NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 135 of 172

vella da Billy Giro Novel...._ *64* Yanda ake ta shiga cikin masallacin ga wasu sunata sa sallaya a waje, wasu akan tabarma, wasu kuwa ma a haka suke tsayawa, anata huduba,Hassan ya kurawa mutanen ido zuciyarsa na wani irin bugawa, Abba ya sa hannu ya riko hannunsa, sannan ya kallu Sageer yace "muje?" Sageer ya daga kai tare da cewa "Yaya yau sai mu rubuta ta cikin tarihi." Hassan yai murmushin yake, haka Abba ya rikeshi, Sageer na rike da babbar sallayarsu, masallacin ya cika dan haka daga baya ya shimfida musu sallayar, Hassan zuciyarsa na ta sake rauni, yana neman yafiya gun Allah akan rashin ziyarta dakinsa dayai na shekaru haka masu tsayin gaske. Haka suka je suka zauna sunajin huduba, a hankali wasu zafafan kwalla suka gangaroma Hassan, dan a iya tsawon hankalinsa zaice bai taba jin huduba haka ba sai dai dayake yanajin na saudiya a waya amma bai taba ji zahiri haka ba, Abba ma ji yai gaba daya jikinsa yayi sanyi, hannu Sageer ya sa ya dafa kafadar Hassan. Hassan ya kalleshi cikin wani yanayi na jin dadi da tausayawa, ji yai ya fara yi masa addu'a a ransa "Allah ka kare wannan yaran, ka biyamai bukatunsa na alkairi, ka kareshi daga sharrin masu sharri, ka bashi mace ta gari wacce zata so shi ta kuma kaunaceshi fiye da tunanin mai tunani." Ganin yanda yake kallansa yasa Sageer yace "yaya." Hassan ya maida kansa kasa kawai baice komai ba, har lokacin sallah yai sukai sallah sannan suka shiga mota. Abba yace "yanzu mu wuce gida? Ko da wani abun?" Hassan ya kalli Sageer yace "kanada abinyi? Ni dai gidan nan nafi san zuwa." Abba yace "gida kafisan zuwa ko gun matarka?" Hassan ya kalli Sageer, shikam dariya yai yace "da alama Abba ka gano yaya, dan na kula ya gama matowa." Ganin yanda Sageer yai ne yasashi yin murmushi kadan yace "Abba ba haka kakeso ba dama?" Da sauri Abba yace "ka gama magana dan kuwa hakan shine buri na." Nan Hassan ya tada mota dan dama yanzu shi ya karbi tukin, Yace "Sageer kai fa? Har yanzu ba labari?" Abba yace "ni kaina na matsu inji labari, ya? Haryanzu dai?? Gashi har zaka fara aiki." Sageer yace "in nayi auren ina zan sata?" Da sauri Hassan yace "Sama, dan ni......." Yanda Abba ke kallansa ne yasa yai shiru tare da waskewa yace "ni sai in barma saman." Dukansu sun gane me yake nufi, Sageer yace "ayi haka kuwa?? Ba gwara ni in fita ba ko kusa ne sai na nema?" Da sauri Hassan yace "a'a kaga kaine karami kana......." Dariyar da suka samai ne yasa yai shiru tare da cewa "ya akai?" Abba yace "wato kafisan kaganku ku biyu?" Hassan yai gum tare da cigaba da tukinsa, Abba ya mai nuni da fruit suka tsaya suka siya. A cikin gida yai parking, suka fito. ********** Jalila kuwa bayan ta fito Ummy ta kaida ita daki ta sata ta shafa janbaki da kuma kwalli, tana sawa kusa ta fito das, Ummy tace "ko ke fa? Ki dinga yin wannan simple makeup din amma ba daga mai sai powder ba." Jalila tace to a kunyace, Ummy ta fito tana cewa "Jalila fito ki tayani mu karasa, nan Jalila ta fito da sauri dankwalin na saman kanta, haka suka karasa girki dan dama Ummy tayi kusan rabi, suna jerawa a dinning Ameera ta dawo, tsalle tai tana kallan Jalila tace "gaskiya ne Matar Yaya irin wannan kashe kala?" Jalila ta maka mata harara tace "to hajiyar sa ido." Ameera ta ajiye jaka da hijab ta matso kusa da Ummy ta gaisheta da gida sannan ta gaida Jalila da gida tace "amma an samu matsala da daurin dankwali." Jalila ta matso kusa da ita tace "ai anan matsalar take." Ameera ta sa hannu ta rikota tace "Ummy muna zuwa." Jalila ta tirje tace "bari mu karasa jerawa, ko?" Ameera ta saketa sannan itama ta fara neman tayasu, Ummy tace "dama kin barshi dan ana gama ci zakiyi wanke wanke, sannan kiyi abincin dare." Kallan Ummy tai da sauri tace "duk ni kadai?" Ummy tace "ko dani za'ayi?" Ameera tace "a'a!" Jalila tasa dariya dan yanda tace a'a abin dariya. Suna gamawa taja hannun Jalila sukai daki, zata fara yi mata Jalila tace "tsaya ayi a hankali dan na koya." Ameera tace to, nan ta fara mata a hankali tana gani, suka gama aka sake warewa aka sakeyi, Ameera tace "yauwa Matar Yaya yanzu kinfi kyau." Jalila tai murmushi tace "Allah yasa na iya daurin da kaina." Ameera tace "ai ba wuya zaki iya." Nan ta kara sa dan sosan hoda ta gyara fuskarta, jin magana a falo yasa ta kalli Ameera da sauri. Ameera tace "Mai Sanyinki ya dawo." Jalila ta mintsineta tace "wallahi zan fadamai sunan da kike cemai." Ameera tace "na tuba ayi hakuri." Nan Jalila tai dariya, Ameera ce ta cire kaya ta sa wasu tana cewa "ba wanka dan wallahi sanyi nakeji." Jalila tace "ni dai sa mu fita tare dan kunya nake." Ameera ta sa riga yar kanti doguwa zuwa gwiwa sannan tasa wando pencil tasa mayafi, ta kalli Jalila tace "ya kamata muje kema mu samo miki kayan....." Ta wani kanne ido, Jalila ta zuba mata ido can tace "wai ni Ameera a gidan wa kika san komai haka? Gaba daya ni
🏠