ย  ย  NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 143 of 172

Tace "yanzu ka yanke?" Yace "Umm haka kawai naga barin mu nan shikadai ne zaisa mu kebe, kinga kafin mu dawo sai na fadawa Abba a nemo mana gida." Dariya ya bata, pillow din data daura hannunta akai shita dauka ta sa a saman fuskarsa tana dariya tace " gaskiya yaya ba kunya a harkarka, saboda haka kawai kake san tafiya?" Pillow din ya turo yasa hannunsa a saman wuyanta ya jawota daf dashi yace "bakya tausayina Jalila?" Tace "Tausayin me kuma?" Ya kara marairaice fuska yace "bakya tausayawa zuciyar dake san ganinsa manne da matarsa?" Tana dariya tace "mene?" Yace "nikam tafiya zamuyi, Allah yasa kafin mu dawo Sageer yayi aure ya tare saman." Jalila tana dariya tace "wato shi ya zauna kai ka gudu ko?" Yace "a'a shima yadan dana kadan sai mu gudu dukanmu." Jalila ta girgiza kai tana dariya tace "ni dai gaskiya so nake na sauka kasa Allah kunya nakeji aga ban sauko ba." Ya daga ta tare da hade fuska ya koma ya kwanta akan pillow. Hannu tasa ta taboshi tace "fishi kai?" Ya kalleta yace "abani cin hanci na fita ko kuma inje in nemi izinin zama da matata." Jalila tai dariya tace "kace me?" Yace "mu gwada mu gani?" Da sauri ta sumbaci kuncinsa tace "inje?" Kai ya daga mata yana murmushi. Ta kalleshi sannan ta fita. Tana rufe kofa ta kalli dakin sannan ta murmusa tace "Yayah!" Sannan ta sauka. Kunya ta kamata dataga Ameera da Ummy sun gama aikin breakfast harsuna jerawa akan dinning cikin kunya ta karasa tace "Ummy ina kwana?" Ummy tace "Jalila kin fito? Ai da kinyi zamanki ma Ameera anjima zata kaimuku abincinku." Jalila da sauri ta amshi kayan hannun Ummy tace "a'a Ummy." Ameera ta guntse dariyarta. Jalila ta shiga maka mata harara...... Bata dade da fita ba ya mike daga kan gadon ya gyara sannan ya dau wayarsa ya sauko. Tana kokarin hawa sama ta kirashi sai gashi. Ummy ya gaida tana amsawa Abba ya fito daga daki ya gaisheshi. Sageer ma ya matso suka gaisa yana cewa "jiya nikam bansan sanda ka dawo ba." Hassan ya harareshi sannan yace "Ummy nikam a sama zanyi breakfast." Da sauri Jalila ta kalleshi. Ya dauke idanunsa yana kallan Abba wanda ke cewa "gaskiya ne, a basu abincinsu in yaso juma'a sa dinga saukowa." Ummy tace "kuma hakan yafi ko saboda ma Jalila bazata sake anan ba." Hassan ya kalli Jalila yaga yanda tai tsuru tana kallansa. Dariya ya kamashi ya guntse ya kalli Sageer yace "Malam gauro aci abinci lafiya." Sageer yai dariya yace "gauron ma ya kusa yin zuciya ya kama nasa." Hassan yai sama yana dariya. Ameera ta kalli Jalila tace "Aunty Jalila ga naku nan dama Allah yaso Ummy ta ware muku." Ta matso kusa da Kunnenta tace "oh su yaya ba kunya." Jalila tasa kafa ta taka ta. #OneLuv๐Ÿ’• [12/30/2018, 10:06 PM] El-hajj: ๐Ÿ—ฏ *JALILAH* ๐Ÿ—ฏ Written By : *AYUSHER MUHD* Wattpad: *Ayusher Muhd* *HASKE WRITER'S ASSOCIATION* *68* Tana ajiye tiren abincin ya sa hannu ya jawota ta fada jikinsa, kallansa tai tace "Yaya?" Yace "me? Bakiso na fadi haka ba?" Tace "taya zakace haka bayan kasan yanda su Ummy kijin dadin cin abinci dakai?" Ajiyar zuciya yai mai sauti yace " nikaina ba haka naso ba, to amma ya zanyi? Na kasa jurewa." Tace "ka kasa jure me?" Jawota yai ya kara rungumeta yace "nafisan na jimu shiru." Dagowa tai ta kalleshi tace "yaya? Nikuma tsoro nake ai." Yace "tsoron me?" Tace "naji ance duk ma'aurata farkon aure ne kawai miji ke nuna musu so, amma da zarar sun shekara daya, biyu zuwa uku zai canza mata, wani maganar mutunci ma ba samu zatai ba." Yanda yake jinjina kai yana tabe baki ne yasa tace " Da gaske haka ake cewa." Ya karkata kai yace "ohhh haka ne kenan?" Tace "mene?" Yace "ban taba ji ba amma yanzu da kika fada da alama na fahimta." Kallansa tai a tsorace tace "me ka fahimta?" Dagata yai daga jikinsa ya zauna gaban abincin da ta kawo, ya nuna mata tare da cewa "matso muci abinci, yunwa nake ji." Kallansa tai jikinta duk yai sanyi, a hankali ta matso ta zauna tace "Yaya bakace komai ba." Yace "me kikeso nace?" Tace "Hmm abinda ke ranka." Yace "bakomai a raina." Kallansa tai tace "bakomai?" Yace "sosai, saboda labarin rayuwar wasu can daban kika bani wanda banida hadi dasu." Tace "yaya Goggo....." Yace "Jalila?" Yanda ya kirata ne yasa tace "naam." Yace "ya sunana?" Tace "Ya..." Yace "ba wannan ba ya sunana?" Tace "Hassan?" Yace "gud, mahaifinki fa?" "Abubakar." Yace "toh, banaso a rayuwata dake ki dinga hadashi da rayuwar wasu da kikaji ko kika gani, koda kuwa rayuwar mahaifinki ce, ni nine, sannan ke kice, bansan mace ba, ban taba magana mai tsayi da wata mace ba bayan mahaifiyata, ko Ameera kina ganin yanda muke magana, ke kadai na sani, so Please inaso ki daukeni a yanda na daukeki, nasan haryanzu baki saki jiki dani ba wanda nasan a hankali ni zan canza wannan, amma banaso ki dinga sako rayuwar wasu a cikin tam
๐Ÿ