NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 128 of 172

re dacewa “ Kasan dazu harda hawaye na? Amma kana zuwa falon naji sun dauke.” Kallanta ya sakeyi fuskarsa a hade yace “ ina tambayarki abu daban kina ban wata amsar.” Tace “Yaya, me yasa inkaga ana wulakantani baka iyayin shirun? Ko wanene kuwa?” Kallanta yai kamar zaiyi magana sai ya saketa, juyawa yai zai fita ma daga dakin. Da sauri ta riko hannunsa daya saketa dashi, tsayawa yai sai dai bai juyoba tace “Yaya.” Juyowa yai yanzu ya kalleta idanunsa sunyi jaa, Jalila ya zanyi da kaunarki? Menene tsakaninki da Sageer? Kallansa tai tace “me kake tunani?” Kallanta yai sannan ya girgiza kansa alamar a’a, zame hannunsa yai ya juya ciki me makon ya fita, jitai yace “yau munje masallaci da Abba.” Cikin tsananin zumudi ta matso kusa dashi, shi kuma baisani ba ya juyo tare da takowa, bugar kirjinsa tai tsayawa sukai a haka, a hankali ta dago ta kalleshi, idanunta sun canza. Shima kallanta yai cikin wani yanayi, murmushi ta sakar mai sannan tace “dan Allah? Tayaya?” Idanu kawai ya kura mata kafin yace “tare da Abba da Sageer.” Cikin jin dadi batasan sanda tasa hannu ta zagayo dashi ta cikinsa ba ta rungumeshi, tace “naji dadi yaya Alhamdulila.” Wani abu ne ya shiga ratsashi kafin yace “Jalilah?” Yanda ya kira sunan nata ne yasa gabanta faduwa. yace “menene ya faru tsakaninki da Sageer a baya?” Gabanta ne ya fadi da sauri ta sakeshi tare da kallansa, zuciyarta na bugawa da sauri da sauri. Tace “naam?” Kallanta yai yana shirin yin magana........... Www— #OneLuv💕 [12/7, 10:12 PM] El-hajj: *_🗯JALILAH!!🗯_* Written By : *AYUSHER MUHD* ✔ote me on wattpad : *Ayusher Mohd* *HASKE WRITERS ASSOCIATION* (_D home of expert and perfect writer's_💡) _Ga taku na musamman 'yan JALILAH NOVEL, D QUEEN BEE & AYUSHER FANS CLUB._ _Wannan shafin sadaukarwace gareku gaba daya, ina godiya sosai da kauna💕OneLuv_ *61* Kallansa tai cikin tsananin tsoro idanunta suka firfito cikin tsananin mamaki, daurewa tai tace "Yaya......." Kallanta yai bakinsa na san magana amma ya kasa, idanu kawai ya kura mata, sai dai shikam a gunsa yaga rashin gaskiya karara a bayanne a fuskarta, murmushi yai wanda gaba daya inka shakeshi bazai ce ya iya irinshi ba, sannan bazaice ma yasan manufarsa ba. Juyawa yai kawai ya koma hanyar waje, Jalila kam gaba daya ta kasa furta komai, saboda tambayar tazo mata a ba zata, sannan bata taba tunanin zai mata irinta ba. Kallan kofar tai wacce ya rufota, saukowa kasa yai Ummy na kokarin yimai magana taga ya fita da sauri, ina zaije da magrib din nan? Jalila kam tafi minti goma sha biyar a tsaye ta kasa motsawa daga gun, kafin haushin kanta ya kamata. Me yasa batace mai komai ba? To me zatace? Da munyi soyayya amma aka kwaceni daga gunshi akamin auran dole? To me zata ce? Hanyar kofa ta nufa da sauri ta fito daga dakin, saukowa kasa tai da sauri, sai dai baya kasa. Fitowa waje tai nan ma bataga motarsa ba, jiki a sanyaye ta kalli inda yake ajiye mota, sannan ta juyo ciki. Ameera ce wace ke rike da cup da spoon tana juya cornflakes din data hado ta kalleta tace "Matar Yaya daga ina?" Jalila ta kalleta tare da yimata yake kawai ta nemi hanyar sama, Ummy ce tace "Jalila?" Juyowa tai ta kalli Ummy wace itama take fitowa daga kitchen tace "ashe Mahaifinki ya tafi?ai bansani ba." Jalila tace "nima bansan ya tafiba Ummy." Kallan mamaki ta mata "wani abun ya faru ne? Naga Hassan ma ya fita." Jalila tace "bakomai Ummy." Ummy ta kalli Ameera tace "in zakici abu ki zauna banasan cin abincin nan naki a tsaye." Ameera ta koma ta zauna, Jalila kuwa tahau sama. Ummy ta bita da kallo tare da fatan Allah yasa ba wani abun bane. Jalila kuwa tana komawa ta zauna a falo tana jiransa, ganin ta kasa zaman yasa ta dauko wayarta ta sauko da sauri, dakin Ameera ta shiga. Ameera wacce shigowarta kenan tana kokarin yin alwala ta kalleta tace "Yaya Jalila lafiya?" Jalila ta matso ta dau wayar Ameera ta mika mata, Ameera cikin mamaki take kallanta, Jalila tace dan kira Yayanki. Cikin mamaki Ameera tace "ni? In kirashi ince mai me?" Jalila tace "ki dai ki kirashi." Ameera ta amsa tana cewa "yaji yayi ne?" Jalila tace "abinda yafi yaji ne. Tunda kin taba gani namiji da gidansa yayi yaji." Ameera tai dariya tana dialing tace "kece dai baki taba gani ba amma yanzu maza ma yi suke." Jalila ta harareta tace "wallahi Ameera nikam kina ban mamaki, bansan a ina kika san komai haka ba, yarinya kafin ki tafasa kina neman konewa." Ameera tai dariya tace "nasan komai wlh, pratical ne......." Jin alamun kamar an dauka yasa tai gum tare da cewa "hello!" Ta fada tana kallan Jalila. Jin ba magana yasa ta kalleta, sannan ta kalli wayar. Cikin mamaki tace "banaji." Jalila tai shiru kafin ta amshi wayar tasa a kunnenta, tace "Hello!" Tana magana aka kashe wayar, kallan Ameera tai ta amshi wayar
🏠