yayi bayan yacire jacket na suit nasa yayi hanging ya zauna yace “yesss to wat do I owe this visit yau babban soja Salim yazo office dina, uhnnn remind me of that your tittle ko matsayi” yayi maganan yana kallon Salim yana daura yatsansa kan lips nasa kaman mai tunani yace “i remember Major! Barka da zuwa Major Salim!” Kansa ya sauke kasa baisan mesa Dady is like this with him ba more like bullying but baiso yakira abin bullying, Dady hates yazama soja with passion so all this years he uses it to make him feel bad, ahankali yakai hannunsa yadan sosa kai Dady sa dan boko ne sosai, gasa dan gayu baya tsufa, yanda yake lurada kansa har mamaki yake bama mutane, calmly Salim yace “good morning Dad” batare da Dad ya amsa ba yace “mekazo nema wajena? Meya kawoka my company, kana garin nan amman saikaga dama kake zuwa gida ka kwana, tunda kadawo daga China I saw you once, skip the formalities I know ba gaisuwa yakawoka nan ba, what is it Muhammad Salim?” Yanda Dady ke kallonsa ido cikin ido haka shima Salim ke kallonsa cikin wata yar murya that is straight and directyace “Dady I’ve seen that girl” Babansa na kallonsa kur bayako kyaftawa yace “the one that saved you five years back sanda aikin sojanku yakusan hallakaka”? Hada lips nasa yayi ya gyadamai kai yayi yace “eh Dady she comes to my construction company for IT this week anan na ganta” Dady yace “okay nice run her a check, idan baka da kudi I can tell my accountant yayi running check din”dan shiru yayi yasauke kansa kasa, Daddy yakara natsuwa sosai yana kallonsa yana nazarinsa. “I’m not here for check Dad” ahankali Daddy yace “Salim” dago kansa Salim yayi ya kallesa, Dady yace “then what are you here you indai ba check ba?” Ijiyan zuciya ya fuzar cikeda dakewa yace “she’s going through alot Dady all because of me, har aure aka mata 6month mijin yasaketa, she has a son yanzu” cikeda rashin kulawa da nuna baiga wani abuba or important na story ba yace “and? I just said run her a check, sponsor the boy to school idan kanaso unless there’s more, but money can solve any problem datake ciki” sauke kansa kasa yayi yayi shiru na kusan 1min kafin anatse yadago kansa yakalli mahaifinsa da kyau yace “inaso na aureta Dady!” Yanda maganan tasauka akan Dady baisan sanda yamike tsaye yabuga table na gabansa sosai yace “wat nonsense!”gently Salim ke kallon mahaifinsa, hade fuska Dad yayi dan ransa yayi masifan baci yace “just 12 ne ko 11days to aurenka kazo kanamin maganan zaka auri wata chan da bansan daga ina take ba, sabida wannan aikin sojan ya maida mana da yara marasa tsoro ko shakkan iyayensu, an kekashe muku zuciya you feel zaka iya tarana da kowace kalan banzan zance, look at what becoming a soldier ya maidaka!” Daddy ya nunasa da hannu yace “look at you Salim very heartless emotionless wicked man!” Dan sauke kansa kasa Salim yayi baice komiba, Dady yacigaba da banbanmi. “Za’a fara shagulgulan bikinka nan da 3days is something wrong with you Salim koko yarinyar tamaka asiri ne”? Yakalli Salim yana jiran amsa amman baice komiba, Dady yace “are you that heartless ka kasa tunani how Nana Khadija will feel few days to bikinku mijinta na zuwa da maganan zai auri wata? You know me very very well I don’t believe in polygamy ban yarda da aure dayawa ba, babu abinda yakai mace daya zaman lafiya da kwanciyan hankali, yaranka su taso kansu ahade, can’t you see mahaifiyarka? She’s always happy sabida batada competitors, she’s fulfilled and satisfied, I make sure na sama maka auren one of the best, my childhood friend Haruna, Yar Niger ya aura, buzuwan yarinya that is very educated she’s just 25 ana maganan bikinku kana kawomin wani maganan banza da wofi, well listen to me, I’m not in support of this, babu abinda kakeso aduniya da ban makaba, kayi degree harda MBA kazo kasameni kanason soja, nahanaka bakaji ba zan iya using other means to stop you from becoming a soldier but ban hanaka ba I let you have your way regardless, kasameni kanaso ka bude companyn ka, al’adan tundaga my grandfather yara works a company iyayensu kai kace no kafi karfi kayi aiki awajena fine ban hanaka ba kabude, ko kana Nigeria baka cika zama gida ba sai barrack ban hanaka ba, you are 39 all this years ban dameka dakai aure ba dudda mates naka sunyi sai yanzu ka kawomin maganan banza da wofi! Ban yarda ba at all nagayamaka” baki Salim yabude zaiyi magana Dady yanunamai hannu yace “quiet! I don’t wanna hear a word, and I will consider nida kai bamu taba magana on this topic ba kajini stand up and get out of my office!” Ko motsi Salim baiyiba yakalli Dady sosai dake kallonsa, Dady yace “ohh bazaka fitaba! Nayi kadan na kora Nigerian Army Major out of my office ko”? Ahankali Salim yamike yajuya yafara tafiya Daddy yace “nonsense!” Chak ya tsaya saiya juyo yakalli Babansa yace “Dad kataba tambayana for once ko inason Nanah Khadija? Koko na amince da aurenta?” Cikin fushi Daddy yace “sabida