NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 131 of 172

tace "zan iya fa." Ya saketa sannan ya shiga toilet shima, sai daya fito ya kalleta tana kan kujera a zaune, yau ma towel dinshi a kasa ya daura, yau kam sai taga ta rage kunyar kallansa, sannan ko ita datai wanka towel ta fito dashi sai dai ta yafa wani a samanta. Kallanta yai yaga tana kallansa yace "ya ya? Yanzun ma so ake akwanta?" Yanda yai maganar ta gane me yake nufi da sauri ta dauke idanunta, sai daya sa riga jalabiya sannan ya matso yace "let's pray." Tace "nayi isha'i ai." Yace "na godiya ga Allah." Bata musa ba ta mike da kyar, hannunsa ya miko mata ta rikeshi suka karasa, sallah sukai raka'a biyu, ya danyi addu'oi sannan ya kalleta, mikewa yai kawai yazo kusa da ita, tana neman yimai magana sai jitai ya dagata, kan gado ya ajiyeta sannan ya zubo musu abinci a plate, yasa spoon daya. Kusa da ita yazo ya zauna ya fara ci, kallansa tai tace "yaya nimafa yunwa nakeji." Yace "au ai ma dauka ke bakyajin yunwa." Hade fuska tadanyi, ganitai ya debo a cokali ya miko mata, baki tadan turo tana neman yin magana. Sumbatar bakinta yai ta kalleshi da sauri, yace "bude" Bakin ta bude tana kallansa, haka ya dinga ci yana bata, bayan sun gama ne ya zauna kusa da ita tare da kwantar da ita kan kafadarsa, ya rufe musu kafa da bargo sannan ya sa hannunsa cikin naga, shiru sukai na wasu mintina kafin taji yace " bacci?" Tace "a'a kawai tunanin rayuwa nakeyi." Shiru sukadanyi kafin yace "mene daga ciki kike tunani?" "Hmmm yanda kawai rayuwa ta juyamin." Ya dan kwantar da kansa a saman nata yace "yaushe kika san Sageer kanina ne?" Ta dago ta kalleshi tace " sanda yazo gidanmu kawo sako." Yace "ya kukai?" Tace "kawai fa kasan me? Na fito inata yan kunkunina wai ina zuwa falo naga Uncle? Mamaki ya kamani, shima yana ganina..........." Yanda Hassan ke kallanta ne yasa tai shiru, sannan tai dariya tace "bacci nakeji." Da sauri ta kwanta ta lulube kanta da bargo. Shiru yai kafin yace Sageer am really sorry. Ya dade a zaune hartai bacci kafin shima ya kalli agoggo karfe 2 saura, yaye bargon yai yana kallanta tanata baccinta kafin ya sunkuyo ya sumbaci goshinta, sannan ya kwanta ya jawota jikinsa. Yau kam zai iya cewa bai tabayin bacci mai dadi kamar nayau ba, dan sallar asuba ma makara sukai. Sai karfe bakwai na safe ta farka, tana kwance a daga gefe da alama garin dadin bacci ne har ta matsa daga kusa dashi, juyowa tai ta kalleshi, batasan sanda murmushi ya bayyana a fuskarta ba, juyowa tai ta kalli agoggo, karfe bakwai? Badai yaya ganin tanata bacci bane yasa bai tashe ta ba? Mikewa tai sam ta manta da jikinta, tana mikewa da karfi taji azaba, da sauri ta koma ta zauna, sannan ta sauka a hankali, tana bude toilet ya bude idanunsa, yana ganin yanayin gari ya kalli agoggo da sauri. Istigfari ya hau yi kafin ya mike, tana fitowa ya shiga, mamaki ne ya kamata, yau yaya ne ya makara? Daren jiya ta tuno, kunya ya kamata, da sauri ta shimfida sallaya tana neman tada sallah. Gani tai har ya fito, ya mata alama data matso nan ta matsa bayansa kadan ya tada sallah sukai, sai daya mata dori sannan suka kwanta, bacci ne ya kwashesu tana kwance akan jikinsa......... ************ Ummy ce ta kalli agoggo karfe 11? Lafiya? Gashi sai ita kadai, yau juma'a Ameera na skul, Sageer da Abba sun fita tare, tana san ta dubasu amma tana ganin rashin dacewar hakan, a zaune take tsuru ta zubama sama ido tana addu'a akan Allah yasa lafiya, taji wayarta na kara. Jawota tai tare da dagawa tace "Aunty Nana in kwana?" "Wato tunda Ameera ta dawo bakida niyyar kira ko?" Ummy tace "kiyi hakuri wlh inata san kira abubuwane duk suka chabe min." "Hmm akwai abinda zai chabe miki banda damuwar yaran can, gaba daya komai na rayuwarki kin dorashi akansa, sam bama kya damuwa da wanda ya dace ki damu dashi." Tace "zaki fara ko? Wai meyasa kike haka ne? Da Sageer da Hassan ai duk 'ya'yanane kuma 'ya'yanki me yasa kike haka ne?" Aunty Nana tace " hmm haka zaki bar Sageer din ba aure?" "Wai yaushe ma Sageer ya girma ne? Duka duka yaushe ya gama service? A bari ya zauna mana?" Aunty Nana cikin dan zafi tace "sai ki bari inya taufa sai kimai....." "Allah ya baki hakuri, ni narasa me yasa kike haka wlh." Aunty Nana tai karamin tsaki, Ummy tace " Ina Hajiya Aina'u ta gujemu." "Aina'u nanan, dazun nan ma taje skul dubo result." Ummy tace "to Allah ya taimak ya kuma bada sa'a." Tace "Ameen." Sun danyi hira kadan kafin suyi sallama. ********* A sama kuwa sai karfe 11 da rabi Jalila ta bude ido, tsananin mamaki yasa ta kara murza idanunta tare da kallan agoggo. Inda Hassan ke kwance ta kalla, a zaune ta ganshi rike da littafi, cikin mamaki tace "yaya ya zaka barni nai ta bacci haka?" Kallanta yai tare da ajiye littafin kan cinyarsa yace " ban fahimta ba? Baccin ne bakyasan na barki kiyi?" Ta kalli agoggo sannan ta kara kallanshi tace "Yanzu me zancema Ummy? Kalli fa agoggo?" Agoggon ya kalla sannan yace "dan kin kai
🏠