i kuwa muje."
Nace ka bari su gama wucewa.
Nan muka tsaya har suka wuce nace to mu tsallaka, Sudais sai tsalle yake wai ya hango Abba, wanda ni a guna mugunta na shirya inata dariyar yarinta.
Kamar zamu tsallaka titin, harna fara tafiya dasu na dawo baya ina dariya, ina cewa ba Abba bane ziraku nayi.
Husain na rike da hannun Sudais ya juyo shima yana dariya yace "amma lalai Hassan, wallahi ni harna yarda
Shikuma Sudais, duk ya damu a karasa karshen titi, Husain ya kamo hannunsa suka juyo da shirin dawowa.
Gaba daya bamuyi auni ba ina kallansa shima yana kallona muna dariya sai gani nai anyi gaba da..........
Numfashinsa ne ya sarke, wasu zafaffan hawaye ne suke zubomai, karar faduwarsu kawai mukaji.
Sam bamu kula da tahowar mota ba, mutanene suka taho gun a rikice, jini....... jini.......
Numfashinsa ne ya shiga fita da sauri da sauri. Kansa na wani irin sarawa, yace " Tsoro da fargabar abinda na gani na fara ja da baya da baya, ina kallan jinin da ke zuba daga kansu.
Inaji mai motar na tambayar waye ya sansu amma bakina ya kasa magana saboda numfashina da yake hawa da sauka, kaina na wani irin juyawa saboda jinin dake kwaranya.......
Kansa ya matse da karfi wanda ke mai wani irin azaba, Jalila kam hawaye duk ya gama jika mata fuska.
Matsowa tai tasa hannunta akan kafadarsa tace "Yaya?"
Hannunta ya dan ture tunda ya fara labarin sai yanzu ya juyo ya kalleta fuskarsa gaba daya ta canza, bata taba ganin Hassan haka ba, yace "Nine sanadiyar rasa rayukansu, wanda haryau kanin Abba Allah bai kara bashi haihuwa ba, wanda ranar sunan Ameera ya zama ranar rasuwar yayana, wanda nai sanadiyar mutuwar daya daga cikin farin ciki Ummy, farincikin mahaifina sannan farinciki na, bancigaba da makaranta ba saboda na dade a asibiti a kwance, sai dana samu sauki ne Abba ya kawo wani gida yana koyamin, a haka da kyar Ummy ta sani nai exam din waec daga nan ban cigaba da komai ba.
Nine sanadi, Taya zan samu farinciki a rayuwata? Taya zanyi murmushi a rayuwata, tunda abin nan ya faru har yau basusan nine sanadi ba, sai dai kowa tausayamun yake akan rashin dan uwa nane yasa ni canzawa haka? Na lalata farincikin kowa na lalata.......:"
Kansa ya kifa akan sityarin mota yanajin wani abu na ratsashi.
Ya dade a haka kafin yace " ki shiga gun mahaifiyarki, bancancanci samunki ba, bancancanci samun farinciki ba."
Shiru tai tana kallansa sai hawaye dake zubo mata wanda kamar korosu akeyi, hannu tasa ta bude kofar motar ta fita.
Idanunsa ya runtse da karfi yasan za'ai hakab sai dai zuciyarshi ce ta sake zafi dayaji ta fita, hakan shine daidai shikuma yanzu rayuwarsa sai tafi tada dan ta riga ta shiga rayuwarsa wanda yanzu ya tabbatar cireta babbar gibe ne a gareshi.
Jiyai ta sake bude motar, dagowa yai ya hade rai sannan ya kalleta.
Yanzu kam gaban mota ta bude gefensa ta bude, kallanta yai sai dai baice komai ba, Jalila ta shiga ta zauna sannan ta rufe motar, kallansa itama tai sannan tace " Inyi magana?"
Kallansa yai kallan mamaki, tace "ka fadi duk abinda ke ranka ni baka barni na fadi nawa ba."
Yace "kamar ya kenan?"
Shiru tai kafin tace " yaya kana tunanin dan Uwanka abinda yakeso kenan?"
Kallan tambaya ya mata, tace "yanzu in yasan saboda shi ka maida rayuwarka haka kana tunani zaiyi alfahari da hakan?"
Idanu ya kura mata, tace "yaya kana yaro lokacin sannan ba da saninka bane......."
Da sauri ya juya kai ya bude kofa yana neman fita, da sauri tasa hannu ta riko hannunsa.
Juyowa yai ya kalleta tace "inhar kanasan in tafi zan tafi, sai dai inhar akan dalilan nan ne hujjajun basu karbu ba."
Kallanta yakeyi, murmushi tamai tace "wace irinn rayuwa kai zuciyarka na dauke da abubuwan nan?....."
Batai auni ba ya jawo hannunta ta fada jikinsa, kankameta yai tsam, yanajin wani abu na ratsashi, duk da gabanta dake faduwa a hankali tace " meyasa kake tunanin su Ummy zasu ga laifinka akan abinda ya faru?"
Idanunsa ya lumshe kawai, bayansa tadan shafa alamar lalashi tace "Yaya kaine abin tausayi ba su Husain ba, su kansu na tabbatar da zasusan abinda ka aikatawa kanka bazasuji dadi ba."
A hankali ya dagota daga jikinsa kallanta yai, ita kanta kallansa takeyi, sai dai ganin kallan da yake mata yasa ta saukar da idanunta kasa, ya rike fuskarta da hannayensa yace "Jalila kinfi kowa sanin halina, inada dizgi? Shariya? Rashin san magana? Rashin iya magana? Rashin iya hulda da mutane? Kin tabbatar zaki iya zama zama dani?"
Shiru tai tana kallansa, sai dai a wannan lokacin ta tabbatar bazata iya bijire masa ba, batada tabbas akan ko tana sanshi sai dai bazata iya musa mai ba, kai ta daga a hankali.
Kansa ya sunkuyo a hankali saitin bakinta, yakai labbansa kan nata.
Labanta ya tsotsa kadan sannan ya dago ya kalleta yace " banasan na zama nine sanadiyar ruguzamiki rayuwa."
Idanunta ta lumshe dan wani abu taji yana ratsata, a hankali ya kara kai bakinsa cikin nata, wani salo yake mata wanda yasa taji gaba daya kanta na juyawa, wani abu na ratsata har cikin kanta.
#OneLuv๐
[12/7, 9:54 PM] El-hajj: ๐ฏ *JALILAH* ๐ฏ