***********
Yanda motar gabansa ta taka burki ne yasa shima ya taka, a tsorace ya dago ya kalli motar dake gaban nasa, ganin ya fita yasashi shima ya fito daga motarsa ya nufi gaban motar.
Yarinyace wacce da kadan tafi Ameera kana kallan yanda gwiwarta ke jiki da gwiwar hannunta zakasan bige ta akai tadan fadi, kokarin mikewa ta shiga yi saboda yanda zanin jikinta ya kwaye, ga mutane harsun fara taruwa.
Juyawa yai zai koma mota yaji muryar mai motar na cewa "ungo! Dan ma tabbatar saboda ki samu kudi kika fadomin kan titi haka, ba tin yau ba dama mukasan irinku."
Juyowa yai cikin mamaki ya kalli mutumin sannan ya kalli yarinyar, wacce ko kallansa batai ba kafarta kawai take dingisawa tana neman wucewa.
Ya sha gabanta yace "ungo tun kafin ki ha kin masifa, ko?"
Juyowa tai ta kalleshi, kamar zatai magana sai suka hada ido, rike da hannun mutumin wanda yake rike da dubu daya yai.
Ya kalleta sannan ya kalleshi yace "in zakai wulakanci sai kayi dakyau, sannan ita data fado dan ta samu kudi kana tunanin 1000 ya isheta?"
Ranta ya kara baci ta kalleshi sannan ta fara tafiyarta, itakam yau da alama batai addu'a ba ta fito daga gida...
Murya a zafafe yace "kai kuma waye?"
Nunamai motarsa yai sannan ya nuna kansa alamar mai motar ne.
***********
#Oneluv๐
[12/30/2018, 10:07 PM] El-hajj: ๐ฏ *JALILAH* ๐ฏ
Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *Ayusher Muhd*
*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*
*69*
Hannunsa ya warbar ganin yanda yarinyar ke dingisawa tana kokarin barin gurin, tausayinta ne ya kara kamashi ya koma motarsa da sauri ya hau ya tadata, gani yai tana kokarin yin wata kwana da sauri yaja motar zuwa inda take, tana shiga kwanar shi kuma yana saurin ratsa gun, horn ya mata, tsayawa tai tare da kallan motar, ganin layin bawai mai girma sosai bane yasa ta matsa tana tunanin duk gurin nan ya mai kadan?
Ta gefenta ya matso sannan ya zuge daya glass din motar saitinta yace "are u okay?"
Kallansa tai yanzu kam ta ganeshi, kai ta dagamai alamar eh sannan ta fara neman juyawa.
"shigo na karasa dake."
Kallan mamaki tamai tace "ina?"
Yace "yace bakya tunanin ya kamata kije chemist?"
Shiru tai tana kallansa kafin tace "nagode na kusa isa gida."
Ya kalleta yace "ina ne gidan? Dan da alama nidin ne bakyasan na kaiki kikacemin kinzo gida."
Hannu ta daga ta nuna mai karshen layin kawai tace anan daga can.
Yace "anan? Daga can? Wannan wani irin kwatanceni?"
Sannan bakiga zaninki ya samu matsala ba? Ba wai saboda wani abu ba ki duba yanayinki kizo na karasa dake."
Kamar zatai magana sai kuma naga ta kalli jikinta, kafin a hankali tasa hannu ta bude motar, shiga tai ta zauna tare da yin shiru.
Yace "mu mike?"
Kai tadaga mai kawai, nan ya mike layin, yace "sai ina?"
Tace "hagu zamuyi."
Yana juyawa ya ga wani chemist, kallanta yai sannan ya gangara yai parking yace "muje."
Kallan chemist din tai tace "ba sai munje ba inmunje gida zan gyara dakaina."
Yai murmushi yace "Sry likita amma yanzu kam sai munje."
Haka ta fito suka shiga, mai chemist din na ganinta yace "Maimuna kece?"
Kai kawai ta daga sannan ta kalleshi tace "Kairiyya fa?"
Yace "tana ciki."
Kallan Sageer tai tace "da ka barni anan ma in nagama sai na wuce gida."
Yace "shiga ki gama ina jiranki."
Mai chemist din ne yai dariya yace "wooo Maimuna yau kece da saurayi, lalai yau akwai abin mamaki."
Kallansa kawai tai ta shiga ciki, ganin mutum na jiranta yasa ta azalzala Kairiya ta mata dressing din da sauri ta fito, dan itakam nauyi ya daura mata na jiranta dayai.
Tana fitowa ta ganshi a tsaye a jikin mota da alama waya yakeyi, tsayawa tai tana tunanin mafita, ko ta gudu?
Sageer ne ya juyo suka hada ido, nan ya mata alama data shiga, shiga tai sannan shima ya shigo.
Haryanzu waya yakeyi sai dai yana juyowa yana kallanta ko zata nunamai wani gun.
Hannu tasa tanunamai gaban wani gida, nan ya kashe wayar yace "nan ne?"
Kai ta daga sannan ya karasa yai parking.
Gidane flat wanda a wannan lokaci zamu kirashi da rufin asiri, karami ne gidan dan daga waje ma zaka san ba wani girma ne dashi ba, sannan ba gate bane kofa ce a gidan.
Kallansa tai tace "na gode." Tasa hannu zata bude kofar.
Yace "sunana Sageer, dan naga kamar bai dace mu rabu ba wanda yasan sunan dan uwansa."
Juyowa tai ta kalleshi sannan tace "nagode."
Ta bude kofar, har ta sa kafarta bata juyo ba tace "kaji sunana a cikin chemist dincan, sunana Maimuna."
Yace "ohh haka ne ashe naji, amma ya akai na shafa'a?"
Kallansa tai sannan tadan motsa baki ta murmusa kadan sannan ta fita, tare da kara cewa Nagode.
Tana shiga ciki ta tadda Mamanta na wanke shinkafa.
Tana ganinta tace "Maimuna? Ya naga kina dingisawa? Lafiya?"
Kallansa tai kamar zatai kuka sannan ta zauna akan kujera irin ta tsugunnon nan, tace " Mama wani dan......." sai kuma tai shiru kafin tace "bigeni akai a hanya, ai nikam kafin na kara zuwa gidan yaya