ย  ย  NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 11 of 172

arantarmu." Tace "students ce?" Kai ya daga yana murmushi. Ummy tace "bani labari." Dariya yai sannan ya mike yace "Ummy ba yanzu ba." Tace "bama nasan ji." Nan yai sama yana cewa "zama na musamman zamuyi ai Ummy na." Da kallo ta bishi tana murmushi azuciyarta tace"Allah ya kawo randa zanga Hassan na walwala kamar haka, Allah ya kawo sanda zaimin zancen mace." *********** Inna ta dade tana nazari kafin ta zagaye sunan mutane hudu a cikin dan littafin nata. Nan ta kira Sani wanda ya kasance Secretary dinta ne a lokacin da take ganiyarta, bayan sun gaisa tace "Nikam ya labarin Alh Ayuba?" Yace "Alh Ayuba ai yana England tun shekaru hudu da suka wuce shi da iyalansa." Tai shiru sannan tai cancel din sunan sa tace " Alh Muhammad fa?" Yace "Hajiya kin manta shine na baki labari an rufe company dinsu?" Tace "Oh na manta." Nan tai canceling din sunansa tace "Alh Abdullahi Taura fa?" Sai daya danyi nazari yace " eh shi yana nan garin Kano, sai dai yayi retire daga managern banki ya fada kasuwanci." Tace "kasuwancin kamar ya yake?" Dariya yai yace "Kasuwanci mai karfi, dan yanada company na motoci, yanada gidan mai sannan yanada store a nan garin." Murmushi tai tace "bashida wani issue na matsala ko personal life dinsa?" Sani yadan yi shiru yace "Ba komai a iya sanina na dai san akwai yaransa uku, sai dai akwai kananan maganganu akan babban dansa wanda inaji kamar akwai wata matsala da yake fama dashi, sai dai su suna kokarin boyewa." Ba tare da wani dogon nazari ba tace "yauwa na gode, yanzu ka bincika ka samomin number dinsa, cikin gaggawa." Yace "To Hajiya!" Harzata tambayeshi mutum na karshe da take tunani sai ta fasa dan dama tafisa ran mutane ukun. Mikewa tai ta shiga dan xagaye d'akin nata tana tuanani, tabbas tanajin ba matsala dan kuwa tasan Taura akwai mutunci sai dai tasan harka ta business bani in baka ne." Ta tabbatar in ta nemi taimako dole sai ya nemi wani abu itama daga bangarensu, waya ta daga ta kira Dady tace "Abakar ya situation din directors dinmu?" Yace "Hajiya abin dai ba dadi, duk an rasa mafita" Batace komai ba ta katse wayar, hoton mijinta wanda sukai ita da Mumy da mijinta ta kalla, sannan ta zauna tare da bude littafin da take karantawa, wanda jin matsalar nan ya sa ta ajiye. Su Jalila an shiga tarkon kauna tunda Sagir ya bayyana mata zuciyarsa, yau komai take in ta tuna kalamansa sai dai kaga tana murmushi ita kadai, yau aikin gidan ko wahala bai bata ba dan yau zuciyarta a cikin shauki take. Nace Hmmmmm #Oneluv๐Ÿ’• [08/10, 19:18] โ€ช+234 816 365 0557โ€ฌ: ๐Ÿ—ฏ *JALILAH* ๐Ÿ—ฏ Written By : *AYUSHER MUHD* Wattpad: *AyusherMohd* *HASKE WRITER'S ASSOCIATION* (_D home of expert and perfect writer's_๐Ÿ’ก) *No 6* Kamar hadin baki yau Sagir da Jalila wani irin bacci sukai mai cike da mafarkin junansu, Jalila bayan tayi sallar asuba ta kalli Goggo dake jan carbi sannan ta gaisheta. Goggo ta amsa sannan tace "Jiya na kula a farinciki kike Allah ya kara kawo farinciki mai d'orewa a rayuwarki." Jalila tace "Ameen Goggo." Sannan ta d'ora da cewa "Goggo kidinga min addu'a inkin yi sallah Allah yasa na auri wanda yake sona nima nake sanshi wanda zai kularmin da ke." Goggo ta daga carbi alamar zata zula mata,da sauri ta matsa tana dariya. Goggo tace "wato gaba d'aya yanzu kinci idon akuya ko? Na kula kwanan nan fitsara kike ji sannan aure kikeso." Tace "Goggo daga cewa amin addu'ar miji sai kice aure nake so?" Goggo tace "bazakuwa ki daina cewa Miji ba kuwa ko?" Jalila tace "Goggo kice komai na a rayuwa, ni ba kawa ba in ba a boko ba, ni ba kowa ba, kedin dai kece komai na, kinga kuwa dole komai na nasanar dake." Goggo tadan murmusa sannan tace " kashe fitilar nan ga haske nan ya fara shigowa, kinga kar battery dinmu yai sanyi." Jalila ta kashe sannan ta mike tace "Na tafi bauta." "Bauta? Kai Jalila bakida dama." Har takai kofa ta juyo tace " Allah ya taimakemu an daina bauta amma wasu karfi da yaji nema suke su mai dani baiwa." Ta fada tare da bude kofa, Goggo tai murmushi tare da bin bayanta da kallo, tace "a koda yaushe addu'ar miji na gari zan miki Habiba." Jalila na fita ta zagaya ta baya inda kofar kitchen take dan tanan take shiga wai dan kar ta tashesu daga bacci, kwanukan da akaci abincin dare ta hade guri d'aya sannan ta zauna ta soma fere dankali, tana d'aura mai ta shiga yin wanke wanke, tana zubawa tana gyaran kitchen, tana gamawa tasa tafashen naman kaza sannan ta fito falo ta fara shara, haka ta gama shara tai goge goge, tana gama abinci lokacin suke fitowa daga daki alamar tashi daga bacci, nan ta shiga dakuna ta gyara ta wanke toilet sannan ta fito ta dafa ruwan tea, ta dau bread din da aka ajiye domin su, nan ta fita. Tana zuwa ta fada wanka tana fitowa ta zura kaya sannan ta shafa mai, duk abinda takeyi tanayi tana duba agoggo, tana fitowa falo Goggo ta miko mata tea a kofi tace "zauna." Jalila ta kalli agoggo taga bakwai da ashirin, da s
๐Ÿ