NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 118 of 172

omy yad'an fad'i, ita kanta tarasa gane dalilin Inna nason Abakar sai yaje gidan Taura, duk da dai tamata bayani a dunk'ule, amma anya babu wata kullalliya a zuciyar Inna kuwa? Itakam sam Inna inta fadi abu akan Abakar hankalinta baya kwanciya, tasan Inna sarai hankalinta nakan company dinta. "Ya akai? Naga kinyi shiru? "Uhm ba shiru nayiba, amma nima ina ganin zuwan naka yanada muhimmanci, musamman idan kahad'a bayanan dana maka guri guda, akan abinda aka mana agidan, kuma nasan duk akan komawar Gwaggon tane, a ganina kawai kace kanason gwaggo tadawo nan gidan dazama kawai, ni wlhy nama amince tadawo d'akin Safeenah yanzun, kaga sai a gyara kafin ta iso, idan kuma za a canja mata kayan d'akinme to, duk fa wannan takamar da mukeyi dan munada company namu na kanmu mukeyi ni sam idanun mijin Jalila yanda yake kallanmu hankalina bai kwanta dashi ba, na tabbatar Innama hakan ne yasata fadar cewa kaje din, ai daga Jalila har Goggon naka ne." Zuwa yanzun kam zuciyarsa tagama yarda akwai wata akasa, wato sai yanzu akasan da Jalila tasa ce? Yace, "ita inna tayarda da hakan?" Yai maganar cikin zargi. Da sauri tace "sosaima, itamace tabada shawarar hakan, aganina tahanyar goge laifinmu ne kawai zai hana Taura karbe kud'insa koda kuwa dansa yaso yin hakan, dan wannan dan nasa ni yafi bani tsoro, dafa zai tambayi kana ina cewa yayi wai Inashi mutumin?" Dady ya cije lebansa, daya tuna ma rainin hankalin da Hassan yamasa randa sukaje asibiti, wai ka fito da kudi kuwa? Ya tuna sanda ya miko mai 1000, kamar shi?? Momy takatse tunaninsa da fad'in "kagani zuwan naka yanada muhimmanci kaji Darling? koba komai zaka lallaba Jalilah, ai komin lalacewa naka naka ne, mu fa kosamun damar kebancewa da ita bamuyiba." Dady yai shiru kafin can yace "Shikenan, babu damuwa, zanje din, amma kafin natafi zan shiga wajen Inna inji miya kamata nafad'ama Jalilah idan naje, kinsan yarinyar tana jarabar son uwarta, sam bata damu da ni dana haifeta ba. Mumy ta kalleshi, jawota yai jikinsa ya rungume ta a ransa yace wato yanzu dalilin 'yata shine na samu 'yancin roko? Da ai komai sai dai a yanke min hukunci, danasan mijinta kafin aurenn lalai dana dade da canza shika....... ********* Alhmdllh komai ya dai-daita, Hassan yadawo dai-dai, amma kallo d'aya zaka masa kahango idanunsa da sukai ciki, har wata yar karamar rama yayi. Tun d'azun idonsa nakan Abba, kallonsa yakeyi ko kiftawa bayayi. ita kanta Ummy ganin kallon da Hassan kema Abban nasu yasata maida kallonta kansa, tasan soyake yace wani Abu, amma Abba sam bashida alama. Hannun Abba Hassan yakamo, yarik'e sosai acikin nasa, wannan yasaka Abba maido gaba d'aya hankalinsa kan Hassan, ya zubamai ido cikin wani yanayi da shikadai ya san me yake nufi. Wasu hawaye masu matuk'ar zafi suka ziraro daga gefen idonunsa. "Abba nasan ban cancanci a yafe min ba, ni kaina nakasa yafema kaina wannan laifin, nasha addu'a inama tun sanda nayi jinya nima nabi bayan su Husain, na roki Allah akan inhar mutuwata shine mafi alkairi ya daukeni, sai dai da alama ba yanzu ba......" Ya kara kallan Abba da idanunsa da suka canza yace "Abba kamin dukkan hukuncin dakaga yadace dani kaida Ummy, duk hukuncin da kukamin bazan taba ganin tsaurinsa ba, Ummy! Abba dan ALLAH Ku hukuntani ko nima zuciyata xata samu sukuni. Kasa karasawa yai saboda gaba daya zuciyarsa ta yi rauni, hannu yakai yarik'e wuyansa yana k'ok'arin janyo numfashi. Lokaci d'aya Abba da Ummy sukai kansa, Jalilah kam fita tayi daga d'akin tana kuka, shi kansa sageer yakasa jarumta dan tuni shima kwalla tacika masa idonsa har suna neman zubowa.Addu'oi Ummy da Abba kemasa, ahankali numfashin yafara dai-daita, Sageer yamik'o gorar ruwan daya d'akko, Abba ya taimakama Hassan yatashi zaune ya jingina da fuskar gadon, bayan yasaka masa fillo. Ummy tabashi ruwan yasha sosai, kafin ya janye bakinsa. Idonsa yayi jajur, kalle-kalle yafara yanason ganin Jalilah amma bata d'akin. Ummy Ce talura da hakan, ta juyo tana fad'in "Sageer! Jalilah fa?". Shima waige-waige yafara, kafin yace, "inagafa tafita". Abba yace, "Sageer jeka kirata". Yace "To Abba" Afalo ya isketa tacusa kanta a cinya tana rusar kuka, tausayi tabashi ya kura mata ido, murya a sanyaye yace "Jalila" Shiru kamar bata jishiba. Ya sake cewa "Jalilah!" Batare data kalleshiba tace "Naam." Cikin muryar kuka ta amsa. "Kizo inji Ummy." Abinda yafad'a kenan yajuya yakoma cikin d'akin. saida ta goge hawayenta sannan tamik'e tabi bayansa. Tunda tashigo Hassan ya kura mata ido, a hankali ya lumshe idanunsa, garin yaya ya bari yarinyarnan ta gama kama zuciyarsa? Ummy tajawo hannunta ta zaunar kusada ita tana lallashi. Bayan wasu 'yan mintuna Abba yai gyaran murya, har yanzu hannunsa nacikin naHassan. Cikin kakkausar murya yace "Hassan!" Abba yakira sunansa cikin muryar damuwa. Kallonsa kawai Hassan yayi amma bai amsaba. Abba ya kalli Sageer yace "Sageer zauna anan." Gefensa kadan ya nunamai, Sageer ya zauna kusa dashi. Abba ya kalli Hassan yace " me kake san ji Hassan? Me kakeso ka
🏠