NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 55 of 69

ana da manyan idanunta ko kyaftawa batayi amman shi bata iya kallonsa haka kawai yaji bazai iya daurewa ba cike da izza yashiga tafiya one one kaman daga sama suka gansa awajen gaban Safeerah ya tsaya yama mutumin wani mugun kallo yace “lafiya!” Wlh ayanda muryansa yafito ba mutumin kadai ba har ita Safeerah saida gabanta yafadi gashi yamata wani babba agabanta sosai, adan daburce mutumin yace “tambaya nakeyi daman kan war……” “meya sami securities dinchan dabaka tambayesu ba kana tambayan matan aure!” Dasauri mutumin yace “ayakuri yallabai, ayakuri Oga” yajuya da sauri yawuce daidai Waleed nawani irin dirlowa daga hannun Mamansa yakama hannunsa yace “ayoyooooo” juyowa yayi yakalli Waleed dakawai ganinsa yasa yaji bacinran yabace dan karamin smile yasaki yace “Hello Finest boy Waleed, come here” yawani daukesa ya rungume yana kallon Safeerah daharta sauke kanta kasa, murya ciki ciki tace “ina yini” bata jira amsar sa ba tawuce dasauri ta tafi ta shiga ward din binta yayi da kallo she still walk kaman da. 7 aka fito da Baba an saka bandage a fuskansa. Yana asibitin har isha’i awajensa Waleed yayi bacci sannan yadawo dashi yamusu sallama yatafi koda Mama tace taje tamasa sallama fitowa tayi but taki zuwa chan tadawo daki, kallonta Mama tayi tace “zo Feerah” zuwa tayi ta zauna gefen Mama, hannunta Mama ta kama tace “Salim yagaya miki waye shi?” Girgizama Mama kai tayi alamun a’a, ahankali Mama tace “dazu kina masallaci Babanki ya tambayesa mesa yake taimakon mu, shine yake gayamana shine mutumin da kika taimaka kika boye lokacin nan!” Tunda Mama tafara maganan kirjin Safeerah ke bugawa none stop, Mama tace “yanuna ma ni da Babanki hannunsa gabaki daya hannun tabon kunane haryau bai dawo daidai ba” wani irin kallon Mama Safeerah take, murmushi Mama tayi takai hannunta ta kama fuskan Safeerah tace “yace yanemeki sama da kasa bai ganki ba not until rannan dakikazo company sa aiki” Mama tai shiru tace “ni da mahaifinki mun aminta da auren mun yarda, and mun yanke shawaran zamu shiga gidan tunda sadakin ki ne, da kyautane da munji wani iri, ga idanun Babanki anyi aiki yana warkewa zai nemi koyarwa we will live good babu wanda zai kara zaginmu, abinda nakeso dake yanzu is kidage da addu’a, Allah yasa Albarka a auren, Salim ba yaro bane abinda yasa muka karajin natsuwa dashi kenan, thank you Safeerah for saving us” Mama tayi rungumeta kankame Mama tayi tunani sunmata yawa aka daman shine mutumin nan? Saisa yadinga kallonta the first day daya ganta in his company, daman shine? But yanzu yafi girma. ** Yau kwanan Baba five a hospital din Alhamdulillah yaji sauki ras idanun dazu aka bude da safe yana gani ras saidai sun kankance but Alhamdulillah, tun after rannan operation din Salim baizo ba sabida wani work trip daya tafi to France na just 3days but kullum yana aiko sojoji akawo musu daily need, yasayama Safeerah 5abayas yabada akaimata saida Mama tai da gaske sannan tasaka kayansa. Yau aka sallami su but Dr Isa yace Salim yace ajirasa zaizo yakaisu gida duk suna zaune, Safeerah tasaka daya daga cikin abayan daya sayamata black yanada stones yamata kyau ajiki sosai dankwalin abayan ta yafa, Waleed short ne ajikinsa na jean dawani blue riga mai kyau da takalmi yayi kyau sai wasansa yake a tsakar dakin sun hada komi nasu tsaf, suna zaune akai knocking tareda sallama hakanan gaban Safeerah yafadi jin muryansa dasauri ta gyara gyalen kanta da kyau tana rufe gashinta, Mama tabudemai Waleed na ganinsa ya jefar da Cheese na hannunsa yadaga hannu yazo dagudu yace “ayoyooooo” daukan Waleed yayi dasauri yayi murmushi kadan yace “Finest Boy Waleed” kankamesa Waleed yayi Mama tace “ai sai ka barsa ko hannunka duk cheese zaka bata masa kaya” dasauri yace “Mama barsa bakomi” yashigo dakin batare daya kalli Safeerah da kanta ke kasa ba yayi wajen Baba yana mika masa hannu cikeda respect yace “Abba ina yini, idanu sunyi kyau” Dan dariya Baba yayi yana feeling very free with Salim yace “ai saiyau nake ganin ka da kyau, Salim kam Masha Allah” dan sunnar da kansa kasa yayi maganan Baba tasa yadanji kunya kadan yace “bari nasa akai kayan mota sai mu tafi” yajuya yakalli kofa yace “come in Boys” sojoji guda biyu suka shigo suna daukan yan kayansu Mama tazo inda Safeerah take zaune kan kujera, duka ta dakamata a sace Safeerah ta kalleta da sauri, wani harara ta mata irin bata iya gaisuwa ba, adan hankali Safeerah tace “ina yini” batare data kalleshi ba, shima bai kalleta ba yace “lafiya lau” yace “Abba Bismillah muje” Baba yace “asibiti ba dadi jama’a” yasauka ahankali yake tafiya Salim dake rike da Waleed na je rawa dashi suka fito, Mama ta kalleta tace “ke da bakin hali baki iya gaisuwa ba ko” kaman zatai kuka tace “Mama magana fa yakeyi saisa ban iya nai gaisuwan ba fa” Mama tace “muje mai kunnen kashi” murmushi tayi suka fito itada Mama. Sunakai wajen motan ijiye Waleed yayi akasa shiya rike Baba cus baida
🏠