ji daga bakina?"
Hassan ya kalleshi yace "Abba!"
Yanda ya kira sunansa sai da Ummy ta juya kai saboda kwalla, Abba ya sa hannunsa akan kafadarsa yace "kasan me yafi damuna akan abinda ya faru?"
Hassan ya kalleshi, Abba yace "gani nake duk nine mai laifi ba kai ba, alamace ta ban nuna ma kulawa ba, ban nunama duk kaddarar data samemu mu dogara da Allah ba, sannan ban nunama duk wani abu daya faru ka sanar dani ba, ban nunama ko me ya faru bazai zama laifine ba."
Hassan kallansa kawai yakeyi kafin ya juya kansa gefe, tare da runtse idanunsa, Abba yace " baka taba tunanin ko baka fita waje ba su sai sun fita kuma sai ajalinsu ya kama a gun? Hassan ina karatunka? Har ka bari zuciyarka ta damaimaiye da zargi? Ta hanaka walwala? Ta hanaka sukuni? Ta maidakai gaba daya wani mutum wanda baza'ai magana dashi ba? Ta maida ma baccinka nightmare?"
Hassan ya kalleshi yace "Abba ni na jaa su....."
Abba ma idanunsa ma gaba daya sun canza kala ya sa hannu ya jawoshi ya rungumeshi yace "Ko kaine hakan ta faru dakai, ace misali dukanku ne ajalin ya kama akanku alokacin, ace bare ne wanda yasaku kuka hau titin, bazanso ya zargi kansa ba har tsawan wannan lokacin bare kai dana, Hassan babban abinda yafi damuna shekarun daka diba kana zargin kanka."
Sageer ya riko hannun Hassan rungume juna sukai a tare suka saki kuka, Abba ya kallesu sannan ya kalli Ummy.
Murmushi tamai tare da jinjina kanta alamar hakan yayi.
Jalila kam na kwance a cinyarta tana share kwalla, a yaushe Hassan ya zama haka a rayuwarta????
**********
"Wai zaliha wacce irin rayuwa kika saka kankine? nifa nace ki kwantar da hankalinki, sai Taura yadawo hannunki, kima bar damuwa darashin d'aga wayarki dayakeyi. nifa nama fara zargin kodai wayar tasace tafad'i? Dan nasan aikinmu ba k'aramin aiki bane dazai bar jikinsa dawuri haka""To amma Anty idan kince wayarsa fad'uwa tayi miyasa har yanzu bai sake zuwaba? tunfa daga d'aga wayar wannan d'annan nasa shikenan ba labarinsa, Dan ALLAH kibarni naje gidan nasa kamar yanda nafad'a miki tun farko"
"amma dai Zaliha bakida hankali ko? shin kin manta sharad'in aikin nan ne? Sannan da kankifa kika sanarmin bak'ak'en maganganun da d'ansa yamiki awaya, ko an fad'a miki Na daina sonkine dazan bari a illata minke abanza? kodai sake shawara amma ba wannanba".
"To Anty yazanyi?"
Lakwai abinda zamuyi kuwa, kibani nanda kwana uku, zanyi tunanin mafita"
"Shikenan Antyna, shiyyasa nake matuk'ar k'aunarki wlhy" ta kwanta akan cinyarta.
Murmushi Anty tayi, batace komaiba ta shafa kanta, Dan halinsu d'aya babu wani banbanci.
***********
Tun bayan fitarsu Abba Jalila ta duk'ar dakai tana murmushin jin dad'in kalaman Abba, ga fuskar Yaya tanuna shima yasamu nutsuwa yanzun.
Kad'an tad'ago idonta tasaci kallonsa, saitaga Ashe shima d'in ita yake kallo, murmushi takumayi tareda kauda kanta gefe.
Muryarsa can k'asa yace taji yace "Jalilah!"
Kasa d'agowa tayi ta kalleshi, amma ta amsa da "na'am".
Shirune yaratsa d'akin Jalilah tana wasa da yatsun hannunta, shikam Hassan idonsa k'yam akanta, ko k'yaftawa bayayi, jinsa yake tamkar wani sabon mutum, bayanin Abba yasaka zuciyarsa ta k'ara bud'ewa, dan Abba ya dade da shi bayan su Ummy sun fita yana kara nusar dashi da nunamai ba laifinsa bane, zuciyarsa ta kuma rage nauyi sosai, wata nutsuwa ta musamman ke ratsa dukkan sassan jikinsa, harma yana tuhumar kansa miyasa bai fad'ama su Abba gaskiya ba a duk tsawon shekarunan? miyasa yasaka ummynsa mai sonsa da da k'aunarsa aciki k'uncin damuwa har wannan shekarun, tabbas ya yarda *JALILAH!* alkairice a rayuwarsa, Dan itace ta bashi k'arfin gwiwar canja komai, yafirzo k'aramar iska daga hancinsa...
Jin yayi shiru sai Jalilah takuma d'ago idonta, karaf suka kalli juna itadashi, tafin hannunta tasa tarufe fusakar tana k'aramar dariya.
Shikuma ya lumshe idanunsa yana gyara zama.
Tashi tayi zata barmasa d'akin yai saurin rik'o hannunta dukda jikinsa babu k'arfi sosai.
Gabamta yad'an fad'i tana jira taji ya janyota amma sai taji shiru.
"Dawo ki zauna to, magana zamuyi".
Rintse ido tayi, kusan 1minute sannan tadawo ta zauna, shima zamansa yagyara sosai yadawo kusada ita....
Jalilah!
Kallansa tai yanda yake kallanta yasa tai saurin sauke idanunta, gani tai kawai ya koma ya kwanta akan cinyarta, ya juyo da fuskarta saitinta.
Kallansa tai tare da zaro ido, yace " dazu ba haka kika min ba? Na tabbatar dana bude idona a haka na gani." Ya fada tare da sa hannunta akansa.
Kallansa tai tare dayin murmushi tace "tunda ka gani menene na sake gwadawa?"
Yace "abinda kika fada nakesan ki maimaita."
Ta dan juya kai tace "ni namanta ma me nace."
Murmushi taga yayi, ta zubamai ido batasan a fili ta fada ba sai jitai yace " haba? Kinasan kiga ina murmushi?"
Da sauri ta kalleshi ashe datace murmushi na masa kyau a fili ta fada.
Kallanta yai yace "badai kina kara sona bane inkika ga ina murmushi?"
Da sauri ta kalleshi tace "naam?"
Yace "me? Bakya sona?"
Bakinta na rawa tace "ni bance ba."
Ya kara gyara kwanciyarsa yace "basai kin fada ba k