NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 133 of 172

allo, yana san yarinyar nan har baisan wani irin so yake mata ba, ko dan a rayuwarsa bai taba zama da wata mace bane daga Ummy sai ita? Dan Ameera ma saboda matsalarsa basu samu sun shaku ba. Jalila ta kwantar da kanta tana kallansa, batasan me yasa ba, tanasan taga murmushi a fuskarsa. Ganin yanda take kallansa ne yasa ya ajiye wayar ya mike a hankali yazo inda take, tsayawa yai yana kallanta kafin yace "Kallan fa?" Tace " kawai mamaki nakeyi ne." Yace "mamaki na ko?" Kai ta daga alamar eh, yace "in zan zuba mana abinci me za'a biyani dashi?" Tace "kamar ya?" Yace " dazu ma nace a daina cemin yaya kuma har yanzu an kasa dainawa, karfa biyan bashi ya miki yawa." Tace "a'a ni bari na zuba da kaina, me yai zafi?" Ta fada tana neman mikewa, hannu yasa ya maidata yana murmushi yace "just joking, amma na yanzu." Bargon ya yaye ya miko mata hannu, kallansa tai ya mata alama data kama hannunsa, nan tasa hannu ta rikeshi, a hankali ya taimaka mata ta sauka, gun da suke cin abinci ya karasa da ita sannan ya zaunar, shima ya zauna.Kular ta bude, plantain ne aka soya aka dora soyayyan wainar kwai a sama, dayan kular kuma anyi potato ball, sai farfesun naman rago. Zubawa tai a plate, sannan ta matso mus da plate din tsakiya, kallanta kawai yakeyi har ta gama sannan yai bismillah ya fara ci. Itama ta fara ci, sunyi shiru suna cin abinci sai dai kallon juna da sukeyi jefi jefi, in suka hada ido kuma sai su saki murmushi a tare. Ya kalleta yace "kin samo sunan da zaki fada min?" Tace "wlh ni yaya......" Kallan daya mata ne yasa tai shiru tana cewa "oh ni..." Jitai yace "me kike cema Sageer?" Kallansa tai kawai tasa dariya, tace "oh ni, shi fa uncle din mu ne dama haka muke cemai." Bai kara magana ba ya cigaba da cin abincinsa, sai dai yanzu ya daina kallanta. Har suka gama cin abinci, ya mike yace "bari nai wanka." Ta daga kai alamar to, ya wuce toilet. Murmushi ta bishi dashi sannan ta hada kwanukan, mikewa tai ta gyara gadon sannan ta dan kara kimtsa dakin, kofar ya turo hangota yai tana gyara gun kujera tare da maida littafin dayai amfani dashi, a hankali ya tako inda take, ita kuma jin motsin kofa yasa tace "yaya ka fito?" Sam batai tunanin yazo inda take ba, ta sukunya tana ajiye littafin taji ya sanya hannayensa ya zagayo cikinta, tsayawa tai cak dan batai zaton jinsa haka ba, a hankali ta juyo ta kalleshi sumbatar bakinta yai kadan sannan yace " kinasan kari ne?" Tace "karin me?" Kara sumbatarta yai yace "yanzu fa?" Kallansa tai kamar zatai magana sai kuma tai dariya, ya matso saitin kunnenta yace "Jalila bansan meke damuna ba?" Dagowa tai, ya juyo da ita saitinsa, tace " bakajin dadi ne?" Yace "ko kadan kawai sai nake jina kamar ba ni ba." Tace "jikin naka ne?" Ya zare hannunsa daga kugunta ya sa akan fuskarta yace "ko kadan kawai dai haka nakejina, da alama shekarun dana samu a dukunkune sune nakesan na fanshe." Murmushi tai har hakoranta suka fito tace " haka ake so ka fanshe duka, tun daga yarintar ka data rike zuwa yanzu....." Yanda yake kallanta ne yasa tai kasa da idanunta tana murmushi gaba daya yaya yasa tana neman cire kunyarta. Saketa yai yace "kin tabbatar zaki jure ko?" Tace "zan jure." Juyawa yai yana sa kaya, ta juya tare da zama kan kujera, shadda ya dauko sabuwa, cikin wanda Abba ke yawan dinkamai baya sawa, duk sanda Abba zai dinkama Sageer manyan kaya sai ya dinka masa, sannan dama ko kananan ma shi yake siyo masa. Yayi kyau kamar ba shi ba, ya dauko hula ya saka, ya karasa gaban madubi ya sa turare tare da sa agoggo, Jalila ta zuba mai ido ta cikin madubi, kallanta yai tai saurin dauke idanta, takalmi ya dauko yazo kusa da ita, hannu yasa ya dau wayarsa tare da nuna mata sannan ya dau key yai hanyar waje. Sai dayaje kofa yace "na tafi." Wani lallausan murmushi ta sakar mai sannan ta daga kai alamar to, ya fita tare da turo kofar, idanu ta lumshe tana tuno daren jiya, lalai itakam bata taba kawo wannan yanayin ba, kwanciya tai kan kujerar tare da lumshe idanunta. Knocking din data jine yasa ta bude idanunta, tare da kokarin mekewa, Ummy ce ta turo kofar tana cewa "ba sai kin taso ba Jalila." Ganin Ummy ce yasa cikin hanzari ta mike tana neman tahowa gunta, azabar dataji ne saboda saurin datai yasa tadan tsaya sannan tadan cigaba da takowa a hankali.Ummy tana kallanta ta fahimci lalai danta ya girma, tana karasowa kusa da Jalila kawai ta rungume Jalila. Cikin mamaki Jalila tai tsuru tana san sanin meke faruwa, Ummy tace "Allah ya miki albarka ya kareki daga sharri duk wani wanda yake nemanki da sharri, ya sa aljanna ta zama itace makomarki, ta sa ki gama da duniya lafiya." Jalila a hankali tace "Ameen." Ummy ta saketa sannan ta jawo hannunta suka zauna a bakin gado, tace "kin dan shiga ruwan zafi ne?" Cikin rashin fahimta tace "ruwan zafi?" Tace "zaki iya saukowa? Muje kasa?" Jalila tace "eh." Ummy tace "dauko kayan da zaki saka sai muje kasa." Mikewa tai ta bude drawer kawai kayan dake sama tasa hannu ta jawo, Ummy tai murmushi tace "Jalila atamfar y
🏠