NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 10 of 172

kai, tun dazu nake kai na kemin ciwo. Parking yai da saurin ganin chemist a tsallaken titi sannan ya fita. An miko mishi magani kenan zai amsa ta shigo da sauri, kallo d'aya zaka mata kasan hankalinta a tashe yake, tana zuwa tace " Dan Allah maganin ciwon kafa." Nurse din ne ya kalleta yace " Ciwon kafa wani iri?" Tace " ban sani ba kawai kafar Goggo ce ta kumbura." Tana hawaye take mai bayani. Wanda yazo siyar maganin ciwon kai sai duk tausayin yarinyar nan ya kamashi, zuciyarshi yaji ta shiga cikin matsananciyar damuwa na ganin yanda yarinyar nan take hawaye. Yace "Ku kaita asibiti mana." Bata ko kalleshi ba tace " Dan Allah nikam ka bani maganin da zai taimaka mata, banida kudi yanzu sai dari biyu, inya fi haka zan kawoma ko gobe ne." Tsananin tausayinta ya kara shigarsa kallan Nurse din yai sannan yamai alama daya hada mata maganin nan masu kyau, bayan ya bata ta mai godiya ta fita. Kallan Uncle take idanunta sun ciciko da hawaye, ba shakka daga baya tayi ta mamakin arhar maganin kenan Uncle siya mata yai? Dan ko bai fada ba tasan da kanshi yake, tunda dai na farko itace yarinyar, to in har abokinsa ne yaza'ai yabashi labari haka dala dala? Sagir yace " tundaga wannan rana Abokin nan nawa ya shiga wani yanayi akan yarinyar nan, jefi jefi yanabi ta layin nan ko zai ganta, sai dai cikin rashin sa'a bai sake ganinta ba har sai da akai assigning dinsa zuwa inda zaiyi bautar kasar sa, duk yanda yaso ya daure akan san yarinyar nan da damuwa da ita ya kasa, shine nake so ki ban shawara me abokin nan nawa ya kamata yai? Yana tsoron kar ya bari ya huce....." Wata irin kunyarsa ce ta kamata, kanta na kasa tana wasa da hannunta tana murmushi. Yace "Jalila, bakice komai ba? Ko ba kya ganin yarinyar nan zata soshi?" D'agowa tai cikin jin kunya tace " Ta ya zatai ta......." Yanda yake kallanta ne yasa tai saurin sa tafukan hannayenta ta rufe fuskarta cikin jin kunya." Yace idanunsa na kanta "Ya zatai ta soshi?" Kallansa tai da sauri tare da cewa ba haka zance ba...." Murmushi yai sannan yace"Ya za'ai ta kasa sanshi?" Da sauri ta mike cikin tsananin jin kunya tai hanyar waje, har taje kofa zata fita taji yace " ba kya tunanin abokin nawa yayi rashin kunya? Duba da yanayinta na dalibarsa?" Bata juyo ba tace " Ai ba malami ne na dindindin ba sannan ko malamin ne banaji......." Sai kuma ta kasa karasawa tana murmushi, yace "wasa wasa al'adarki ce tsayawa a tsakiyar magana, gashi nikuma zuciyata so take taji me zakice." Cikin jin kunya ta juyo ta kalleshi sannan taj waje da sauri. Idanunsa ya lumshe cikin wani irin jin dadi sannan yabi bayan kofar data fita da kallo. Jalila kam tana tsaye ita kadai tana murmushi, lalai yau tana cikin jin dadi. Ganin motarsu tayi parking ne yasa tai saurin shiga dan ta hango Uncle na tahowa, ita kuma yanzu kunyarsa takeji. Tana shiga motar Safeena tace " Jalila ya sunan wannan malamin?" Jalila ta hade rai tace "Wanne?" "Wanda muka gani dazu da safe, yauwa wanda ya ajiye motar can." Ta fada tana nuna motar uncle Sagir. Jalila ta kara hade rai tace "menene?" Safeena tace "Meye kuwa, kawai dai burgeni yai nake tambaya." Jalila tace "Sai ki tambayi matarsa dan ni bansani ba." Safeena tace "Yana da mata?" Jalila ta guntse dariyarta a ranta tace "yayarki ba insha Allah." ************* Hassan shi kadai a zaune a garden din gidansu, dan da kyar Ummy ta lalabashi ya fito, idanunsa a rufe sai dai ni kaina bansan tunanin me yake yi ba, ko kuna idanun kadai ya rufe. Daga bayansa yaji an rufe masa idanu, mikewa yai a zabure, Aina ta turo baki tace "Yaya!" Kallanta yai sannan yace "Meye hakan?" Tace "Yaya wai ni sai yaushene inka ganni zaka nuna farinciki kamar da?" Bai tanka mata ba sai kokarin barin gun da yai,idanunta ne suka canza, tsananin tausayinsa ya kara ratsata, sai yaushene Yaya zai dawo kamar da? Tana tsaye har sai da taga ya kulle. Tahowa tai daga gun jiki a sayaye, tana tura kofa taji ance "WAH!" Idanu ta runtse dan ta tsorata, dariya taji an kwashe mata dashi, ta bude idanunta cikin shagwaba tace "Ya Sagir!" Yace "Matsoraciya!" Tace "Naji din na tabbatar ko kaine sai ka tsorata." A tare suka nufi cikin falon suna tafe suna hira, Ummy tace "Haba Aina, an shigo da trolly banga mai trolly din ba." Tace "Ummy Yaya na hango shine naje mu gaisa." Ummy tace "kece ashe kika koroshi daga inda yake" Kusa da Ummyn taje tare da zama a kasa tace "Ummy ina wuni?" Ummy ta amsa sannan Aina tace "Ya jikin Yayan?" "Jiki Alhamdulila zance kenan? Sai fatan Allah ya yayemai larurar nan." Tausayin Ummy ne ya kama Sagir, kusa da ita ya zauna yace "Ummy d'anki yayi girlfriend" Kallansa tai tace "Haba?" Aina ta tabe baki tace " da alama yarinyar bata da taste." Harararta yai tare da maka mata pillow yace " uwar sanjin gulma sai kije can ki shiga da kayanki kafin Ameera ta dawo." Ta tabe baki sannan ta mike tare da jan Trolly dinta. Ummy cikin zumudi tace "a ina take Sagir?" Yace "Mak
🏠