ย  ย  NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 117 of 172

kallo, ya d'an saki guntun murmushi, sai kuma ya lumshe idanunsa, ahankali ya furta " kin cancanta jalilah ". Ni kam danake labe nad'an dara kad'an.๐Ÿ˜… ************* Har washe gari Abbah baice komai gameda zancen da Hassan yay masaba, wannan ne yakuma saka Hassan cikin matuk'ar damuwa, amma kasancewar Jalila a gefensa zuciyarsa tana d'an rage nauyi. Ita kanta Ummy shirun na Abba ya dameta, duk da bai canza fuska ba, amma yanda ya share maganar sai lamarin yake nuk'urk'usarta. Sageer ma daya kasa daurewa sai da ya tambayeta mi Abban yace gameda maganar jiya. "Sageer baice komai ba fa, nikaina abin ya dameni, gashi bansan wane hali Hassan yake cikiba, naga har yanzu matarsa bata fitoba". Ya sageer ya ja ajiyar zuciya, sai kuma yace "insha ALLAHU babu abinda yafaru Ummy, bara muga zuwa 9 idan bata sakkoba sai a bincika" Ta kalli Sageer cikin jin dadi tace to Sageer. Ummy batace komai ba tacigaba da aikinta, amma zuciyarta sai sak'e-sak'e take mata akan Hassan da kuma shirun Abbah. tare sukayi komai da Sageer. ************* Safeena ta kalli RAM tace "ina ne nan din?" Yace shiga ki gani, tura kofar tai, yan mata ne da maza kowa yasha kaya na duniyanci suna ta cashewa. Da sauri ta kalleshi tace "menene hakan?" Yace "baki gane ba? Wannan shine rayuwa ai." Ta kallesu sannan ta kalleshi da sauri ta juya da gudu tana girgiza kai, yanda taga mata na rungume maza ba kunya? Ina zata iya shiga tai abin nan? Daki ta shiga ta fada kan gado tana kuka da kiran sunan Inna da Mumy da Dady.......... Nace hmmmmm [12/7, 10:10 PM] El-hajj: *_๐Ÿ—ฏJALILAH!!๐Ÿ—ฏ_* Written By : *AYUSHER MUHD* โœ”ote me on wattpad : *Ayusher Mohd* *HASKE WRITERS ASSOCIATION* (_D home of expert and perfect writer's_๐Ÿ’ก) *57* Har 9 tawuce babu jalilah babu labarinta. Su Ummy suka kammala aiki tsaf itada Sageer, ko ya Ummy taji motsi saita waiga, azatonta jalilah ce. Shi kansa Sageer hankalinsa yafara tashi, yana daurewane kawai saboda karya k'ara tada hankalin Ummy. A can kuwa bangaren su jalilah ciwon Hassan ne ya motsa, saboda damuwar daya kwanta dashi a zuciyarsa, akan shiru da Abba yai akan maganar su Husain, gani yake maganar tazama gaskiya shine silar barinsu duniya, shiyyasa Abba yake fushi dashi, dama Jalilah tana fad'an bahaka bane saboda kawai ta kwantar masa da hankali. Cikin dare sau biyu ciwon natashi, shi yasa sam jiya basuyi wani barcin kirkiba, sunayin sallah da asuba kuma suka kuma kwantawa dansu rage barci. Dama Hassan jiya a k'asa ya kwanta, duk yanda Jalilah taso yadawo saman gado bai dawo ba. Bayan sunyi sallar asubahi ma a k'asa ya kwanta akan sallayar dayai sallah, can cikin barci Jalilah tadinga jiyo kakarinsa, a zabure ta mike cikin tsoro ta kalli inda ya kwanta. A razane ta sakko kusa dashi ta tsugunna agabansa, hannuwansa daya rik'e wuyansa itama ta rik'e tana kiran "Yaya! Yaya! Innalillahi please Yaya katashi." Gaba daya ya canza, abin ya tsorata ta, yau kam ciwon yamafi na kullum tsanani, dan jikinsa har rawa yakeyi, kansa tad'aga ta d'ora a cinyarta tana kuka da tofa masa abinda tasani, tun tana d'aukar lamarin k'arami sai taga yawuce tunaninta, da ciwon yayi kamar zai lafa saikuma jikinsa yafara rawa yakuma damk'e wuyansa yana jawo numfashi da k'yar. Tanaso tatshi taje takira su Ummy amma takasa, bazata iya fita tabarshi shi kad'aiba, dabara ce tazo mata data hango wayarta, da k'yar tamik'a hannu ta d'auka, tashiga laluben number Ummy. Jikin Ummy har rawa yakeyi wajen d'aukar wayar. Saboda ganin number Jalilah, Sageer nazaune gefenta, yayinda Abbah ke shirin fitowa daga d'aki. Tana gama jin maganar Jalilah ta jefa wayar a kujera, bata tsaya sauraren tambayar da sageer kemataba, ganin haka shima Sageer yarufa mata baya zuwa sama, dan ya fahimci ba lafiya ba. Gaban Abba ne yafad'i yabi saman da kallo cikin matuk'ar tashin hankali, badai jikin Hassan bane, da sassarfa yabi bayansu shima. Sun tarada Jalila tanata kuka har yanzu, gata rik'eda Hassan tana kiran "Yaya katashi!". Gaba d'ayansu suka rufu akansa kowa yana masa addu'a, Ummy kam tama kasa addu'ar, kuka kawai takeyi, hakama Jalila. Ganin halin da Hassan ke ciki cikin kidima Abba yakira Doctor, a gaggauce yamasa bayani akan halinda Hassan d'in yake aciki, yana kashe wayar ya matso kusa dashi tare da riko hannunsa. Babu dad'ewa saiga Dr, Abba na ganin kiransa ya fito da sauri, lokacin ciwon yafara lafawa, sai numfashi da yake fitarwa sama-sama, har yanzu kuma kansa nakan cinyar Jalilah dake share sauran hawayenta, da taimakon Abba da Sageer suka maidashi kan gado, doctor yafara aikinsa.... *********** Mumy ce ta kalli Dady tace "Dadyn yasmeen kayi shiru? ko kafasa zuwan" Kallonta kawai yakeyi, amma yakasa cewa komai, yarasa miyasa suka damu da zuwansa gidan Taura itada inna, kodai wani k'ullin sukai masa ne? sukeso yaje ya afka. Hannunsa Momy ta kamo ta kwantar da kanta akan kafadarsa, juyowa yai yana kallonta, kafin ya d'an saki iska a bakinsa. "Wai shin menene dalilin da yasa kika damu da zuwana gidan taura ne haka?"Gaban M
๐Ÿ