NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 102 of 172

inci?" Sunkuyar da kanta tai, Ummy ta amshi ledar hannun Sageer tace "ga shi kije kuci da Hassan muma munyo namu tsarabar." Jalila ta amsa tace "angode." Ta fada sannan ta leka bayan Ummy, Ummy tace "tana can." Jalila ta sunkuyar da kai tace "tam." Ameera ta matso tace "ya jikin?" Jalila tace da sauki. Ummu tai gaba Ameera ma tabita, ta kalli Sageer tace "Sannu da zuwa." Kallanta yai yace "ya jiki?" Tace "na ware ba wani serious bane dama." Ya kalleta cikin kulawa yace "Sannu Allah ya kara sauki." Tace Ameen ta juya, da kallo ya bita. Kowa daki ya shiga da ledarsa dan duk sun gaji. Jalila ta wuce sama. Tana shiga ta sameshi a zaune, yana ganinta ya dau littafi wai karatu yake. A ranta tace ko gajiya bayayi. Ta matso dan dama ta dauko plate daga kasa, ta bude tace "yaya sauko Ummy ta kawo mana abin dadi." Kallanta yai yace "menene abin dadin?" Ta bude kedar ta ciro ledar juice sannan ta ciro foil paper ta bude, kaza ce da kuma daurin kundu wanda yasha hadi na musamman. Juyowa tai ta kalleshi, kallanta yai sannan ya sauko fuska ya zauna, dandai yunwa yakeji amma da cewa zaiyi bazaici ba. Kallansa tai batasan yanda zata raba musu ba gashi plate daya ta dauko, kallansa tai shima kallanta yai tace bari na dauko wani plate din. Ta fada tana kokarin mikewa, hannu yasa akan hannunta data dafa kasa zata tashi, kallansa tai, yace "muci tare." Tace "naam?" Yace "me? Dama ba haka kikeso ba?" Tace "nakeso kamar ya kenan?" Yace "duba ki gani, kinsan mu biyu ne a dakin nan kika dauko plate daya, yimin bayani meyasa kikai hakan to?"Jalila ta kalleshi kamar zatai magana kawai sai tasa dariya tace "lalai Yaya, yanzu nace zan dauko plate ka hanani sannan kace nice nakeso." Yace "to ba hakan bane?" Tace "wlh ba haka bane, ni na....." Yanda ya mata da fuskarsa ne yasata ta kasa magana alamar bayarda zaiyi da duk abinda ta ce ba. Bismilla tai tasa hannu tana cewa "shikenan tunda an dakeni an hanani kuka." Bai tanka mata ba yasa hannunsa, a tare suka fara ci, itadai kunya take, shikam wani irin sanyi yakeji a ransa, yana kallanta yasa hannu cikin plate din, a kann hannunta yasa hannunsa. Dagowa tai ta kalleshi, kallanta yai sannan ya kalli hannunsa, yace "yanzu nine nasa hannuna ko kece?" Tai dariya sannan ta kalli hannun nashi tace "to hannun waye a sama?" Ya kalla yace "nawa ne sai dai me yasa nakeji a jikina kamar dauramin akai?" Tace "me? Daurama?" Dariya ta fara yi tana kallansa, samun kansa yak da shagala gun kallanta, wanda har bai san ganin yanda take dariya yasashi sakar murmushi ba. Tsayawa tai da dariya tace "Yaya! Kasan kayi murmushi yanzu?" Fuska ya hade tare da zare hannunsa da sauri yace " a ina nai murmushin?" Tace "wallahi kayi yanzu, baka san kayi ba?" Juya kansa gefe yai yace "u are mistaken." Tai shiru tana kallansa kafin tace " mistake nai? Amma na tabbatar naga kayi murmushi." Yace "are u sure ba hakan kike san gani ba?" Tace"wannan karan bazan musa ba, dan ina san inga ka yi murmushi kullum fuskarka a daure take." Ya kalleta tare da daukan cup din juice yasha. Haka sukaci abinci tare sannan ta mike ta wanke hannu ta sauka kasa dan kai plate. Tana fita ya saki ajiyar zuciya yace "Hassan?" Gaban madubi ya koma ya kalli kansa, a hankali naga yanayin fuskarsa ya canza zuwa tashin hankali, yasa hannu ya bude drawer karshe ta jikin madubi. Wani littafi ya dauko ya bude tsakiyar hoto be ya bayyana, kallan hoton yai cikin wani yanayi sannan yamaida hoton ya rufe ya runtse idanunsa, bancancanci farinciki ba, ban kuma cancanci inso ko a so ni ba. Mikewa yai ya dafa kansa dake sarawa........ Gaba daya ranar bai sake magana ba har ta gaji ta kwanta dan ba alamar fuska. Washegari ma da Ummy tace ya kaita gidan Goggo bai musa ba ya jira ta suka fita tare, yana kaita kofar gidan baijira me zatace ba yai gaba. Da kallo tabi motar tana mamakin abinda ya faru, ko a mota duk yanda taso suyi magana kin yarda yai. Shikuwa yana ajiyeta yaja mota yana tunani. Jalila kam tana shiga gidan Goggo ta saki baki tana kallan iko Allah, ta shigar da kayan data taho dashi, nan suka zauna suka hau hira cikin farin ciki. Lantana ma ta zauna sukaita hira. Goggo cikin hira ne take tambayarta wanda ya kawota. Jalila tace driver dinsu ne ya kawoni, Yaya ya fita ne. Goggo tace "Allah sarki, na dauka shine ince bai shigo mun gaisa ba na mai godiya." Jalila tace "zaizo shima." Haka sukai ta hira suna tuno rayuwar baya da yanda sukasha wahala, Goggo tanata kara nuna mata ta kula da mutanen nan dan tabbas sun musu hallacin da basu taba tunani ba. Jalila jefi jefi tana tuno abinda yaya ya mata yanzu da zata sauko, ta fito ta kalleshi tace "Yaya baza......" Gano tai ya dauke kai yana neman wucewa. Tsayawa tai dagalo tana kallan ikon Allah kafin ta shigo. Meya sameshi? Sai bayan magrib yaro ya turo ta fito, tana fitowa taga Mamman, jikinta ne yai sanyi ta bude bayan mota ta shiga tayima Lantana da Goggo sallama akan sai ta dawo. Haka suka hau hanya, ta kasa daurewa tace "Mamman ina Yayan?"
🏠