda ita kanta batasan tunanin me take ba, sai dai kawai ta kurawa kasa ido.
************
Sageer na juyawa yace "oh a kusa ma dasu Aunty Nana take, nan ya gangara gidan yana cewa likita ce?? Ahh ina..., student? Kai ya jinjina yace da alama kam dan yarinyace, dariya yadanyi yace student harda nunawa irin ita likitan nan ce? Ko da yake hakan nada kyau alama ce ta nuna tanada confidence akan karatunta.
Ganin ya wuce kofar gidab yasa yai saurin kallan koffar gidan tare da yin reverse yace "ahhh Sageer."
Yasa hannunsa acikin kansa.
Bugawa kofar yai yaga ba wanda ya bude, wayarsa ya dauko ya kira Aina'u yace "Aina kina ina ne hakan?" Tace "ni ai ina Sokoto."
Cikin mamaki yace "Sokoto? Me ya kaiki?"
Muryar yayarta yaji tace "me takeyi anan ko?"
Da sauri ya kashe wayar tare da shigewa mota yace "au ashefa acan Aunty ke aure?"
Tada motarsa yai yai gaba.
************
Mumy ke ta kara kiran wayar dady amma yaki ua dauka, duk yanda takira kuwa ba'a dauka, kallan Safeena tai tace "Safeena inaji baya kusa ko ya bar wayar a wani gun."
Safeena tace maybe.
Sultan dake gefe yana latsa waya ne yace "yana gida har na fito."
Cikin mamaki mumy tace "bacci yake?"
Yace yana falo yana kallo.
Mumy tai ajiyar zuciya tace "maybe wayar ya barta a daki."
Har dare su safeena da Sultan suka tafi sam ba dady ba alamarsa sai kiransa take bai dauka ba.
Harta gaji ta daina.
*************
Ihun data kurmane yasani na tsorata, gani nai cikin hanzari ta nufi kitchen, wuka ta dauko ta shigo dakin cikin tashin hankali kamar mahaukaciya sabuwar kamu.
Zaliha jikinta banda uban rawa ba abinda yakeyi, shi kansa jikinsa rawa yake kamar wanda ake kadashi.
Zaliha ta kankame rigarsa tana ihu tace "shikenan yau ajalina yayi, uban me ya kawoka dakina?"
Hannu yasa ya tureta da karfi harta fadi yace "ki zo falo inda nake cikin wannan shigar kice bazan biyoki ba? Sannan dana biyoki ai ke kika fara rungumeni." Ya fada yana nunata sanye take da vest wanda gaba daya rabin kirjinta a waje yake da wani short knicker sanda ya matseta dam.
Banko kofar datai ne yasa Zaliha ta kara kwarma ihu tana kada kankameshi da neman ya taimaketa.
Tureta yai da karfi ta kuma kanta a jikin gado, kanta ya fashe, amma kuka ya hanata magana.
Tana shigowa yai toilet da gudu ya shiga ya rufe.
Kan Zaliha tai tana ihu, Zaliha ta hade hannayenta alamar roko, tana kuka tana cewa "tuba nake Aunty ko taimakeni ki yafemin, da alama na haukacene dan bana cikin hayyacina, ko kuma inaji Taura ne yamin asiri dan na tabbatar ba'a hayacina nake ba.
Sa kafa tai ta harbeta da karfi sannan ta daga wular kamar zata caka mata, sai kuma naga ta tsaya, ihu ta kara sawa ta cillar da wukar sannan ta bude wardrobe ta fara cillo mata da kayanta tace "fita dan*******🤐"
Wallahi in kika kara minti biyu a gidan nan zaki fahimci ko ni wacece, sannan kayanki kawai zaki dauka wallahi ko biyar dita bazaki fita dashi ba.
Kuka Zaliha ta shiga yi tana neman Yayarta data temaka ta mata afuwa.
Haka ta kwashi kaya kadai ta fita.
***********
Kai ya girgiza mata idanunsa a rufe yace "ban yarda ba."
Murmushi tai sannan ta kwanta itama tana fuskantarsa cikin sanyin murya tace "to ni ya zanyi?"
Yace "ina na sani, ni dai asani."
Shiru tai tana tunani, wai dole sai ta sashi ya bude idansa.
Kallansa tai tana murmushi sannan ta matso da fuskarta a hankali tana kokarin kai bakinta kan goshinsa, hannu yasa ya jawota daf dashi, idanunta ta bude sosai tana kallansa, shima bude nasa idon yai yana kallanta kafin yace "a karasa."
Kallansa take gabanta na faduwa tace "mene?"
Idanunsa ne suka canza yace "abinda ake shirin min, gani nai bazan iya missing ba idona a rufe."
Kallansa tai tana numfashi da dan sauri, tace "ba mission din ya kare ba? Tunda ka bude idon ba?"
Kai ya girgiza yace "a ina?" Ya nuna mata bakinsa yace anan nakeso.
Dan harararsa tai kadan sannan ta matso da fuskarta ta dora bakinta kan nasa tana neman matsawa.
Bude bakinsa yai yasa nata a ciki, dama da alama kiris yake jira.
Sun dade suna sumbatar juna kafin su tsaya, a hankali suka kalli juna.
Gani nai sun sa dariya a tare baki yasa ya cije lebanta, kallansa tai sannan ta kara dariya ta dan tureshi kadan tace "gaskiya yaya wannan cin zali ne."
Yace "to a rama mana in anji zafi?"
Tace "zan rama amma ba yanzu ba."
Dariya yai kafin yace "dazufa da kuna tare dasu Ummy munyi magana da Abba."
Tace "wai ka fadamai?"
Yace "sosai ma, me za'a jira?"
Tace oh yaya ba kunya, kuma me yace?"
Hassan yace "matso kiji."
Matso da kunnenta tai yakai bakinsa yace "kin tabbatar kinaso kiji?"
Ta daga kai, yace "hmm to a sakemin."
Kallansa tai tace "me kuma?"
Yace "abinda akai yanzu ni bai ishe