a da kallo da idanunsa da sunfaramai dishi dishi, cambass dinta yaga ta dauka tarike a hannu tadaga sama irin dashi zata kwada musu idan sune, fitowa zaure tayi sai alokacin ta gane gidan makociyarsu ake bugawa da karfin gaske ana cewa. “Open the door is Soldiers” haba jin haka yasa wani karfi yazoma Safeerah tunda ga hukuma sune zasu iya taimakon bawan Allahn chan su fito dashi batare da an kashesa ba, yarda kambass din tayi ta shiga bude kofansu da saurinta, tana budewa taga sojoji anan lungunsu sunfi guda talatin ga manya manyan bindigogi a hannayensu dayasa taci cikinta ya daure daidai itama Maman Habiba nabude kofa gabanta na faduwa, ganin sun kallo Safeerah dukansu yasa tafashe da kuka tace “banine ba” tanuna cikin gidansu tace “dan Allah ku taimaki wani bawan Allah dasuka kusan kashewa yana cikin gidan nan” dasauri duk suka kalleta Babban cikinsu yace “lead d way” dasauri tajuya takoma ciki suka biyota har cikin dakinsu, ana ganinsa sojojin sukai kansa da gudu. “Sir Sir” kawai suke fada amman baya hayyacinsa, daukansa sukai yadan bude idanu kadan yabi kowa da kallo sai kuma ya lumshe idanun ruf arude sukace “Sir” Babban yace “let’s move” sukai waje dashi Safeerah ta bisu da gudu ba takalmi kafanta, ta tsaya gaban lungun gidansu, motocin sojoji sunfi goma tagani sunyi layi, bude mota akayi ana kokarin sakashi yabude idanunsa kadan yakallota, duk cikin uban sojojin nan da mutanen anguwa da aka fiffito ita kadaine wearing white, no shoes a kafafunta, those eyes looking reddish, sunyi ja, she looks like an innocent angel, bakinsa ya shiga motsi amman haka aka sakasa amota sukaja motan da mahaukacin gudu, sauran sojoji suka tsaya dan saisun nemo wayanda sukai this act suci ubansu, daidai wani mutum dabazai wuce 50yrs ba baida jiki siriri ne sosai ga furfura a fuskansa rikeda wani jaka yazo wajen ya tsaya gefenta yace “meke faruwa anan Safeerah? Ina takalmi”? Kafin tai magana wani soja yace “Ke!” Wani firgicewa Safeerah tayi saida tarike Baba gam tace “na….na’am” sojan yazo ya tsaya gabanta fuskansa ba rahama yace “agidanku akaga Oga meya faru? Waya tabamana Oga”? Wlh tsabaragen rudewa batasan sanda tace “Anas Magu ne!” Wani kallonta Baba yayi yana salati aransa, Babban Sojan yayi ihu yace “Soldiers!” Atare suka amsa “Yes Sir!” Cikin bacin rai yace “I don’t care idan zaku juya anguwan nan up side down kushiga house by house, afitomin da koma waye Anas Magu” Baba yawani fincike Safeerah yayi cikin gida da ita, makociyarsu nabiyosu tace “hauka kikayi Feerah? Ke kinsan wani rigima kika sa kanki kuwa dake da iyayenki, aiko wanda basuci nasaran konawa ba kika boye, ku zasu kona amadadin sa”? Fashewa da kuka Safeerah tayi brain dinta kwata kwata bai gayamata meta aikata ba sai yanzu kuma tsaf tasan yanzu bala’in nan kansu zai dawo kuwa, Baba yace “wai meke faruwa ne ma tukunna?” Makociyar su tabasa labari daga farko zuwa karshe hankalin Baba yatashi sabida yasan su waye mutanen nan, sukai charko charko a tsakar gida suna kallon Safeerah dake kuka ba kakkautawa, ana ahaka Mama tadawo wata yar dattijuwan mata da bazata wuce 40yrs ba tace “meya faru ne kaga yanda sojoji ke ma yaran unguwan nan kuwa awaje” tai maganan tana kallon Safeerah dake kuka, nan Baba yagaya mata komi itama tsoro yashiga jikinta duk sukai charko charko ana kallon Safeerah makociyar tace “uhmm Allah ya takaita fitinan nan, nidai gaskiya zaman unguwan nan yazo karshe bazan iyaba, Allah dawo da Malam, sai anjiman ku” tawuce tafita, Mama takalli Safeerah tace “ni banki boyesa dakikai ba, amman mesa zaki kira sunan Anas basaikice baki Sani ba, ke kina girma kinki wayau” Baba yace “dan Allah bita ahankali meta sani eh guda nawa take dakike expecting tayi abu kaman adult, zo taho Mamana” tasowa tayi tazo gefen Baba ta kankamesa tai zuru zuru sabida tasan tai laifi, ahakadai sukasa abincin dare, sai wajajen 10 nadare sojojin sukabar unguwan sun tafi da mutanen dasuka kama but not all still anbar few sojoji a unguwan, da kyar Safeerah tai bacci Mama ma haka Baba dai yakasa runtsawa dudda an tafi dasu yasan ways na yan unguwan nan.
Yana kwance a falo yaji an dirko gidan da sauri yamike yashige daki yataso Mama yaga yamata tawuce dakin Safeerah su rufe kofa tawuce tarufe kofan, Baba yaji ana dirkowa soyake yabasu hakuri yarsa tai kuskure amman yarinya ce, yafito yana kokarin kunna torchlight kafinma yayi magana suka shiga yimai duka baji ba gani Baba salati kawai yake, Mama tasaki Safeerah data rungume ajiki jin karan bugun da akema Baba tabude kofa tafito Safeerah tasa ihu na bala’in tana kuka dan tabiyo bayan Mama ganin dukan da akama Baba, suna ganin Safeerah daya yazabura yayo kanta yace “zonan dan durun Babanki” “Mamaaaaa” Safeerah tai ihu tana kankame Mama, Mama tace “kuwa Allah kuyakuri Safeerah sa’ar kanninku ce, yarinya ce tayi shirm….” Ture Mama yayi ya fizgo Safeerah Baba yatashi da duka karfinsa ya turesa ya maida Safeerah daki