Β  Β  NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 109 of 172

binda ke damunta sunki dan su itace mahaifiyarsu ita kadai suka sani. Ita ma ta nemi a barsu, haka ta sha wahalar wannan lokaci duk ta rame ta fige. Taura tsananin tausayinta yasa ya umarci dauke yaran sai dai kuka tasa ta nemi a barmata wai mijinta ya tafi kar a rabata da 'ya'yanta. Haka ya bar mata su, har Allah ya kawo mata nata haihuwar ta haifi danta namiji aka sa mai Sageer." Ajiyar zuciya yai yace "Kin fahimci labari na kashe na farko?" Jalila wacce idanunta ke zubar da hawaye tace "Kune yaran kanana, sannan wacce ta rikeku wato kanwar mahaifiyarku Ummy ce???" Hassan yace "eh, Ummy ce." Haka muka taso mu uku, sai dai nu biyu mun girmi Sageer da shekara biyu, dangin mahaifinsa suka daukeshi saboda takaicin yanda take kula damu. Haka muna kuka aka tafi dashi, bayan mun dawo gidan mahaifanta ne aka yanke shawarar hada auransu. Da harta ki amincewa sai dai ganin za'a kwacemu yasa ta amince. Tunda take bata taba nuna tanasan akawo mata danta ba, duk kuwa da kowa yasan zuciyar uwa. Haka Abba ya daukemu muka koma Egypt, zamansu zama ne na kara bawai na aurataya ba, har a hankali suka fahimci mahimmancin junansu. Shekararmu takwas a garin muka dawo nigera, na taso da tsananin kaunar Ummy wanda ko hawaye ko damuwa naga tanayi sai na yi tayin kuka, ganin yanda take zama tai shiru wani sa'in tana kallan hoton Sageer yasa nai ta kuka nace a dawo Nigeria adauko mana shi. Tundaga lokacin Ummy ta ajiye hoton ta daina daukowa, shima Abba ganin haka yasa ya ajiye aikinsa muka dawo. Husain nada magana sannan akwai saukin kai, muna tsananin san Ummy sai dai shakuwar dake tsakanina da ita daban ce. Muna dawowa nace Abba na yaje ya dauko Sageer. Haka mukaje suka hanamu, gashi a kauye suke sun tubure akan dansu bazaiyi agola ba. Sai da Abba ya daukeni mukai zuwa kauyen nan sau kusan goma kafin su amince. Haka suka bamu shi muka kawoma Ummy shi, tayi kuka sosai dan bata taba tunanin za'a bata shi ba. A kuma lokacin ta dauki alkawarin bazata taba banbantamu da Sageer ba." Cikin tsananin mamaki Jalila ke jin wannan labarin, to meyasa Uncle yace bazai ko dan abinda su Hassan suka mai bazai iya musu butulci ba? Saboda daukoshi da sukai? Hassan yai shiru kafin ya dan runtse idanunsa, wani abu na ratsashi......... [12/7, 9:54 PM] El-hajj: πŸ—― *JALILAH* πŸ—― Written By : *AYUSHER MUHD* βœ”οΈote me on Wattpad : *Ayusher Mohd* *HASKE WRITER'S ASSOCIATION* (_D home of expert and perfect writer's_πŸ’‘) *53* Wata irin muguwar shakuwa ce tsakanina da Ummy wanda ko mahaifina banajin kaunarsa haka a raina, ita kanta ko yaya naji ciwo kafin nace da zafi fuskarta ce zata nuna tanajin zafin abin, hakan yasa ko banida lafiya banfiya nuna mata ba, Husain nada kawaici sannan baifiya makon uwa kamar ni ba, da farko bamu taba sanin ba Ummy bace ta haifemu saboda yanda muke, har saida muka dawo daga Cairo, mu kawai mun dauka kanin mu Sageer ne kawai babansa daban. Sageer shikansa baisani ba shi sai da yaje ziyara gun dangin mahaifinsa, sai dai koda wasa bai taba nuna mata ma ya sani ba, duk wani tunani da zakiyi akan yanda Uwa zataso danta Ummy na mana wannan san, Aunty Nana itace yayarsu Ummy amma mahaifiyarta daban, halayenta ba irin na Ummy bane sai dai itama ko da wasa bata nuna mudin ba 'ya'yan Ummy bane, har yau babu wanda na taba ji yace mu ba 'ya'yanta bane sai wanda ya sani tun fil'azal. Yai shiru sautin numfashinsa ya canza kafin yace "haka rayuwarmu ta taso cikin farinciki da kaunar juna har zuwa shekara 13, a lokacin mu muna shekara sha uku shi kuma Sageer na shekara 11, wannan lokacin ma aka kara samun matsala dan 'yan Uwan mahaifinsa daga zuwansa hutu suka rikeshi wai sun kula Ummy ba ta kawoshi duk hutu da alama so take ta daukeshi. Hankalinmu ya tashi dan ni da Husain har zazzabi mukai, sai dai ganin Ummy ta watsar da komai yasa muka ware muma. A wata rana wacce ta zamarmin ranar bakinciki a tarihin rayuwata, a lokacin kanin Abba yazo shida matarsa da 'ya'yansa sunzo gida tayamu murna na suna dan Allah ya albarkaci Ummy da samun 'ya mace ya wato Ameera. Dukansu mata ne sai Sudais kadai wanda yake namiji sannan shine karami dan shekararshi shida a lokacin, yan uwa da dama sunzo tayamu murna. Da yake ni duk inda taro yai yawa ba sanshi nake ba hakan yasa na fito daga cikin gida. Har nayi waje Husain ya kwallamin kira na juyo, yace "ina zaka?" Dayake akwai shaguna a karshen layin mu nace shago zani, yace "bari inzo muje." Nan ya taho da sauri, muna fita kofar gida mukaga Sudais, nace "Sudais daga ina?" Yace "alawa na siyo." Ya nuna mana alawar hannunsa, Husain ya amshi daya ya bude muka taho mu uku, muna tafe munata hira wanda ni kaina a yanzu na manta hira me mukeyi. Har mukaje karshen layin, hango wasu maza mukai a kan titi suna kan doki gashi mutane sai kallansu akeyi, abinka da yarinta kawai sai muka kutsa ciki kuna kallo. Daga tsallaken titi na hango wata mota kamar ta Abba, nace "Husain kaga motar Abba." Ni a guna nasan ba motar bace zolayarsa nakeyi, shikuma yana gani ya yarda yace "a
πŸ