ย  ย  NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 103 of 172

Yace "wlh Hajiya bansani ba, waya yamin yace in daukoki." Tace "okay." Haka suka isa gida taitama Ummy godiya da Abba. Kafin ta hau sama. A daki ta sameshi yana karatu, sallamarta kawai ya amsa shima baiko kalleta ba, Jalila ta daure tace "Yaya na dawo." Yace "naganki." Shiru tai a tsaye kafin ta nufi toilet, tai wanka ta sa kayan bacci sannan ta fito ta dau bargo ta shimfida tana cewa "Yaya bacci nakeji, yau da alama na zama kasa, ko dan banyi baccin safe bane? Ina ta zumudi?" Bai tanka mata ba, tai dariya tace "hmm basa banba, ni fa da agida bansan ma wani baccin safe ba amma yanzu jin dadi yasa har in banyi ba sai naji wani iri." Bai tanka mata ba hakan yasata yin shiru, ta sa bargo ta kwanta, bata dade ba bacci ya dauketa. Juyowa yai ya ajiye littafin ya kura mata ido, idanunsa ne suka canza kala a fili yace " Jalilah! Jalilah!" Sannan yai shiru, mikewa yai ya shiga toilet ya watsa ruwan zafi sannan ya zura riga, harzai wuceta ya tsaya, sai kuma ya koma ya zauna kusa da ita. Hannu yasa a gefen fuskarta yana kallanta cikin wani yanayi. Cikin wata raunaniyar murya yace " nasan i am hurting u, sai dai kafin kiji zafin abinda nake miki ni na ji zafi, duk sanda na wulakantaki inaji a jikina sai dai bansan ya zanyi ba, Jalilah bansan ya zanyi ba banasan naga na dawwama a koda yaushe a cikin kuntata miki." Shiru yai yanajin wani abu a kirjinsa kafin yace "Jalila Husain......." Ya runtse ido a hankali wasu hawaye naga sun zubomai masu zafi, hannunsa yakai kan labanta. Idanunsa ya sake rufewa a hankali ya shiga matso da kansa ya sumbashi bakinta, bakinsa ya bari a kan labanta. Idanunta ta bude, me zata gani? Shima idanu ya bude suka kalli juna, da sauri tasa hannu ta tureshi, ya mike tsaye da sauri. Tace "Yaya!" Yace "bargona nakesan dauka sanyi nakeji." Tace "bargo?" Bargo a....... Ta kasa karasawa, yace "bargo a me?" Tace "bakomai, nagane tun jiya kaki kulani, yanzu kuma gashi kanamin magana." Yace "yanzun ma bakiji me nace miki ba? Bargona zaki bani." Tace "to in na baka in shimfida me?" Ya kalleta taya zaiyi yace mata shi kwanan kasan ne bayaso? Ya hade fuska yace "sai ki kwanta akan gado ni sam laushin katifa samin ciwon baya take." Da sauri tace "haba? Da gaske na kwanta?" Ya kalleta sannan ya dau bargonsa ya kwanta akasa. Murmushi tai sannan ta hau kan gado tana dariya jin dadi. Can kuma tace "yaya badai barmin kai ba?" Yace "barmiki? Bakiji me nace ba?" Tace "oh naji." Ta kwanta tare da juya baya. Shiru tai kamar mai bacci tana tunanin abinda ya faru yanzu, hannunta takai kan labanta ta shafasu, shima kwanciya yai yana tuno abinda ya faru, me yakai shi? Baisan ya akai yaji a lokacin sumbatarta yakesan yi ba. Ahhh kansa ya shafa yace "Hassan!" #OneLuv๐Ÿ’• [12/7, 9:54 PM] El-hajj: *JALILAH* ๐Ÿ—ฏ Written By : *AYUSHER MUHD* โœ”๏ธote me on Wattpad : *Ayusher Mohd* *HASKE WRITER'S ASSOCIATION* (_D home of expert and perfect writer's_๐Ÿ’ก) *50* Yana cikin barci wajen karfe uku taji ana wani irin numfashi sama sama, yanzu kam ta riga tasan shine da sauri ta sa hannu ta danna waayarta sannan ta kunna fitilar dakin, yau a rufda ciki ta gashi ya tukunkune daga can gefe hannunsa nakan wuyansa gaba daya zufa ce take keto masa, mikewa tai da sauri tazo kusa dashi. Hannuntasa ta janye hannunsa daga kan wuyansa, idanunta sun ciciko tana kiran sunansa. Amma ina, hannunsa ya fizge daga gunta ya rike kansa dake wani irin sarawa, Jalila ta ga yau abin nasa dayawa dan har pillow ya dauka ya danne kansa dashi. Cikin tsoro da tausayinsa yasa ta janyowshi ta rungumeshi ta baya tare da sa kuka tana cewa "Yaya! Yaya dan Allah kandaina......." Jitai jikinshi duk yanata ketowa da zufa, sakeshi tai da sauri ta kure karfin AC din dakin sannan ta dawo a rikice ta kara janyoshi tana kuka. Yau abin ya dade dan ita kawai data rungumeshi ta kifa kanta a jikinsa bata sake dagowa ba. A hankali numfashinsa ya dawo, ya bude idanunsa, ganinshi yai a jikin Jalila tanata kuka. Shiru yai cikin takaici abinda ke faruwa wanda gashi duk sanda abin ya tashi sai yasa Jalila kuka haka. Mikewa ya fara kukarinyi, idanunta ta bude ta daukeshi a kansa, da sauri tace Yaya? Zama yai sannan ya jawota kusa dashi, jiki a sanyaye take kallanshi. Bata an kara ba taji ya rungumeta tsam, ya kwantar da kansa kan kafadarta. Bakinta na rawa tace "Yaya!" "Let's stay like this for a moment......" cikin wata murya mai sanyi ya fadi hakan, shiru tai ta kasa motsi. Can yasa hannu a bayanta kamar me lallashi yace " sai yaushene zaki canza hobby dinki?" A hankali tace " to ya zanyi duk ka canza lokaci daya, ga....." Yace "are u worried about me or are u scared?" Tace "zaka fara ko Yaya?" Shiru yai kafin ya saketa ya kalleta yace "irin wannan kure mana AC haka fa?" Ta tashi ta dau remote tana cewa, zufa kaketayi shiyasa na kunna. Ya kafeta da ido yace "kin tabbatar dan ni kika kunna?" Tace " ban gane ba???" Yace "a'a to haka kawai dan ina zufa sai a kure AC haka?" Ta kalleshi tace "nikam ko dan ka kwanta a
๐Ÿ