NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 105 of 172

Yake hanashi shiga mutane? Yake hanashi murmushi? Yake hanashi zama cikin yan uwansa? Shiru tai tana tunani, da alama shima yanada painful past wanda yafi nata. Yana fitowa daga wanka ya shirya, ganin bata dakin ga motsin karar TV a falon yasa yasan tana can, sai dai bazai iya kiranta ba. Zama yai akan kujera yana kallan kofa yana jiran shigowarta, dan yunwa yakeji. Jalila kuwa ta shiga tunani sai can ta dawo daga tunanin nata, ta mike ta bude kofar, a zaune taganshi tana shiga suna hada ido, yana kallanta yai saurin dauke kai. Ta shigo ciki tace "Yaya ka fito shine ba magana?" Bai kalleta ba yace "inyi magana ince me?" Ta kalleshi tace "kacemin ka fito in taso." Ya kalleta yace "gashinan ai ban kiraki ba kin taso." Tace "lalai yaya, to bari nakoma sai ka kirani." Tai maganar cikin zolaya. Yace "nidai kafin ki koma bani abinci naci inyaso sai ki koma." Ta kalleshi tadan canza fuska tace "ba kara ma kenan? Bari na fadama Ummy to nace kace ba sai naci abinci ba." Baisan sanda ya dan murmusa ba yace "yaushe kika koma haka?" Matsowa tai tace "yaya wlh yanzu bakinka ya motsa, wallahi yau na gani sosai." Tsuke fuska yai yace "yau menene ruwanku da dariyata?" Tace "ni kuwa nake da ruwa yaya, bakasan yanda abin ke damuna ba, kome fa zakace fuskarnan a tsuke kake fada." Kallanta yai yace "bakyaso?" Ta daga kai da sauri tace "sosai ma, wani sa'in in tone din maganarka ya koma cold sai jikina yai sanyi." Kalaman Ummy ya tuno data fadamai dazu, kallanta yai yace "magana zaki tsaya yi bazakiban abinci ba?" Ta dan turo baki ta nufi inda ta ajiye abincin, a ranta tana cewa what am I expecting? Zubamai tai tace "ka sauko." Yace "yanzun ma kin manta da plate din ne? Dan muci tare?" Cikin shagwaba tace "yaya Allah fa ba haka bane." Yace "shagwaba kika koma?" Ta kalleshi tace "yaya wai meyasa kakemin haka?" "Menai?" Ta kalleshi kamar zatai magana sai kuma tai shiru, a ranta tace "rannan kamin kiss bance komai ba, jiya ka kwanta a cinyata bance komai ba amma kai komai nai sai ka fassara." Mikewa taga yayi ya wuceta ya zauna a inda ta zubamai abincin. Kallanta yai tana tsaye hannu yasa ya jawota, ta zauna a kusa dashi. Kallansa tai tana mamaki tace "Yaya!" Yace "wai ni yaushe nake yayanki ne? Kin kama suna kin rike kamar ke kika samin?" Baki tadan turo sannan ta zuba abinci a nata plate din, gani tai yasa spoon dinshi cikin plate dinta. Da sauri ta kalleshi yace "ba haka kikeso ba?" Tace " bangane ba....? Bai kara mata magana ba yacigaba da ci, kallansa ta tsaya yi tama kasa ci, sai can ya kalleta yace "kin koshi ne?" Spoon din ta maida ciki ta cigaba daci ta mamakin wannan abu. Yana gamawa ya dau key ya bar dakin baice mata komai ba, baki ta saki tana kallan ikon Allah. Saukowa yai kasa ba kowa a falon, yai hanyar waje. Mota ya shiga kawai ya fita, Jalila ta dade a zaune kafin ta kwaso kwanuka ta fito. Ganin bakowa a falon ta wuce kitchen ta wanke kwanukan, tasan Ameera na skul, da alama Ummy na daki. Sageer fa? Bude kofar daki taji da sauri ta kalli gun. Sageer ne ya fito sanye da kaya da hula da alama fita zaiyi. Kallanshi tai shima ya kalleta, da sauri ta dauke kai ta juya zata koma kitchen. Yace "Jalila?" Tsayawa tai a inda take sannan ta juyo ta kalleshi. Ya matso inda take kadan ya kalleta yace "ina making dinki uncomfortable ko?" Kallansa tai ta girgiza kai alamar a'a sannan tace "a'a Yai murmushi yace "kiyi hakuri Jalila." Tace "Uncle sai yaushe ne zaka daina bani hakuri? Bazance ban taba jin zafin abinda ya faru ba, dan da naji zafinka sosai sai dai a yanzu ko kadan banajin zafin ka, na fahimceka, nasan dalilinka." Kallanta yai yace "nagode Jalila, nagode da fahimtar da kikamin." Ta kalleshi tace "Ummy tace duk ka canza, ni kaina nasan ba haka kake ba, Allah yasa banice sillar canzawarka ba." Ido ya kura mata kafin yace "ko kadan Jalila, inma akwai dalili to bazai wuce zuciyata ba wanda kuma basai kin damu da ita ba, zata daina da kanta." Kallansa tai tace "Uncle!" Yace "kidinga cemin Sageer kawai, hakan shine daidai a matsayinki na matar yayana." Shiru tai kafin tace "saidai na kiraka da Yaya sageer yanda Ameera ke cewa." Yace "hakan yayi, nagode Jalila sannan Please let us take it to our grave, kar kowa yasan abinda ya faru." Zatai magana sukaji muryar Ummy tana cewa "Sageer fita zakai?" Da sauri ya juya dan baiji karar kofa ba, Jalila ma ta kalleta. Ummy ta kalleshi tace "menene?" Yace ba komai, na fito ne banganki ba nake tambayar matar Yaya. Tace "ina ciki ina addu'oi. Yace "Ummy zanje gun Abban." Tace "to Allah ya bada sa'a." Yace "Ameen ya fita." Ummy ta kalli Jalila tace "Jalila!" Jalila ta matso tana cewa " Ummy nikam banga Ameera ba." Ummy tace "sun koma skul yau dama hutu ya kare." Tace "oh shiyasa, naji gidan shiru." Ummy tai dariya tace "wlh kuwa, Jalila gidan namu is so boring." Jalila tai dariya itama tace "muma haka gidan yake, Sultan kullum yana daki yana game ko jin kida, Safeena kuma tana gun Mumy ko suna kallo ita da Yasmeen, Inna
🏠