NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 138 of 172

e aiki a lokacin ta shiga duba halin da Inna ke ciki. Sai da suka dade dan har Mumy tayi kuka harta gaji kafin su fito. Kallan Mumy wacce tana ganin likitan ta fito ta taso da sauri, tace "Doctor menene ya faru da Innata?" Murmushi ta mata tare da dafa kafadarta tace "ki shiga tana ciki, in kin gama ki sameni a office zanga wasu patient ne." Da sauri ta shiga ciki, Dady ya bi bayanta. Inna na kwance tana bacci, ansa mata abu a hancinta, Mumy ta zauna tare da rike hannunta tana hawaye. Wayarta da tun suna mota taketa kara ta kalla, zaro ta tai a jaka tare da duba mai kiran. Number Safeena ce a hankali ta daga tare da cewa "Safeena!" Kuka kawai taji ansa mata, hankali a tashe tace "Safeena? Menene hakan?" Safeena cikin kuka take cewa "Mumy ki taimakeni, dan Allah ki zo ki daukeni daga garin nan ko kice in taho." Hankali tashe tace "Safeena menene hakan? Ke da kika tafi karatu?" Tana kuka tace "gaba daya ni banajin dadin komai a garin nan, ban iya komai ba, dan komai yi min ake anan, ni ba kawaye ba kowa baya sona, gaba daya komai yamin zafi, wallahi ni karatun ma ba gane shi nake ba, Mumy ki taimaka ki ce na taho inba haka ba Allah zakuyi dana sani." Cikin tsananin tashin hankali ta mike tsaye tace "Safeena! Karkiyi komai na rokeki da Allah, naji koma menene ni zan dauki laifin ki shirya ki sai ticket ki taho, koma menene ayi daga baya." Safeena tasa kuka tace "nagode Mumy!" Kafin Mumy ta sake magana harta kashe, Dady ne yasa hannu ya rikota yace "menene ke faruwa? Me makwan ki lalasheta sai kice ta taho?" Tace "to ya zanyi? Cewa tai wallahi zamuyi dana sani, intai abinda bai kamata ba fa?" Yace "ke bakisan birgar yara ba? Bakisan halinsu ba kenan? Tayi ne dan dama ki tsorata." Tace "Dadyn Yasmeen in kuma ba hakan bane ba fa?" Yace " amma yarinya akaita wata kasar ki sa ta dawo? Kudin da aka kashe fa?" Mamaki ya kamata tace "kudi? Mu daina musu anan, Inna na kwance, amma nikam ya akai Inna ma ta shiga wannan halin?" Shiru yai kafin ya jawota jikinsa ya rungume yace "ina lekawa na ganta a haka, bakisan tashin hankalin dana shiga ba." Hawaye ne ya zuba mata tace "nagode ma Allah ma dayasa ka shiga da bansan ya zamuyi ba." Dady ya kalli Inna tare da runtse ido..... ************ Yana gaba tana binshi a baya suka fara sauko wa, harya kai steps na hudu tace "yaya? Me zakacema su Ummy?" Yace "ke zakiyi musu bayani ai." Ta saki baki zatai magana taga har ya yi nisa, da sauri ta sauko. Suna falo a zaune anata hira, Ameera ta zake sai labari take basu. Sageer sai dariya yakeyi. Suka sauko, Ummy ta kallesu tace "za'a fita ne?" Yace "eh Ummy dama...." Bata jira ya cigaba ba tace "a dawo lafiya." Yace "sai mum dawo." Sageer yace "Yaya ba neman Ameera tai rakiya?" Harararsa yai yace "yau ba islamiya ne?" Tace "yau fa friday yaya..." Yace "oh ba'azuwa yau?" Tace "eh!" Ya juya ya fita, Jalila kanta a kasa tace "Ummy!" Ummy tace "a dawo lafiya Jalila" Ameera tai dariya, fitowa tai ta taddashi a gun Mamman da alama makullin ya ansa sannan suna magana. Yana ganin ta karaso ya bude motar da key din hannunsa sannan suka cigaba da magana. Itakam shiga tai ta zauna tare da kallansa yana magana, ta tabbatar da dane gaisuwa ma dakyar zata hadasu. Can ya taho itakam ta saki jiki tana kallansa, sai dataga yazo jikin motar ta sauke idanunta da sauri. Bude motar yai ya shiga tare da kallanta ya kunna motar suka fita. Sun danyi shiru kadan kafin yace "Kinsan wata rana da kika taho cikin ruwa, kina kuka?" Tace "ni? Yaushe?" Yace "ranan dana fara ganinki amma ke baki ganni ba." Kallansa tai da sauri tace "kaine dama wannan dan......" Sai kuma tai gum, sai kuma tasa dariya tace "dama kaine?" Ya kalleta sannan yace "kinsan nasan kin zageni a lokacin?" Tace "ni?" Yace "sosai dan na ganki a adaidaita ma kina harare harare, da yan maganganu." Kallansa tai tace "inalilahi..." Ya kalleta kawai tare da mai dakai kan titi yace "ban taba tunanin mara kunyar nan itace wacce ake nemamin ba." Tace "Allah inada kunya." Yace "ai da nake nufi, dan haka na daukeki, sai dai in aka duba abin nine na miki ba daidai ba, ta ya ina ganinki cikin wannan halin amma nai ignoring dinki sannan naji haushi dan kin hararen?" Ta kalleshi tace "nima ai ban kyauta ba, menene nawa nasan wanda ban sani ba ya taimaka min?" Yace "kuma fa haka ne." Dariya tai tace "lalai yaya ba kara?" Yace "karar kenan, fadar gaskiya." Ita kanta mamakin yanda suke hira tai har suka isa kwanar gidan, wani shago ya tsaya yace suje sudan siyo mata abinda zata kai kauye, Jalila tace "kamar me?" Yace "ina na sani?" Tace "nima wlh ban sani ba kaga ban taba zuwa ba." Yace "to kawai mu bata kudin gobe in zasu tafi sa biya ita da Mamman su siya." Tace to. Nan suka ja mota. A kofar gidan sukai parking, matsowa yai gaf da ita, ta zaro ido tana kallansa cikin mamakin m
🏠