NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 122 of 172

e?" Kansa ya jinjinama Sageer din. Gaba d'ayansu farincikin ya bayyana a fuskokinsu, Ummy harta kasa boyewa ta furta " Alhamdulillahi ala kulli halin". Abba ma abinda yafad'a a zuciyarsa kenan. Sageer kam harda d'an rungume Hassan saboda jin dad'i, Ummy tace "inama Auta tana gida yau taga abinda take buri a rayuwa?" Jalila ai murmushi tace "Ameera yar makaranta." Hassan ya juya yana kallon Jalilah da itama jin dad'in yasakata taketa murmushi, ganin yanda dukkansu suke farinciki, sai itama takema nata dangin irin wannan fatan wataran. Kamar zaiyi magana saikuma yayi shiru. Abba ne yalura da hakan, yace "Jalila taho mana ki zauna." A kunyace ta matso zata ja kujerar kusa da Ummy, Ummy tace "Malama Jalila zauna kusa da mijinki, nima bakiga a kusa da nawa nake ba?" Da saurin tai kasa da kanta saboda kunya, Ummy ta kalli Sageer tace "wanda yasan gauro ne sai yai sauri ya kawo tashi matar." Sageer ya kalleta sannan ya kalli Abba cikin shagwaba yace "Abba kaji Ummy ko?" Abba yace "gaskiya kar a sake cema d'ana gauro inba haka ba kuma yanzu nai zuciya namai aure." Kallansa Sageer yai yace "aure?" Ya matsa daga gun Abba da sauri. Tuntsirewa da dariya sukai yanda ya matsa din, Hassan ya kalleshi cikin wani yanayi da shikansa baisan wani iri bane. Yaukam cikin far in ciki sukayi break d'in nan, dukda Hassan baya magana, kuma koda komai yafito fili dama har yanzu bawai yana yawan magana baneba, baikuma saki jiki dasuba gaba daya, amma abinda yazama dole yayi magana akansa yanayi. Bayan sun gama Abbah yafita aiki cikin tsantsar farim ciki. Suko duk a falo suka zauna suna hira, harda Hassan, dukda shikam ko k'ala bai ceba a zaman nashi, amma yana saurarensu, gaba daya hankalinsa nakan abinda yaji, kodai zuciyarsa ce take kara mai? Kodai ba wani abu tsakaninsu? Kallansu yai yana nazarin su, soyake yagano abinda ke faruwa? suna son juna har zuwa yanzu kokuwa? Su kuwa basusan dawan garinba, damage itama jalilan bawani baki take sakawa a hirarba, k'arfin hirar Sageer da Ummy ne, dan Sageer ya iya barkwanci, sai dai daga anyi abin dariya zata sa dariya. Wajen karfe 12 Hassan ya mike ya hau sama, Ummy ta bishi da kalli cikin jin dadi. Jalila ma bata dadeba ta mike tahau sama, a kwance taga shi kamar mai bacci. Toilet ta shiga ta fito sannan ta kara kallansa, kamar bacci yake kamar kuma ba bacci yake ba, kamar tai magana sai kuma ta jona wayarta a charge kawai ta fito. Sunkai tsawon lokaci suna hirar, har karfe biyu tai Ameera ta shigo. Tana shigowa ta baje a falo wai ta gaji, Ummy tace tashi malama ki wuce kitchen. har agogo yanuna 2, Ummy tace, "Ameera tashi kishiga kitchen, yau kece zakiyi abincin rana, kullum sai dai kici ki kwanta." ''Wayyo Ummy, nikad'ai zanyi?yanzu fa na dawo daga makaranta." Ummy tace "to kedawa zakiyi? Tunma kafin rana tamiki kitashi kije ki d'ora, dan abbanku da wuri zai dawo yau, inya dawo baki gama ba kinga sai ki bashi amsa." Ameera ta shagwabe tare da kwanciya akan kujera tace "Ummy wlh....." Kallan da Ummy ta mata ne yasa tai shiru ta mike tsaye kamar zatai kuka. "Karki damu, tashi muje natayaki kinji Ameera". Jalilah tayi maganar tana dafa hannun Ameera. Cikin murna tace "yauwa matar yayana" Hararta Ummy tayi "Jalila kiyi zamanki, taje tayi ita kad'ai, zauna ki huta". Jalila tace "Ummy bangajiba aii, bara na tayata yanzun nan sai kiga mun gama." Bata bari Ummy tasake maganaba taja hannun Ameera suka tafi kitchen da sauri. Ummy tabisu da kallon sha'awa da tsantsar k'auna. ******** Tunda Abba yafito daga gida Zaliha kebin motarsa abaya abin da zai baka mamaki a ina tasan gidansa?tun jiya da yamma tashigo garin, a hotel ta kwana, yau kam da farar safiya tazo unguwar tasu take jiransa, guri tasamu tayi parking tana dakon fitowar Abba daga gida. tana hango an bud'e gate tafara addu'ar ALLAH yasa shine, ganinsa kuwa tasaki wata ajiyar zuciyar dan dad'i, haka taita binsu abaya har zuwa office. Yana zama a kujera yayinda Secretary d'insa kemasa bayani akan wasu bak'i, dakuma wasu abubuwan da suka faru a jiya sukaji ana knocking d'in k'ofar. Atare suka kalli k'ofar Abba yace, "munada bak'ine?". Yace "a'a gaskiya Alhaji, amma bansaniba ko shigowarmu nan suka zo" "OK, jeka gani to". Yana bud'e mata, batajira komaiba taturo kai cikin office d'in tana yauk'i, sanye take cikin wani shegen leshi, daya gama had'uwa, ga d'inkin yayi mata k'yau sosai tamkar zata fashe saboda matsetan dayayi, takawo siririn gyale ta d'ora a kafad'a, bak'amar fad'uwar gaba Abbah yajiba azuciyarsa, saida ya had'a da addu'ar " Hasbinallahu wa ni'imal wakil". Ganin haka Secretary din yafita, dan hannu zaliha tad'aga masa alamar yafita. Yanda kasan gunki haka Abba ke zaune yana bin Zaliha da kallo, harta k'araso inda yake. Mai makon ta zauna akan kujerar dake gaban desks din, saita zauna a saman desk d'in kawai tana juya idanu "haba myT! babu fad'a miya kawo gaba kuma?". Yanda tayi maganar cikin mat
🏠