NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 59 of 69

kasa Safeerah tayi batai magana ba, Layla tace “bazaki min tambayoyi kan mijin naki ba”? Sake sunnar da kanta kasa Safeerah tayi kunya takeji Layla tace “ai shikenan” ta gyara zama tace “kinga Yaya yanada kirki na bala’i amman bayason raini yanada fushi aka tabasa, sannan halinsa nada wuyan ganewa yanada wuyan ka karantasa amman he’s easy going wlh, he is into diet so yanason healthy meals, bayason soye soye ko oily abu, he love vegetables, fruits, da proteins, Allah yasa albarka a aurenku yakada fitina”…. Baffa yace “nine yayan mahaifinsa, due to some unforeseen reasons Allah bai bawa mahaifinsa daman zuwa ba, ga Aminina, mahaifin Babban amininsa Kabir, ga kaninsa Auwal, sai kanwarsa Layla, danmu yamin bayani sun riga sun daidaita zancen sadaki da Safeerah ko”? Baba yace “kwarai” Baffa yace “to za’a bamu aurenta yau ne ko akwai abinda kukeso ayi” Baba yace “adaura yanzu mun shirya” nan take aka daura auren Safeerah Shu’ibu da Salim İbrahim Maradi akan sadaki wannan gida aka shafa anata addu’a ana samusu albarka, wani boyayyen ijiyan zuciya Salim ya sauke da saida KB ya lura, he’s feeling kaman finally yabawa zuciyansa abinda yadade yana nema, yaji wani sanyi aransa, dawata natsuwa, da contentment” EPISODE 3️⃣1️⃣ Mama tai shiru like shikenan Safeerah tai aure, wannan aure ne da su sukamata ba wanda aka mataba a chan gidan ba, har kasan ranta takewa yarta addu’a Allah sa this aure should be the best for her. Sunci abubuwan da aka kawo har cupcake Safeerah tayi, Salim ne kawai baici abu sosai ba dan he is really overwhelmed so cikinsa yacika, sallan azahar sukayi anan falo akai jam’i sannan akai sallama za’a tafi, Mama tace “bari na kira Layla” wucewa Mama tayi sama tasami Layla adakin daketama Safeerah hira tana bata labarin duka yan gidansu tace “zaku tafi Layla” tashi tayi tace “tom Safeerah saimun sake haduwa ko” mikewa Safeerah tayi wlh kawai kunyan Layla takeji ta gyadamata kai tace “tom nagode sosai Anty agaida Meenal da kowa” hannunta Layla takama ahankali, hannun Safeerah taushi kaman na karaman yarinya tace “tom byeee” sannan tasaketa tawuce tafito suka sauka kasa tareda Mama, babu kowa a falon waje tafice sai chan tashigo tazo wajen Mama tabata wata yar jaka tace “gashi yace abawa matarsa” atare daga Mam har Layla sukai murmushi, karba Mama tayi tace “tom zan bata kuwa yanzu, agaida yara dakuma Mama Layla” Layla tace “zasuji Mama bye” tawuce tafita Mama takoma sama tasami Safeerah zaune kan gado yarinyar duk tai wani iri Mama ta ijiye jakan gefenta tace “mijinki yace akawo miki” ko kallon jakan batayi ba sai gyadama Mama kai kawai datayi ahankali Mama ta zauna gefenta ta kalleta tace “menene Safeerah?” Girgizama Mama kai tayi tace “bakomi Mama, kaina naji yanadan ciwo kawai” hannu Mama takai takamo kafadanta hakan yasa gently takai kanta tadaura kan kafadar Mama wani natsuwa taji saita sake gyara zama kawai ta kankame Mama, wani irin sassanyar kuka tasaki da batasan ma daga ina yazo ba, Mama tace “ke a aure na biyun ma still kuka zakiyi” cikin kuka tace “Mama bansan mutumin nan ba, bansan komi akansa ba, satin nan na sansa, satin nan na auresa, Mama wlh banason nakuma aure na tsani aure, maza basuda kirki, all abubuwan nan dayakeyi idan he is worst than Abbati fa Mama? Bansan komi kansa ba, zai yarda Waleed ya zauna gidan? Idan ya yarda yanzu daga baya yace yaron yabar gidansa fa? Mama rike d’a wanda bakai ka haifesa ba is not easy all this dayake yi da Waleed maybe kawai dan ya aureni ne danni bantaba ganin wanda yaso yaron dabashi ya haifa ba, ga Momma nan dudda yayar mahaifina ce amman bata kaunata sabida ba ita ta tahaifeni ba, ita kenan yar uwanmu na jini balle wani, Mama yara irinsu Waleed nada gundura, Waleed is selective wajen cin abinci kina ganin zai jure nonsense dinnan, Mama yafara dukansafa? Yafara kyaransa fa? Mama bazan iya jure any form of cutarwa ko takura ma Waleed ba, babu abinda bana tunani yau dinnan, kawai I’m scared ne” tafashe da kuka sosai Mama na shafa bayanta tai murmushi tace “kodan abinda kika mana Safeerah bazaki taba tabewa ba, i know badan kanki kika yarda da auren nan ba saidan mu, banda haka Salim seems like a good person, yanada hankali, gashi yanada natsuwa, wlh hakanan inaji ajikina bazai taba cutar da Waleed ba, idanma yayi muna raye fa zaki maido mana dashi daman ba kowa ke iya rike danda banasa ba” rushewa da kuka tayi tace “Mama ni wlh duk auren dazanyi da Waleed bazai zauna dani ba saidai auren yamutu, ni bazan rabu da Waleed ba” kawai tasama Mama kuka Mama tadanyi dariya ta jijigata tace “toh mara kunya naji mai d’a zan tayaki da addu’a, Allah ya sanya albarka a auren nan, yabaku zaman lpy kinji, Allah bazai wulakanta ki ba Feerah, share fuskanki kibude abinda yakawo miki” gyadama Mama kai tayi tadago takai hannu tana goge fuskanta tass sannan tadauki jakan tabude ahankali waya tafara cirowa iphone 16 pink, saikum
🏠