ba yardanka ko amincewan ka nake nema ba Salim! Khadija is my choice diyar aminini na and dole ka aureta, moreover kai ka kalli wannan zuciyan taka dake cike da wickedness da rashin da’a nada space na soyayya ko san mutum? Of course I know bakason Nana Khadija sabida mutum like you is not capable of loving anyone a riga an cire emotion dinnan a filin yaki!” Baki Salim yabude zaiyi magana Dad yacemai “get out before I loose my temper dan zan sabamaka sosai” wucewa Salim yayi wajen kofa haryasa hannu zai bude kofan ya tsaya yajuyo yakalli Dady calmly yace “Dady I know kai mahaifina ne saisa natako zuwa nan na sauke hakki nabaka hakkin ka, I am an adult that can make decision about my life, I don’t need you kamin aure zan iyayi dakaina, I am simply here dan na sanar dakai zan auri Safeerah and make her my wife today!” Yana maganan yajuya yabude kofan yafice Baffan sa yagani agaban office din ya tsare Salim da idanu murya ciki ciki dan ransa Salim yace “ina yini Baffa” yawuce abinsa bai jira amsan sa ba yasauka kasa yakai wajen parking yana kokarin bude motansa akace Salim, juyowa yayi Baffan sa yagani hakan yasa ya tsaya Baffa yazo wajen yace “Salim mesa zakama mahaifinka wannan furucin? Wani aure kake shirin yi bayan ana shirin bikinka Salim”? Ahankali yace “Baffa ni yaro ne? Bashi zai ciyarmin da matar dazan aura ba, he think sabida yahani zan hanu, idan bazaku nemanmin auren ba zan nemi wasu sujemin, i am tired of the way Dady ke treating dina kaman ba shi yahaifeni ba, he was never there for any decision nawa daman, why did i even come here today thinking zai yarda? Baffa stay out of this sai ajjima” yabude motansa yashiga yaja abinsa yatafi, juyawa Baffa yayi yakoma office na Dad yashiga har lokacin yana tsaye yana huci yace “Yaya kaji maganan banzan da Salim yake gayamin? Is because ka lallabani that year na hakura ban kira an koresa daga camp na soja ba, look at what this boy becomes today eh” Baffa baice komiba yawuce fridge na office din yabude yaciro ruwa ya tsayaya a glasscup yazo yamikamai yace “sha” karba yayi yakai baki ya kurba ya ijiye cup din Baffa yace “zauna to muyi magana Aliyu” zama Daddy yayi ahankali yadan sauke ijiyan zuciya, Baffa yace “kadaisan yanda nake yabanka in terms of sauraron yara da biya musu bukatunsu ko” runtse idanu yayi yace “nasani amman abinda Salim yazo dashi ba me yuwa bane Yaya kagane, bikinsa saura kwana goma yazo dawata magana kumama bazawara zai aura haba” Baffa yace “to menene a bazawaran eh?” Dasauri Dady ya kallesa hannu Baffa yadagamai alamun ya isa yace “calm down kawai kaduba zancen, auren nan kaika hada dakazo mai da maganan baice a’a ba, yanzu yazo maka da tasa saika yarda kaima me aciki he’s matured enough to hold both of them, kadena treating Salim kaman wani yaro” wani kallo yama Baffa yace “yanzu anma yar karaman Nana adalci?” Baffa yace “shi fa namiji mijin mata hudu ne kowa yasani sabida baka yiba doesn’t mean is wrong, bagani da mata biyu ba” Dady yace “ai kaga har yau bana shiri da amaryar ka Uwargida ce tamu” murmushi Baffa yayi yace “dan Allah ka saurari yaron nan stop trying to control Salim the more kanayi the more yana kufce maka” sosai yakalli Baffa yace “ba’a haifi yaron dabazan controlling ba, mubar maganan cus I will never ever support auren nan wlh kuwa”.
EPISODE 2️⃣7️⃣
5 na yamma za’a shiga aikinsa around 4 yashigo hospital din yau tukasa ake aka budemai baya yafito yana sanye da kayan sojoji, wucewa cikin hospital din yayi zuwa dakin yayi knocking tareda Sallama Mama tabudemai tace “Salim shigo” shigowa yayi yakallesu yace “ina yinin ku, ya karfin jiki Baba” atare sukace da sauki, kujera Baba ya nuna masa yace “zauna Salim” zama yayi ahankali yana tunanin ina Safeerah da Waleed basa dakin, dan shiru Baba yayi chan yace “mesa kake taimakon Safeerah Salim? Mahaifiyarta ta sanar dani komi hartakardun filayen an nunamin, in everything this is the only question nakeda shi, na ganka naga mutum mai amana da fadin gaskiya, aiki za’a shiga dani bansan ko zan fito da raina ko akasin haka ba, Salim ka gayamin mesa kake taimakon Safeerah”? Shiru Salim yayi kaman yana tunani sai chan yakai hannunsa na dama yadaura akan hannunsa na haggu ya yacire bitirin hannun rigansa yaja hannun rigansa sama gabaki daya har zuwa muscles dinsa da ananne rigan taki matsawa sama, hannunsa na haggu a kone fatan takoma mai tabo gabaki daya dinnan Mama tace “Subhanallahi kataba yin hatsari ne tabon kuna nake gani haka gabaki dayan hannunka? Meya sameka haka?” Dago kansa yayi yakalli both Mama da Baba ahankali yace “shekaru biyar da suka wuce abin yafaru” sai yayi shiru yace “lokacin ina mata kin lieutenant a soja nazo kano wani aiki ina gudu a titi wani yaro kawia ya shigomin da gangan bayan na kaisa asibiti yace na kaisa gida ina shigowa layin naga kawai an taru akaina an kaini wajen taya aka kulleni” yayi shiru yadan lumshe idanu kaman he