NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 139 of 172

e yake shirin yi da yamma nan, gari da haske? Jitai yace "kin manta spots din nan?" Kallansa tai tace "name??" Yace "ko ayi sai a tuno?" Da sauri tasa hannu tadan tureshi kadan tana dariya tace "ba ruwana." Yace "au baki manta ba ashe neman magana ne." Da sauri ta bude kofa tana dariya, ta shige ciki. Goggo na ta kara karfafa kafarta tana ta yawo a tsakar gida, lantana na falo ana ta kallo ana yanka alayahu, Jalila ta budo kofa. Goggo cikin mamaki ta kalleta tace "Jalila!" Da gudu Jalila ta karasa ta rungumeta, tace "Goggona!" Goggo ta shafa bayanta tace "haryanzu ba'a girma ba?" Jalila ta kara kankameta tace "shine zakiyi tafiya ba rakiya." Hassan daya shigo ya tsaya yana kallanta, Goggo tace "Hassan sai kayi hakuri wannan matar taka inta samu gu akwai sakalci da shagwaba." Da sauri Jalila ta dago, ta kalleshi, dan batasan ya shigo ba. Sake Goggo tai cikin kunya ta boye a bayanta. Hassan ya karaso ciki, Goggo tace "muje falo." Lantana tanaji alamu ta dauke kwanan alaiyahun ta shige kitchen. Hassan ya shiga yana murmushi, Jalila na rike ta baya da rigar goggo. Da zata zauna tasa hannu ta ture hannunta tace "to ai abarni na zauna ko?" Jalila ta saketa tare da zama a kusa da ita. Hassan ya kalleta yace "ikon Allah! Malama a barta ta sake mana." Jalila ta noke kafada alamar a'a dariya ma ta bashi ya kalli Goggo sannan ya gaisheta ta amsa tana cewa "ai kanada aiki, dan wannan in ta samu guri...." A ransa yace ai haka nake so. Amma a fili kawai murmushi yai yace "tafiya kuma tazo." Tace "wallahi, ai in ba zuwa nai ba hankalina bazai kwanta duka ba." Yace "Hakane, Allah yasa a taradda alkairi." Tace "Ameen." Nan ta tambayi su Ummy da mutanen gidan, suka danyi hira, Jalila na makale da goggo. Goggo ta kalleta tace "tashi ki taya lantana ayi sauri a gama abinci yaci." Ta mike tai kitchen. Basu dawo ba sai da sukai sallar magrib, da zasu tafi yaba Jalila kudi ta kai mata, da kyar Goggo ta amsa tanata cewa ai Ummy ta bata wasu, taira godiya kamar ranta zai fita. Tana mamakin wadan nan mutane da halinsu, lalai haihuwa ta biya mata, ko a mafarki bata taba kawo kanta cikin wannan halin ba...... #OneLuv💕 [1/12, 9:39 AM] Maryam: 🗯 *JALILAH* 🗯 Written By : *AYUSHER MUHD* Wattpad: *Ayusher Muhd* *HASKE WRITER'S ASSOCIATION* *66* A hanya hannunta ya jawo ya rike yana tuki da daya hannun, shiru tai kawai tana tunanin yanda taji haushin mutumin nan sanda ruwa ya daketa, lalai inkaga mutum ka kalleshi, ikon Allah baya karewa a rayuwarnan. Kallanta yai yace “me kike tunani?” Tace “kawai!” Yace “ni sai yaushe za’a fara mannemin kamar yanda akema Goggo?” Ta kalleshi sannan ta sunkuyar dakai tace “manne mata nake?” Yace “umm, gashi ni kuma abin birgeni yakeyi, a taimaka a faramin irin shi.” Dariya tai tana kallanshi tace “lalai yaya! Nikam bansan ya nakeyi ba.” Hade fuska yai tare da sakin ajiyar zuciya yace “ya zanyi? Da alama sai na jira.” Tace “sai ka jira me?” Kallanta yai tare da kara hade fuska yace “ ya na iya?” Shiru suka danyi har sukai tafiya mai dan nisa kafin yace “Jalila haryanzu bakiyi tunanin komai akan maganar Abba ba?” Yai maganar yana murza hannunta.” Ta kalleshi cikin kulawa tace “ko kara kawoshi a raina ma banyi ba, ai na fada ma duk yanda kace haka za’ayi.” Iska yadan furzar kadan yace “ina san mubar gida mu zauna mu biyu amma bana sha’awar barin kasata, sannan banasan tafiya nabar family na.” Shiru tadanyi kafin tace “ka duba kaga abinda ya dace, ni duk abinda ka yanke daidai ne a gurina.” Kallanta yadanyi kafin ya karkatar dakan mota kan layinsu, yace “ nagode Jalila, na tabattar akan dukan lamurana yanzu am not alone.” Murmushi tamai tare da saukar da idanta kasa. Cikin gidan suka shiga yai parking din motarsa tare da kashe ta, kallanta yai yace “muje ko?” Tace “hannuna...” Yace “au.” Sannan ya saketa, kallansa tai tace “na dauka yanzun ma cemin za’ai, kin tabbatar ba ke kike san na rikeki ba?” Tai maganar yanda yake magana, girman idanunsa yadan rage yace “haka nakeyi?” Tace “eh mana.” Yace “sakemin naga?” Tai gyaran murya kadan tace “kin tabbatar ba ke kike san........” Bakinta ya sumbata tai saurin zaro ido tare da kallansa, sannan ta waiwaiga wajen window, yace “ya akai? Kunya kike?” Tace “yaya? In wani ya ganmu fa?” Yace “hmm to menene a ciki? Mukai a wajen gidan goggo ma bare cikin gida?” Da sauri tasa hannu ta toshe ma baki tace “oh ni Habiba!” Kafadarsa ya daga alamar ko a jikinsa kafin ya nunamata bakinsa da hannu. Sakarmai baki tai ta turo bakinta tace “yaya dan Allah ka daina zancen wajen gidan Goggon nan tun kafin mu fada a inda za’aji.” Yace “ahh ta ya za’ace indaina zancen rana datake special a gurina?” Idanu ta kuramai k
🏠