a tai tace "me?"
Gani tai yayi gaba, da kallo ta bishi tace "yau maganar ma wahala take?"
Fitowa tai dan ta fahimci ta biyoshi yake nufi.
Haka ya fita, tana kokarin fita Ameera ta fito jitai tace "Amarya sai ina?"
Harararta tai tace "inda kika aikeni, kicema Ummy zamu fita."
Da gudu Ameera ta taho tace "ina zaku? A daren nan?"
Jalila ta in fada miki?
Tace eh ina? Ta fada tana matso da kunne Jalila tai dariya tace "inda Ameera ta aikemu."
Tai saurin yin waje tana dariya, dan tana tsoron karta dade a tsaye tai laifi.
Yana cikin mota harya tada ta bude gefensa zata shiga yace " shiga baya."
Komawa tai baya ta shiga tana yan kunkune, tana rufe mota yaja suka fita.
Suna fita motar Sageer na shiga gidan.
Tafiya yake, ba mai magana a cikin motar, ita kuma haushin ce mata dayai ta shiga baya yasa batai magana ba.
Kanta ta sunkuyar, jin alamun an tsaya yasa ta dago.
Gidan Goggo? Kallan gidan tai sannan ta kalleshi cikin mamaki.
Kashe motar yai sannan ya kwantar da kansa jikin kujera.
Jalila cikin mamaki tace "gidan Goggo?"
Shiru yai har tana tunanin bazaiyi magana ba, cikin wata murya taji yace.
" Jalila?"
A tsorace tace "naam."
Shiru ya sakeyi na wasu lokuta kafin yace " Zan fadamiki abinda ke damuna, abinda na aikata wanda a koda yaushe dana saninsa shike hanani sukuni, a duk sanda na tuno da abin ko cikin bacci ne nakan ji kamar nima na mutu, nakanji gaba daya duniyar ta zamarmin bakinkirin, nakanji komai na cikin duniyarnan ba abinda yake birgeni, zan sanar dake a gaban gidan mahaifiyarki idan harkinga bazaki iya zama dani ba, sai ki bude kofar ki shiga gida gun mahaifiyarki, in kuma har........."Sai yai shiru, dan bayasan yasa ransa akan abinda bazai samu ba.
Shiru ne ya kara ratsa cikin motar, ita kam Jalila tayi tsuru tsuru.
" Abdullah Taura shine mahaifina, tunda ya tafi karatu kasar Egypt suka rikeshi ya fara musu aiki a can, gaba daya mutum ne mai tsananin san aiki, hakan yasa ba ruwansa da mace balle aure.
Ganin yanda bashida niyyar yin aure yasa mahaifinsa ya masa kamun mata, wacce take 'yace ta abokinsa.
Amininsa ne tare suka taso, yanada 'ya'ya dayawa sai dai duk maza ne su uku ne mata.
Babbar yarinyar Uwargidan ce, su kuma biyun matarsa ta tsakiya ce ta haifesu, dan matansa uku.
Babbar tanada mijinta sai aka bashi ta tsakinyar mai suna Hauwa'u suna kiranta da Jidda.
Daga can aka sashi ya dawo, yana zuwa ya ganta ya aminta da ita akai aure a sati biyu da zuwansa dan dama sun shirya komai, anayi ya dau matarsa suka koma garin Egypt.
Bazaka taba tunanin auran hadi ne tsakaninsu ba dan suna kula da kaunar juna.
Basu dade da aureba Allah ya bata ciki.
Irin girman cikin yasa hankalin Taura ya tashi, ba shiri ya ajiye takarda akan yana bukatar hutu mai yawa suka taho.
Gidansu ya kaita dan hankalinsa da nata sai yafi kwanciya.
A lokacin da suka iso dama ana ta fama da bikin kanwarta, ganin yanda Yayarta ke shan wahala yasa sam hankalinta ya tashi, tana kuka muraran aka kaita gidan miji, haka aka gama biki lafiya ta tare, aka dukufa da mata rubutu da kula da ita, saboda cikin yasata ta kumbura sosai.
Taura a koda yaushe yana gidan, kai abin makulashe, magani da duba jikinta, har Allah ya kawo lokaci.
Satinta daya tana nakuda wanda ya kara wahalar da ita, aka dauketa aka kaita asibiti aka bata gado.
A wata ranar asabar aka yanke hukunci yi mata tiyata dan abin yaki karewa.
Kanwarta a rikice tazo asibitin dan labari ya kai mata, kuka kamar ranta zai fita, haka aka shiga da ita tiyata tana rike da hannun kanwarta.
A dakin tiyata ana zaro 'ya'yan nan biyu ana kokarin yi mata dinki tace ga garinku nan.
Tashin hankalin da suka fuskanta a asibitin nan ba'a magana.
Kowa ka gani hankalinsa a tashe yake, haka duk sanda aka kalli jariran nan biyu sai an zubar musu da hawaye.
Haka aka kaita gidanta, Taura kamar zaiyi hauka, dauriya kawai yakeyi ba magana, dan inya tuno da jariran yaran nan wadanda ko ganinta basuyi ba sai aji hankalinsa ya tashi.
Kanwarta ita ke kula dasu dan ko gidanta bata koma ba, dayake mijinta shima na gida ne, a karshen layin ma ya kama gida.
Jin ance ta koma gidanta yasa tace itakam dasu zata tafi, duk yanda akaso ta hakura amma taki, kuka ma tasa tace itakam abarta dan bazata iya barinsu ba.
Haka aka hakura ta tafi dasu, sai Taura ya hadata da kanwarsa wacce take shekara 14 suka tafi tana taimaka mata.
Gaba daya Taura ya canza, kullum sai yaje ganin yaran nan hankalinsa ke kwanciya, kowa ya gansu bazai taba cewa basuda uwa ba dan sosai take kula dasu, kowa jinjina mata yakeyi dan yarinyace sannan ko haihuwar fari batai ba.
Duk wani bukatunsu Taura ya dauke musu, sannan ya kasa komawa ma gun aikinsa.
Har yaran nan suka shiga shekara guda, suka fara tafiya, kowa ya gansu abin sha'awa."
Hassan yai ajiyar zuciya yace "A wata rana mahaifinta da mijinta sunyi tafiya sukai hatsari wanda ya dauki rayuwarsu.
Taga tashin hankali ga mutuwar miji ga kula da yara biyu, sannan gashi batasan tanada karamin ciki ba.
Gashi duk yanda akai yaran nan su barta taji da a