NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 56 of 69

karfi sosai yasaka sa abayan mota Safeerah da fitowansu kenan tareda Mama tadan saci kallonsa he’s so gently da mahaifinta, Mama ma tabisa da kallo sai tadan sauke ijiyan zuciya wlh she loves Salim for yarta sosai, karasawa wajen sukayi itama ta shiga baya, adan kunyace Safeerah tashiga gaba, shima yashiga Waleed na jikinsa ya kunna motan yaja har zuwa estate din Baba da Mama nata kallon ikon Allah sabida basu dauka a irin waje haka yabawa Safeerah gidaba, wlh estate din yafi GRA su Momma kyau sau dari, ga gidajen iri daya sak, saima dayayi parking gaban wani hadadden gida ga flowers anyi decorating wani mini garden, ga bike na yara da ball yasa awajen wanda she is sure bata gani the other day ba, yanzu wannan hamshakin gidan Safeerah ta karba jama’a? Kashe motan yayi yabude yafito yazagayo ta bangaren Baba yabude masa kofa, fitowa Baba yayi Mama ma haka, itama Safeerah jikinta yadan mata wani iri amman tadaure tabude motan tafito taciro key dake yar jakan hannunta ganin ko kallonta Salim bayayi wasa yake da Waleed abinsa yasa tai wajen kofa su Baba na kallonta tabude tajuyo ta kallesu saikuma takasa magana, Salim yace “mushiga ciki Abba” shiga Baba da Mama sukayi duk suna kallon gidan this is the moment of disbelief awajen gidan nan nasune yanzu? Su? Suka zauna afalon dayake a gyare, Salim yasauke Waleed yace “remember don’t cry zanje office okay” gyadamai Waleed yayi, gently yace “je Ummi tasa maka cartoon” dan satan kallonsa Safeerah tayi jin abinda yafadi yamike tsaye yace “sai anjiman ku Abba” har yayi kofa Baba yace “Salim” dasauri Salim yajuyo yace “na’am Baba” ahankali Baba yace “gobe kazo da magabatanka adaura muku aure ba amfanin bata wani lokaci tunda nasami lpy” faduwa gaban Safeerah yayi sosai jin abinda Baba yafada, Salim yadan gyadamai kai yace “toh Abba”. EPISODE 2️⃣9️⃣ Wani haske kalaman Baba sukasa yaji aransa, deep down yanaji kaman yawani fizgo gobe tayi, he just wanna hear those golden words an daure tsakanin Salim Ibrahim Maradi da Safeerah Shu’ibu, rabonsa da gidansu yau kwana nawa dayana France ko sau daya Ammi bata kirasa ba maybe Dady yafada mata, sai kawai yawuce gidansu, parking yayi yafito flat nasa yawuce shower yafada tun yana ciki yaji wayansa na kuka karasa wanka yayi yafito jin wayan na kuka again yasa yatafi wajen wayan, ganin Ammi ke kiransa yasa yadaga wayan muryanta ba dadi kwata kwata tace “kazo ina dakina” bata jira amsawan sa ba ta katse wayan, ijiye wayan yayi shima yacigaba da shiryawa, wani 3quater yasaka wando yasaka, yasa t-shirt mai dogon hannu, slippers yasa sai kamshi yake yafito, flat nasu yashiga yaga Lubna da Ameera a falo suna tattare souvenirs dasuka hada na bikinsa dasauri sukace “sannu da zuwa Yaya” wucewa yayi bai amsasu ya gyadamusu kai ganin abubuwan dasuke hadawa yasa yatuna da auren da za’amai yawuce dakin Ammi yayi sallama yabude dakin Ammi ya shiga, Auwal yagani aciki da Layla kanwarsa datai aure yarta daya Meenal, Ammi yagani tahade rai sosai tana kallonsa, Layla tamike da murmushi sosai kan fuskanta tace “Yayaaa yau kwana na biyu ina gida banganka ba wayanka baya shiga” hancinta yaja yayi murmushi yace “i was in France” Auwal yace “ya hanya Yaya”? Anatse yace “Alhamdulillah” yana tahowa cikin dakin rike da Layla data basa side hug yasami waje yazauna yakalli Ammi yace “ina yini Ammi” Ammi bata amsasa ba sabida yanda ranta yake abace tace “kullum rannan duniya complain na mahaifinka is baka girmamasa, bakada respect menene menene, I see complain nasa baseless kawai yacika korafi ne but slowly na soma yarda da maganar sa yanzu” tai shiru, cikin tsantsan bacinrai tace “me nakeji haka daga bakin Dadynku Salim?” Dan lumshe idanu yayi yabudesu yace “me yaran nan keyi anan Ammi”? Yayi maganan yana musu wani kallo hakan yasa duk suka tashi zasu fita Ammi tace “nina kirasu kudawo nan cus enough is enough” tsayawa duk sukayi Auwal yazauna kan hannun kujeran da Salim ke zaune kai din, Layla tazauna gefensa ahankali, Ammi tace “wat kind of embarrassment is this Salim? Few days to your wedding, gobe zasu fara events one week to wedding, Bazawara zaka auro ana zaune lafiya harda d’a fa?” Sauke kansa yayi kasa, Ammi tace “I’m talking to you kamin banza menakeji me hadinka dawata bazawara datazo IT company? Because she saved you and so?” Da dan zafi kan muryansa yace “wat if sonta nake Ammi? Wat if all this years I’ve fallen for her tun sanda ta taimakamin I’ve beeen searching for her? Dan naganta yanzu ta taba aure tanada yaro does that change anything Ammi? I am a Man yaushe karin aure yazama wani laifi ko wani abu? What am I doing wrong Ammi”? Cikin fushi Ammi tace “everything you are doing is wrong Salim, mahaifinka daya hada auren nan zaka kunyata? And yes it does matter sabida you are too small ka auri bazawara not to even mention ta taba haihuwa bayan ga budurwa wacce bata taba aure ba ce zaka aura” dan runtse ido yayi he hat
🏠