NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 137 of 172

yake ta ajiye sannan ta zauna kusa dashi tace "Ummy tace na kawo......" Jawota yai ya rungumeta tare da sakin numfashi, a hankali yace "ya jikin?" Tace "da sauki." Saketa yai sannan yasa hannu ya jawota kan cinyarsa tare da sakala hannunsa ta cikinta, kansa ya zuro ta kafadarta ya dan kwantar kadan yace "Jalila me kike tunani akan maganar Abba?" Tace "Kaine zakai tunanin abinda kaga ya dace, ni ko me ka yanke yayi a guna." Hannu yasa ya juyo da fuskarta saitinsa a hankali ya sumbaci bakinta yace "kinyi kyau wanda har ji nai kamar na jawoki jikina." Idanunta ta dago ta kalleshi tace " ya bakai ba?" Yace " oh kumafa haka ne, ya akai banyi ba?" Tace "ah haba nima ai wasa nake." Yace "wasa? Nikam ba wasa nake ba, next time ki bini bashi." Idanu ta zaro tace "da gaske sai kayi?" Yace "ah ba matata bace?" Kallan mamaki tamai tace "agaban su Ummyn? Su Abba?" Yace "Uhm Hmm....." Baki ta saki tana kallansa, nashi bakin yakai ya sumbaceta kallansa tai. Yace "me? In kara ne?" Tace "kai yaya." Fuska ya hade yace "wai ne menene hadinki da sunan nan?" Tace "wai to meyasa bakaso?" Yace "ah ni yayanki ne? A yaushe na zama yayanki?" Tace "to ba duk haka aka cema ba?" Yace "inji wa?Ummy Hassan take cemin haka ma Abba, Sageer da Ameera ne ke cemin haka." Tace "to ni me zance ma inba haka ba?" Yace "oho amma nidai banasann sunan." Kallansa tai ta sakarmai wani murmushi tace "to ya...." Sai kuma tai gum... (Nace samun gu su Hassan🤔) #OneLuv💕 [1/12, 9:39 AM] Maryam: 🗯 *JALILAH* 🗯 Written By : *AYUSHER MUHD* Wattpad: *Ayusher Muhd* *HASKE WRITER'S ASSOCIATION* (_D home of expert and perfect writer's_💡) *65* Idanu ya kafeta dashi, tace "to ni wlh...." Katseta yai yace "shikenan fadi abinda ya miki nima zan fadi abinda yamin." Ya dagata daga jikinsa ya mike, da sauri ta sa hannu ta rikoshi, kallanta yai fuskarsa a sake yace "menene?" Tace "haushi kaji?" Yace "ko kadan, banasan ne na takura miki akan abinda bakyaso." Tace "baka fahimceni bane yaya bawai banaso bane." Sai kuka tai shiru tana kunyar tace batasan me zatace mai ba. Kallanta yai yace " mubi komai a hankali, gaba dayanmu a new to this, kar muyi rushing, let's take it slowly. Kinji?" Yai tambayar yana kallanta, kafin yace "it look like kamar ni nake rushing dinmu." A hankali tana kallansa tace "a'a yaya, ko kadan ba haka bane." Ya daga kai alamar fahimta, kafin ya dan rungumeta na wasu sakan ni sannan ya saketa ya nufi toilet. Zama tai tare da yin ajiyar zuciya, ta sa hannu akanta tare da cewa "duhun kai baiyi ba wlh, ni yanzu sunan ma dazan cemai kadai bansani ba?" Kwanciya tai rigingine tare da sa hannunta a saman goshinta tace "Goggo na!" Hassan kuwa yana fitowa ya shafa mai a hannunsa ya sa turare, kallanta yai itama ta kalleshi sannan ta mike zaune, yace "kin gaji ko? Naga kunsha girki." Tace "a'a bayan duk Ummy ce tai sama da rabi." Ya matso tare da daukan agoggonsa daya cire daya shigo yana sawa yace "Ki sha abarbar." Tace "Ummy ce tace na kawo ma fa?" Yace "itama Ummy wasa takeyi tasan abarba bata dameni ba inasha amma ba sosai ba tun ina yaro." Cikin mamaki take tunanin to meyasa Ummy tace ta kawo mai? Kallanta yai yace "nasa a dauko mun motata inaji yanzu ta iso, ko zamu ki gaida goggo?" Da sauri tace "da gaske?" Yace "eh, naji zatai tafiya gwara kije kafin ta tafi." Tace "bayan ko fadamin batai ba." Wayarsa ya dauka yace "to tunda bazaki ba bari ni naje." Da sauri ta mike tace "zani zani." Murmushi yai tare da yin gaba. *************** A zabure Inna tace "me kace?" Dady yai murmushi tare da ajiye mata takarda yace "Yanzun nan muka dawo daga gun lawyer 'yarki tamin transfer na shares dinta, shine nace bari na sanar dake karkiji a gari kiji ba dadi." Hannunta ne ya shiga rawa ta na kokarin daukan takardar, Dady yasa hannu ya dago mata tare da mika mata saitinta yace "gashi! Shiyasa yanzu nake tunanin kamar zan iya kwatar matsayin da aka hanani, dan yanzu na fiki shares a company din balle in na hada dana Safeena da Sultan, tunda jininane su, ni an hanani saboda ni ba jininki bane yanzu fa?" Inna kam takardar kawai take kallo ga kalamansa na ratsata, kanta ne yadau wani irin zafi sai gani nai tayi baya luuu..... Dady ya mike tsaye a tsorace tare da kwallawa Mumy kira, ya boye takardar a aljihu, gabansa na wani faduwa saboda tsoro karyaje ya zama ajalinta. Mumy wacce ke kwance akan kujera tunda suka dawo ta mike da sauri a zabure ta hawo sama. Ganin Inna a kwance yasa ta kwalla kara tare da kallansa tace "mu kaita asibiti, in wani abu ya samu Inna banaji zan iya rayuwa...Nashiga ukuna." Da sauri ya kinkimeta sukai kasa, a rikice suke dukansu, a mota ya sata suka ja sukai gaba. A cikin asibitin Standard suka tsaya, Mumy rungume da Inna sai kuka take kamar ranta zai fita. Suna shiga aka amsheta, nan likitae dak
🏠