Β  Β  NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 132 of 172

11:30 kina bacci menene damuwar Ummy?" Ganin kamar ma bashida niyyar ganewa tace "nikam yau bansan ya zanyi ba." Tafada tana kokarin sauka. Kallanta yai tana dan dingisa kafa, dariyarsa ya gumtse sannan yace "me zakice ma Ummy in taga tafiyarki?" Gabanta ne ya fadi, ta kalleshi da sauri, tace "yaya nashiga uku? Ya zanyi? Yau nikam na gama yawo." Kara matse dariyarsa yai sannan yace "kawai ki kwanta sai nace bakyajin dadi. Karasowa tai kusa dashi tace "gaskiya kam, yaya ka taimaka kacemata ina zazzabi." Yace "karya fa kenan?" Kallan mamaki tamai tace "yaya kaifa ka fara cewa, sannan ai ba karya bane tunda dai da gaske banajin dadin." Da sauri yasa hannu saman goshinta yace "daga ina ne yake miki ciwo? Nuna min?" Kara shagwabewa tai kamar mai neman yin kuka tace "haba yaya!" Dariya yadanyi sannan yace "ki kwanta bari na sauka kasa." Kwanciya tai tana cewa "yauwa Yaya." Fuska ya hade yace "me zakimin in zan sauka na kai sakonki?" Tace "kamar ya kenan?" Yace "aikena zakiyi naga, to me zaki biyani?" Tace "oh ni yaya, yanzu kuma me kakeso?" Yace "banasan sunan yayan nan, na rasa me yasa kika kama suna kamar ke kika rada min, komai yaya bayan ni ba yayanki bane." Ya mike ya fita, kasa ya sauko Ummy na zaune tana kallo, sai dai idanunta ne kawai ke kan Tv din amma batasan me ake ba, hankalinta nakan su Hassan. Hassan taga yana saukowa, daurewa tai kamar bata damuba ta kara kallan Tv din da kyau kamar bataganshi ba. Harsai da ya kusa saukowa sannan tace "Hassan!" Murmushi ya mata ya matso kusa da ita yace "Ummyna an tashi lafiya?" Tace "lafiya kalau yarona, ina Jalila? Ko tana bacci?" Yace "a'a." Kallansa tai kamar zata sake tambaya, yanda tafa yayi gefe da kansa ne yasa tace "ga breakfast dinku can sai ka daukarmuku." Yace "tam." Kitchen din kawai ya shiga ya dauko musu tiren abincin sannan ya hau sama, yana ajiye wa ya dauko na daren ya sauko dashi. Ummy tai murmushin jin dadi, tace "Hassan, Abbanka yace ka shirya anjima zaizo shiga Sageer kuje sallar juma'a in kuma bai gama abinda yake ba zai kiraka a waya kaje sai ku tafi." Yace "To Ummy." Haryadanyi gaba sai kuma yace "yarinyar nan fa?" Tace "kwana biyu kenan banga kiranta ba." Yai murmushi sannan ya juya ya tafi. ********* Dady cikin bacin rai ya kalli Mumy yace "wai menene hakan?" Kara kwantowa jikinsa tai tace "menene? Ranka ne a bace?" Daurewa yai yace "a'a kawai banajin dadi ne." Hannunta ta zaro daga cikin rigarsa tace " meke damunka?" Yace "menene ma bazai damen ba? Gaba daya ba wanda yake ganina da daraja? Yaran nan bakiga yanda yaci mutunci na ba? Ita kanta yarinyar ba mutunci na take gani ba, Harta employees din company dinmu ba mutunci na suke gani ba." Jiki a sanyaye ta kalleshi tace " ko inma transfer na share dina na company? Ya kalleta yace "so kike Inna ta kara tsanata?" Tace "ba sai ta sani ba, sai muyi a tsakaninmu." Jawota yai jikinsa yace "banaso inzama silar samun matsala tsakaninki da mahaifiyarki." Kwanciya tai a jikinsa tace "karka damu da wannan." #OneLuvπŸ’•[1/12, 9:39 AM] Maryam: πŸ—― *JALILAH* πŸ—― Written By : *AYUSHER MUHD* Wattpad: *Ayusher Muhd* *HASKE WRITER'S ASSOCIATION* (_D home of expert and perfect writer's_πŸ’‘) _Where are u my beloved Wattpadians? A word can't express how much u means to me, when ever i feel down, ur comments always cheers me up.........πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•Luv U AllπŸ’•πŸ’•πŸ’• *63* Yana shiga daki ya kalleta, tana dukunkune cikin bargo wai a dole kar Ummy ta shigo. Hassan ya matso kusa da ita yace "Amarya tashi ku gaisa da Ummy." Kara dukunkunewa tai tana dagamai hannu alamar tanasan magana, guntse dariyarsa yai ya matso kusa da ita gaf da fuskarta. Tana juyowa ta ganshi gaf da ita, idanu ta kifta tare da hadiyar yawu tace "Yaya me ka cema Ummy?" Yace "kamar me kenan kike san ji?" Cikin rada ta sake cewa "ba tare kuke ba?" Yace "ni da wa kenan?" Labanta tadan ciza kamar zatai kuka tace "Yayah Please." Baki yadan tabe sannan ya koma kan kujera yace "Ummy wai ki tafi batasan magan........." Ai bai karasa ba ta yaye da sauri tana cewa "Ummy wallahi ba......." Ganin ba kowa yasa ta hadiye maganarta, kallansa tai cikin mamaki, gani tai bashida niyyar kallanta, waya yake danna wa. Jitai kamar tasa kuka, lalai yayan nan, wato dama rashin lafiya ce ta rikeshi zolaya da tsokana ce fal cikinsa? Gaba daya ma kamar baisan tanayi ba, haushi ya isheta ta koma ta kwanta. Dariyarsa ya guntse sannan ya kalleta, yace "Amarya yaushe zaki bani abinci ne? So nake na shirya kafin sallar azahar." Juyowa tai bangaren da yake, ta hade fuska wai a dole tayi fishi ta kalleshi. Kallanta yai yace "Allah daga na irga yan mintina ba'a ban abinci ba bazanci ba." Mamaki ya kamata tace "da gaske sai ka ki ci?" Yace "Ko zamu gwada?" Batasan sanda tai dariya ba, shima dariyar yai kadan a ransa yace "u smiled." Amma a fili ido kawai ya kura mata yana k
πŸ