ย  ย  NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 111 of 172

Written By : *AYUSHER MUHD* โœ”๏ธote me on Wattpad : *Ayusher Mohd* *HASKE WRITER'S ASSOCIATION* (_D home of expert and perfect writer's_๐Ÿ’ก) Trauma is defined by the American Psychological Association (APA) as the emotional response someone has to an extremely negative event. While trauma is a normal reaction to a horrible event, the effects can be so severe that they interfere with an individual's ability to live a normal life. In a case such as this, help may be needed to treat the stress and dysfunction caused by the traumatic event and to restore the individual to a state of emotional well-being. Some common sources of trauma include: Rape Domestic violence Natural disasters Severe illness or injury The death of a loved one Witnessing an act of violence e.t.c. Idan muka duba abinda ke rubuce a sama, zai bamu damar cikaken fahimtar matsalar Hassan, Trauma na ganin mutuwar kaninsa da yake tsananin so sannan da Guilty na laifin da yake tunanin shine sanadiyar yin hakan, kafin na fara rubuta matsalolin Hassan sai danai bincike akan matsalar cutar Trauma wanda ke damunsa, na dauko bayanin sama ne saboda mu fahimci matsalarsa musan me ake nufi da wannan kalma ta Trauma, akwai mutane dayawa dake dauke da wannan matsalar sai dai bama damuwa da abinda ke damunsh saboda rashin sanin matsalarsu, wasu cikin bacci zakaga suna razana, wasu kansu ke daukar zafi, wasu duk sanda sukaga jini, duk wadannan na faruwa ne a yayin da sukai karo da wani mumunan abu wanda ya taba ayuwarsu yakan hanasu yin rayuwa yanda ya kamata. Allah ya mana mai kyau ameen..... *54* A hankali ya dago ya kalleta, itama ta bude idanunta. Kallansa tai sannan tai saurin saukar da idanunta kasa, ta zame daga jikinsa ta koma ta zauna akan kujera, karamin gyaran murya yai na burin kunya yace " zaki shiga ku gaisa da Goggo?" Bata kalleshi ba tace "a'a." Tada mota yai sukai gaba, shiru ne ya ratsa motar ba wanda ya sake magana. Sunyi tafiya sosai, kafin ta daure tace " Yaushe kuma Ya Sageer din ya dawo?" Yace "Sageer? Bayan abin ya faru ne hankalin su Abba ya tashi shine suka nemi alfarma akan a dawo dashi, ko hankalina dana Ummy zai kwanta, dakyar dai suka amince." Ta dan kalleshi tace " Yaya na kasa fahimtar abu daya, me yasa kafi damuwa da Ummy kadai? Dan na kula yanda ka damu da Ummy baka damu da Abba ba." Kallanta yai sannan yace "haka kike gani?" Tace "bani kadai ba hakan ne ma." Shiru yai har kamar bazaiyi magana ba sai yace " Abba a koda yaushe in na ganshi nakanji tsananin tausayinsa, nine sillar rasa dansa da kuma dan kaninsa sai dai yanda yake nunamin so shine ke damuna, i have to be cold to him saboda ya rage damuwa dani, dan ban cancanci kaunar da yakemin ba, inasan ya rage san da yakemin ne saboda ko daga baya inyasan abinda ya faru bazai dameshi ba." Jalila ta kalleshi kawai sai jitai tayi dariya, kallan mamaki ya mata yace "dariyar menene?" Tace "yaya, wallahi rashin sakarma mutane fuska da zama cikin mutane yasa gaba daya tunaninka daban ne, kana tunanin wai abinda kakemai na zafi zafi shine sai sa ya rage sanka? Ko ya rage damuwa dakai?"- Hassan ya kalleta cikin mamaki, tace "ashe ma gwara ni." Fuska ya hade yace "gwara ke me?" Tace shikenan. Shiru yai baice komai ba ta kara cewa "tab lalai yau naji abinda ban taba ji ba." Harararta ta yai yace "zaki cigaba ko?" Ta rufe bakinta tace "bance komai ba." Haka suka isa gida, suna isa suka shiga ciki, Abba na kallansu ta glass din falonsa, murmushi yai na jin dadi tare da godiya ga Allah.Suna shiga daki ta shiga toilet tai wanka saboda fashin sallah da takeyi, sannan ta fito ta dau bargo zata shimfida, kallanta yai yana zaune akan gadon yace "ki dawo nan ki kwanta yau ma a kasa zan kwana." Tace " a'a ka kwanta." Kallanta yai tace "in na kwana yau gobe ma anan zan kwana." Yace "sanda na matsu da gadon sai na tureki na kwanta." Tadan hade rai kadan tace "bari na dau hijabina na tafi gidan Goggo kafin ma a tureni inji ciwo." Murmushi yai yace " wannan dai neman magana kike, matar dana kaiki har kofar gidan kikace bazaki iya rabuwa dani ba?" Baki ta bude cikin mamaki tace "a yaushe akai hakan?" Yace "musawa zakiyi kenan?" Ta matso kan gadon wai ita a dole an ba ta mata rai ta kwanta tare da juya baya tace " wallahi na kula duk abinda banceba sai acemin nace." Kallan bayanta yai ya tuno abinda ya faru a mota, kallanta yai yace "to ko mu sanar da Goggo laifin da mukai?" Juyowa tai ta kalleshi tace "laifin me?" Yace "na fitsarar da mukai......" Da sauri ta mike tasa hannu ta toshemai baki tace "yayah." Kallanta yai sannan ya zare mata hannun data rufemai baki yace "yanzu yanda kika hau kaina me kike nufi?" Da sauri taja baya tace "wai ni yaya....." Yace "wai a yaushe na zama yayanki ne?" Baki ta turo tace "to ni me kakeso nacema?" Yace "oho amma ni bansan yayan nan." Tace " to naji ka daina tsokanata." Fuska ya hade yace "a yaushe na tsokaneki? Bakiyi rashin kunyar bane? Ko yanzu baki hau kaina ba?" Tace "kaine fa ka jawoni kamin kiss sanna
๐Ÿ