NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 121 of 172

inkasa sakin jiki dani a gidanan, bansan ko har yanzu kina fushi daniba, ni kanin Yaya ne haka kawai zakisa a ranki kinga........." 'Dagowa tai ta kallonshi, wannan yasakashi yin shiru batareda ya k'arasa maganar bakinsaba, ta gyara tsayuwarta tana kallonsa sosai, idonta ya fara tara hawaye tace "Yaya sageer nafad'a maka tuni komai ya wuce agareni, kuma zuwa yanzu na fahimceka, bani yakamata ka godemawaba, kaine ka cancanci a godema, domin ka sadaukar da farincikin ka saboda d'an uwanka, samun irinka a wannan rayuwar sai an tona, kazama mai rama alkairi da halacci, ta share kwallar data zubo mata akan kumatunta sannan tacigaba "Ya Sageer ka cancanci kowanne irin godiya, amma kayi hak'uri da rashin sakin jikina agareka, nasan ahankali komai zai zama labari insha Allah, kaima Allah na tabbatar bai manta dakai ba zai baka mace tagari wacce tafini komai sannan mai sanka da k'aunarka". Kallanta yai tare da sakin murmushi wanda har hakoransa suka fito yace "nagode Jalilah, sannan dan Allah ina rok'on wata alfarma agareki". Kallansa ta sakeyi tace "ina jinka, Allah yasa bai fi karfina ba." Sageer ya kalleta yace "Jalilah inason koda wasa kar dan Allah kar wanda yasan wata alak'a tataba shiga tsakaninmu, sannan dan Allah ki kuma nika kulawar dakikema Yaya akan tada, kullum burina yadawo normal mutum kamar kowa, inga yana farinciki, yana shiga jama'a, yana mu'amullah acikin mutane kamar kowa." Kanta ta gyad'a a kunyace, tace "Allah ya bani iko Ya Sageer, zanyi iya k'ok'arina kai ma sai kai naka, har cikin rains ina tsananin tausayin halin da Yaya yake ciki nima, dan babu abinda yakai k'untatar zuciya a rayuwa, mutum bacin ran yini d'aya yashiga ya yake tsintar kansa, bare tsawon shekaru irin haka" "Gaskiyane, mucigaba damasa addu'a, inaji ajikina zaki sauya komai insha Allah, nima kicigaba damin addu'a Allah yabani wadda zata tallafeni irin haka." Tausayi yabama Jalila, dan haka takuma k'asa dakanta, karka damu Ya Sageer dan Allah kaima ka dawo yanda kake da mai walwala, dan Ummy ta bani labarin bahaka kakeba abaya, duk da bazata nunama ba na tabbatar abin na damunta." Murmushi yai yana k'ok'arin barin wajen, "karki damu, zan canja insha Allahu." "ALLAH yasa" itama tafad'a tana fara tafiya domin duba Hassan. Da sauri Hassan yakoma baya dan karta hangoshi, tun farkon maganar tasu yana tsaye, amma basu ganshiba, saboda sun juya masa baya, yaje yana kokarin shiga falon yaji suna zancenshi, fuskarsa dauke da murmushi ya tsaya a bayan bango yana jikinsu, a hankali kunnensa ya dinga juyo mai hirarsu. Yana zaune bakin gado Jalilah tashigo cikin d'akin da sallama. Bai kalletaba amma ya amsa, da 'yar fara'arta takaraso inda yake tace "Laa Yaya ashe katashi? nifa wai hawowa nai na tasheka." "Na tashi!" Haka kawai yace ba tare da ya kalleta ba, kallon data masane yagane shima maganar tasa tafita da tsauri, amma saiya dake. Jalilah batayi zuciya ba tace "Yaya mai zai hana yau kazo kaci abinci tareda Ummy da Abbah, kodan kakuma saka zukatansu cikin nutsuwa?" Yanzu kam bashida zabi. daya wuce kallonta da kyau, yarasa wane irin mahaukacin so zuciyarsa takema Jalilah, baikamata yaji zafin maganganunsu da Sageer ba, musamman idan yai dubi da sadaukarwar dasukayi suduka agareshi, yadad'e yana mamakin yanda kokad'an Jalila bata sakewa da sageer dan Sageer mutum ne mai faran faran yasan sageer da saurin sabo da yawan barkwanci. Ashe akwai abinda ke tsakaninsu, ya akayi haka ta faru? tayaya iyayensa suka aura masa budurwar k'aninsa? shin basu sani bane? Da wani ido zai kalli Sageer? Ace shi da yake babba bai barma kaninsa abu na sai shine kanin nasa zai barmai? kai amma yasan babu yanda za'ayi Abbah ya aura masa wadda yasan Sageer na nema amatsayin matar aure kuma, to meke faruwa.......?" Girgiza hannunsa da jalilah tayine yakatse masa tunanin nashi. Tace "Yaya lafiya kuwa?" Baice komaiba, amma yamik'e tsaye, gani tai yanufi hanyar fita, sai da ya bud'e k'ofar sannan yajuyo ya kalleta yace "kona koma na zauna ne?" Da Sauri tamik'e tana murmushi tace "a'a Yayah ina fa." Karasowa tai kusa dashi a hankali tace "Nagode." "Da akayi me fa?" Yai maganar yana karasa fita daga dakin. Ta biyoshi tace "daka amince." "Hmm" kawai yace, yacigaba da tafiyarsa. Suna sakkowa kuwa saiga Abba da Ummy suma sun fito. Hassan ya karasa kusa dasu ya gaishesu, duk cikin fara'a suka amsa masa, Sageer ma dake zaune a falo yataso, gaishe da su Abba yafarayi, kafin ya gaida Hassan shima. Cikin danne abinda ya tokare mak'oshinsa ya amsa, harda mik'ama Sageer d'in hannu tareda daga kafadarsa, a tare suka mike suka nufi cikin falon. Ummy da Abba suka bisy da kalli cikin jin dadi, haka suka k'arasa kan dining suka zauna, Jalila ta shiga ajiye musu plate, kowa ka kalla fuskarsa a sake take. Abba da Ummy kuwa cikin mamaki suke da kallon Hassan daya ja kujerar dining ya zauna, alamar yau taredasu zaiyi breakfast. Cikeda jin dad'i Sageer yace "Yaya yau zakaci abinci damun
🏠