NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 107 of 172

*Ayusher Mohd* *HASKE WRITER'S ASSOCIATION* (_D home of expert and perfect writer's_💡) Thanks alot for the love 😍May Allah Subhanahu Watta'ala always help and guide us👏🏻 *52* Yanajin motsin shigowarta ya mike ya maida hoton sannan ya fito daga dakin, da kallo ta bishi tace "yaya!" Ko kallanta baiyi ba bare tasa ran zai amsa mata, saukowa kasa yai ya zauna a garden. Ita kuwa ganin yanda ya giftata ko kallanta baiyi ba tace "me kuma nai? Ni Habiba?" Abba ne ya dawo, yana sauka daga cikin mota ya hango kan Hassan, gunsa ya nufa. Jin motsin tahowar mutum yasa Hassan juyowa. Ganin Abba ne yasa ya juya yana kara tunani, Abba ya karaso ya zauna daf dashi. A hankali yace "sannu da zuwa." Abba yai murmushi yace "Eldest me kake tunani? Naga ka dade banganka anan ba." Hassan yai shiru sai dai ya kalli Abba. Abba ya sa hannu a kafadarsa kamar abokinsa yace "Mata ne?" Da sauri ya kalleshi. Abba yai murmushi yace " na canka kenan." Yai saurin cewa "a'a ko kadan." Abba yai dariya sannan ya sauke hannunsa daga kafadar Hassan, yadan yi shiru. Hassan bai kalleshi ba yace "ina yarinyar? Ka daina tunaninta?" Abba shima yana kallan kasa yadan hade hannayensa gu daya yadan matsa, yace " ba kamar da ba." Hassan ya dan kalleshi yace "kana tunanin santa kake?" Abba yace "yanzu gaskiya kakeso na fadama ko kuma abinda nasan zai kwanta maka?" Hassan yace "gaskiya!" Abba yadanyi murmushi kadan yace " inayi sosai, sai dai kamar yanda mahaifiyarka tace zanyi kokari ganin na cireta a raina, dan ina ji a jikina ni kaina ba san daya kamata nake mata ba." Hassan yai shiru kafin ya jinjina kai yace " nagode Abba da kake kokarin cire ta aranta dukda abin ba mai sauki bane." Abba ya riko hannunsa yace "kasan yanda hankalina ya tashi? Lokacin da naga kana fada akan abin? Nayi tir da zuciyata nayi dana sani wanda bazan iya misaltamaka ba." Hassan ya kalleshi sannan yace "bansan nima sanda na hau haka bane....." Abba ya kalleshi yace "naji dadi a kasan raina, at least inada wanda nasan zai hanani, kaga kamar Sageer na tabbatar bazai dage akan abinda nakeso ba, balle Amira, kai kuma ba lafiya ce dakai ba, balle ka hanani abinda zuciyata ke neman jefani, sai dai bansan har jikinka yayi sauki haka ba ina can ina shirme." Ya karasa maganar jiki a sanyaye. Hassan yai shiru kafin yace "Abba a koda yaushe ka dinga tuna wacece Ummy a garemu, in har wannan tunanin na zuwa maka na tabbatar ba abinda zai gifta zuciyarka." Kai ya jinjina yace "ni kaina bansan ya akai zuciyata ta nemi kawomin shirme haka ba, bayan nasan irin kaunar da kakema Mahaifiyarka, bayan kai din kaine rayuwata." Hassan ya kalleshi cikin wani yanayi na tausayawa. Can ya dauke kansa da sauri saboda kwallar dake neman taruwarmai a ido, ya juya kansa da sauri. Abba ya sake dafa kafadarsa yace "ya ya? Fada kukai da matar taka shine kai yaji?" Hassan ya kalleshi sannan ya dan murmusa kadan. Cikin tsananin mamaki Abba yace "Hassan murmushi kai?" Yace "wa? Ni?" Abba yace "sosai ma kuwa, na tabbatar kayi murmushi yanzun nan. Hassan ya mike da sauri, Abba ya jawoshi ya zauna ya riko hannunsa yace "nagode Hassan." Hassan ya kalleshi yace "name?" Yace "na komai ma, kai d'a na ne wanda na haifa sai dai ban taba alfahari da komai a rayuwa ba kamar ka."Jiki a sanyaye yake kallansa kafin yace "bancancanci samun wannan matsayin ba." Abba ya dan harareshi yace " in tuno ma?" Da sauri Hassan ya mike dan ya fahimci abinda yake nufi yai hanyar ciki, Abba na cewa "in ban tuno ma ba na tunawa matarka." Da sauri ya shiga ciki, Abba ya bishi da kallo cikin tausayawa, har idanunsa suka dan canza, ya juyo tare da dan runtse ido yace "Alhamdulila!" Tana kasa taga hawansa sama, da kallo ta bishi, shigewa yai. Bata hau sama ba sai bayan magrib, dan sunatare da Ameera da Ummy bayan ta dawo daga makaranta, bayan magrib din ma Ummy ce tacemata dare yayi. Ameera tai dariya tace "kai Ummy ba kara?" Ummy tasa hannu tadan kwadeta tace "zaki fara ko?" Mikewa tai ta hau sama, Ummy ma ta mike tace "ke kuma sai kiyi ta zaman gulma. Ameera tace "bari na jira Ya Sageer ya dawo muyi hira, tunda dai ni kowa ya watse ya barni." Ummy tai tafiyarta tana cewa "bari ma na kirashi naji naga ya dade bai dawo ba." Jalila tana hawa sama ta ganshi a kwance, yau ba karatu yake ba sai dai a kwance kawai yake shiru, ta shiga da salama. A hankali ya amsa wanda ita kanta bataji ba, shiga ciki tai tana kallansa. Yaci abinci, a ranta tace yau ba jira?amma rannan harda jin haushinsa. Hartana neman zama a kan kujera sai ta juyo ta fito falo ta zauna, ta kunna Tv. Shiru tai tana tunani, meke damunshi? Ko bashida lafiya ne? Da sauri ta mike ta shiga dakin, tazo jikin gado tace " Yaya? Bakajin dadi ne?" Kai kawai ya girgiza mata alamar a'a idanunsa a rufe. Tai shiru kafin ta juya, har zata fita sai kuka ta shiga toilet. Tana rufo kofar ya mike, ya kalli kofar toilet din. Mikewa tsaye yai ya dau makullin mota ya dau wayarsa. Tana fitowa ya kalleta ya mika mata hijab dinta, kallans
🏠