NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 49 of 69

amata sai lips dinta yahau rawa Mama ta tsareta da idanu ahankali tace “cewa yayi wai bayan an sallamemu mu koma gidansa daya kaini nida Waleed jiya dukanmu muyi zaman mu wai yabani gidan shine nacemai a’a banso” tai shiru Mama dake kallonta tace “sai yace mene?” Kallon Mama tayi batasan mesa gabanta ke faduwa ba murya chan kasa tace “yace tunda inada girman kai bazan amshi kyautansa ba wai zai aureki yabani gidan a matsayin sadaki yabani zuwa dare nayi tunani” Mama na kallonta tace “wani shawara kika yanke Safeerah?” Dasauri takalli Mama tace “Mama mesa kike min tambaya haka?” Mama na kallonta tace “aure nabiyu ne wannan kinada yancin zaban miji dakanki” bata fuska tayi tace “Mama ni bazan kara aure ba harna mutu zanyi tunani nasan inda zamuje idan an sallami Baba” Mama tadade tana kallonta sai bata kara cewa komiba. EPISODE 2️⃣4️⃣ Waleed shima bacci yayi dan yayi ciye ciyen nan Mama ta kwantar dashi kan lafiyayyen couch na dakin. Motsi Baba yayi hakan yasa daga Safeerah har Mama suka taso da sauri Safeerah tai wajen muryanta yayi rauni sosai tace “Baba Baba kanajina gani nan” bude idanunsa Baba yayi ahankali yadan gani dishi dishi but he was able to know Safeerah ce murya chan kasa yace “Mamana kin dawo? Ina Waleed?” Fashewa da kuka Safeerah tayi kawai ta rungume Baba sosai tace “Baba kayakuri dan Allah, Baba baran karaba kayakuri I’m sorry kaji Baba, sabida nine rashin lafiyanka yatashi ko, baram kara tadamaka da hankaliba kaji Baba” hannunsa yadaga ahankali taredayin murmushi dan gaskiya yasami sauki yace “ai kaganta ga kiriniya ga iya kuwa, Feerah rigima, ya isa toh bar kukan haka” ya shafa bayanta Mama ta tsaya tana kallonsu kai Baba na son Safeerah bana wasaba to ko don ita kadaice yarsa oho amman baya wasa da Safeerah dagosa Safeerah tayi tana dago gadon ya zauna tace “meke maka ciwo yanzu Baba?” Girgiza kai yayi yace “ba abinda ke min ciwo Alhamdulillah inama dan gani baga Waleed chan ga kujera ba” yanuna Waleed dake bacci, Mama ya kalla yace “waya kawoni asibiti”? Yayi tambayan sabida yasan ba Mama Kubra bace wannan dake fushi dasu ahankali tace “Salim ne yakawo ka” shiru Baba yayi yana tunani yatuna sanda yazo yana masa maganan Safeerah daidai nan Dr Isa yazo Baba yaduba tsaf sannan yayi murmushi yace “bansan ko Major Salim ya gayamuku ba, inhar kanaso zaka bamu yardan ka muna kyautata zato zamu iya maka aiki a idanunka da sababbin technology mu dasuka shigo tsaf zaka iya gani, Major Salim yariga yabiya kudin aikin consent naka kawai mukeso dazaran BP ka yasauka sai ayi fixing time ashiga surgery Baba” tunda Dr Isa yafara magana kowa na dakin kallonsa yake especially Safeerah da kirjinta yahau bugawa batada burin da ganin Baba ya dawo, wayan nan idanuwan sune suka tankwafar da Baba yakasa samin sana’a muguwar yayarsa na yanda taga dama dashi, Baba yaje school yayi FCE he’s such a good teacher idanunsa suka dawo he can look for teaching job again har ranta taji dadi, Baba yadan kalli Mama sabida shi kudin ne aransa sai cin kudin Ogan yarsa suke but saiyaga Mama ta gyadamasa kai hakan yasa yace “to likita kunada consent dina a ina zanyi signing?” Wata takarda yasan karba daga hannun nurse ya matso yasa a hannun Baba yasamasa biro Baba yayi signing, Dr Isa ya karba yace “I will monitor you zuwa gobe idan BP ka yazama stable za’asa lokaci na aikin” gyadamai kai yayi yace “an gode likita, Allah saka da alkhairi” juyawa yayi yafice, Mama takalli Safeerah tace “kinyi salla wai ke yarinyar nan” girgizama Mama kai tayi, Mama tace “tashi kitafi masallaci kiyi salla” tashi tayi ba musu tawuce tabude kofa tafita ta rufo zata wuce saitaki ta tsaya dan yanda Mama ta korata when she can simply pray adaki is somehow kunnenta tasa jikin kofan muryan Mama taji cikeda damuwa tace “Yayarka nata kiran wayanka Malam nasaka wayan silent banso yarka maraji tagane, sakon ta ya shigo ta aiko maka da sako a message” wayan Baba ya kalla cikeda damuwa yace “mita fada a sakon?” Shiru Safeerah taji Mama tayi sai chan tace “waya baka izinin shigomin dawani kato gida? Gidanka ne ko gidan ubanka ne? Gidana ake shigomin da wasu batare da izinina ba to bari kaji zumunci yaci uwarsa da ubansa tunda baku da godiyan Allah dakai da matarka kuma ku kama sahu kubi yarku ko kofar gidana kada ka kara zuwa inba hakaba saina maka wulakanci wanda harka mutu bazaka mantaba munafuki shashasha” Mama ta sauke ijiyan zuciya ta kalli Baba tace “yanzu ina zamu Malam? Ta ina zamu fara gamu da y’a, gamu da jika? Kano zamu koma da ake nemanmu akashe? Inamu ina zaman Abuja? Ko an maka aikin ma a ido kafin kasami aiki it takes time a zamanin nan damuke, bazan maka karyaba nadamu Malam” murmushi Baba yayi saiya rungumo Mama yanada danne damuwa yace “kidena damuwa ni nasan Allah bazai barmu ahaka ba, ya isa dan Allah karki kuka yarinyar nan tazo ta gane” wani kalan nauyi Safeerah taji zuciyanta yamata sai kawai ta tashi
🏠