na sama, Mumy kuma itama ko tana falo ko daki, dama gun Goggo nane muke zama muyi ta hirarmu."
Ummy tace "sanda kowa yake zama, bacci da kallo ke me kikeyi?"
Tace "aiki, girki, ko wanki."
Ummy tace "hmm da alama ya kamata ki kara samun hutu a gidan nan, yanda kikai aiki acan ba hutu yanzu duk sai ki fanshe hutunki gun mijinki."
Jalila tai dariya tace "ai nan gidan ba aiki Ummy."
Tace "ba wani nan, ina mijin naki?"
Cikin kunya ta girgiza kai.
Ummy tai ajiyar zuciya tace "Haryanzu baice miki zai fita?"
Tace "eh, yanzu ma fa....."
Sai kuma tai shiru tare da sa dariya.
Ummy ma tai dariya tace "Jalila bansan ke ba amma i am sure Hassan na sanki, idanunsa kadai sun tabbatar da hakan."
Jalila ta kalleta sai dai batace komai ba.
Ummy ta dafata tace "Jalila godiya, kina sani farincikin dana dade bansamu ba, ganin Hassan na samun sauki yasa kullum zuciyata nakejinta tass, shikansa mahaifinshi yanzu hankalinsa yafi kwanciya har yake fita aiki ya dade haka."Jalila ta sunkuyar da kai a ranta tace me nayi? Ummy tace "mungode Jalila, sai dai ki kara hakuri sannan ki kara kula dashi, insha Allahu bazaki tabba dana sanin auran Hassan ba."
Dagowa tai ta kalli Ummy sannan ta daga kai alamar to.
Hassan na fita yaje bakin wani shago yai parkin, fita yai ya shiga ciki.
Mai shagon ya tambayeshi abinda yakeso, Hassan yai shiru kafin yace "kawai abashi abunda ya dace."
Cikin mamaki mai shagon yace "abinda ya dace kamar me kenan?"
Gidan mamar matata zankai, ya fada tare da dauke kai.
Mai shagon ya guntse dariyarsa sannan yace "katan din juice fa?"
Hassan yace dame?
Yace sai ka hada ko da kayan tea ne.
Hassan yace "samin to."
Nan mai shagon ya laftamai kayan tea dan kana kallan motarsa kasan da akwai kudi, ya sa mai juice kala uku a bayan boot ya cafki kudinsa.
Hassan na fita yace "Alhamdulila Allah ya kara kawoka."
Hassan ya shiga mota yai gidan Goggo.
Ya dade a waje yana tunanin abinda zaice kafin ya shiga.
Almajirai yasa suka shiga da kayan.
Goggo na zaune tana jin radio ana hada musu wuta a waje ya shiga ciki.
Tanaganinsa ta mike fuska dauke da fara'a tana lale lale.
Ya zauna ya gaisheta ta amsa cikin farinciki, shidai yai shiru.
Kowa ta tambayeshi sai dai yace "lafiya."
Data gama tambayar tai shiru shima yai shiru.
Can yace "ba wuta ne? Naga kamar da wuta a layin?"
Tace "gyarawa sukeyi yanzu, Hassan mungode sosai sosai, Allah yayi albarka ya inganta rayuwa."
Yace Ameen
Shiru suka karayi kafin ya mike yace zai tafi.
Tace "da wuri haka?"
Yace "eh."
Tace "to mungode."
Tana fitowa waje tai karo da kayayaki, nan ta kara mai godiya har ya fita.
Mota ya shiga yai ajiyar zuciya, sannan ya tada kota ya juyo gida.
Jalila kuwa bayan ta gama komai a kasa, ta daura abincin ran.
Yana shiga yaji motsi a kitchen, lekawa kitchen din yai, hangota yai tana aiki, yanka vegetables takeyi, tsayawa yai daga inda yake ya kura mata ido, gaba daya yanayin fuskarsa ya canza.
Ya dade yana kallanta har itama jikinta ya bata ta juyo.
Ganinsa tai a tsaye da alama ya tafi tunani, ta matso tace "Yayah!"
Kallanta yai yaganta a gabansa, tace "yaya naga kana......"
Da sauri ya wayance yace "kallan yanda kike aiki nakeyi, kin tabbatar kin wankesu kafin ki fara yankawa dai ko? Dan naga kamar baki wanke ba."
Cikin mamaki ta kalleshi, juyawa yai ya fita, da kallonta bishi,, yanzu kam ranta ya sosu, me yake nufi?
Haka ta cigaba da aikin ta ranta a bace, dan bakin cikin har kwalla ce tadan zubo mata.
Shikuwa yana hawa sama ya bude drawer ya dauko hoton Husain yana kallo, a fili cikin wata murya yace "Husain ya zanyi? Nasan bai kamata ba, bai kamata nai sha'awar rayuwa ta jin dadi da wata ba, ban cancanci yin farinciki ba, ban cancanci a soni ko inso wani ba sai dai bansan meke damuna ba, Husain i am really hurting her, wanda nakeji kamar na fita jin zafin abinda nake aikata mata."
"Zuciyata na kwadaitamin yin rayuwa da ita, zuciyata na san ta kyautata mata, inasan ingana cikin farinciki, Husain inajina kamar bani ba."
Yai shiru tare da rutse idanunsa, ya koma ya jingina da jikin drawer din, a ransa yace "Husain zan sanar da ita komai, dan abinda zuciyata ke rayamin kenan, in har na sanar da ita zan barta tai deciding abinda taga ya dace, inhar tana tunanin rabuwa dani shine mafita shikenan, in kuma....."
Sai yai shiru, tare da kara runtse idanunsa,shiru yai ya dora hannunsa akan goshinsa yana tunanin abinda ya faru a baya.
Baisan hawaye sun zubo mai ba.
**********
Mumy ce ta kalli Dady bayan ta amshi hular dake kansa tace "Dadyn Yasmeen! Inna ta yarda."
Yace "dame?"
Tace "bazata daurama laifin abinda ya faru ba."
Yace " meyasa kike takurama kanki? Nacemiki bakomai, zan iya yin komai indai a kanku ne."
Ta ajiye hular ta rungumeshi tace " karka damu, na fadama it's my turn to protect you"
Kallanta ya shafa sannan yace " nine ya kamata nai protecting dinki ke da yarana."
A tare sukai murmushi......
#OneLuv๐
[12/7, 9:54 PM] El-hajj: ๐ฏ *JALILAH* ๐ฏ
Written By : *AYUSHER MUHD*
โ๏ธote me on Wattpad :