cikin murya yar kankanuwa tace “ni…..ni…..dai ka banni natafi nariga na rantse baram koma gidan ba!” Tsareta yayi da idanu yayi shiru hakan yasa tadago kanta jin shiru wlh ayanda taga idanunsa batasan sanda tajuya zata bude kofan kitchen dasauri tafada ba strictly yace “don’t try that!”
Kasawa tayi ta tsaya jikinta na rawa, lumshe idanu yayi yadan sassauta muryansa yace “bazanso this poor innocent boy suffer sabida foolish and childish decision naki ba, you can stay here as long as you want, bring parents naki su zauna tareda ku nabar miki this house! I will give you the papers anjima! The house is yours!” Dawani irin sauri Safeerah tajuyo gabanta na faduwa so take ta kalleshi but takasa dan lankwasa kanta tayi ahankali tace “thank you amman ni bazan karbi gidanka ba!” Tsayawa yayi yana kallonta shima babu wani wasa ko tausasa murya yace “idan ego dinki bazai barki ki amshi gidan nan dana baki ba how about nabaki gidan ta dalilin aure!”Dummm! Dummm! Dummm! Gaban Safeerah yawani irin fadi this time around saida ta dago idanunta ta kallesa shima kallonta yake fuskansa babu alamun wasa kowani kwana kwana kai tsaye yace “marry me Safeerah!” Sarawa kanta yayi da bugawa all at the same time batasan sanda ta lumshe idanu ba, is this man okay ko daman ance sojoji nada mental problems ko cus mema yakawo maganan aure? For someone that she just looked yanzu bataga wani sign ko alamu na yana sonta ba ko yakamu da sonta but he is proposing marriage auren mene? Mezatayi da aure? Ita da babu abinda ta tsana kaman aure she promised kanta bazata kara wani aure ba har abada aure daga ina kuma? Juyawa tayi zata bude kitchen tashiga yace “don’t get me wrong! Ba auren ki zanyi ba because ina sonki, or I need wani abu from you or anything nope! On the contrary bakida wani abu dazaisa namaji sha’awan aurenki, I don’t do small foolish girls!” Yayi dan shiru kafin ahankali yace “I told you earlier as a mother you don’t own your life, rayuwanki belongs to children naki, the moment ka haihu you have to give your all for yaranka, hakkine akanki to protect your children, you need to be strong for them, kajure komi for them, this is the same thing your parents did for you, I spoke to iyayenki, I just left d hospital Mahaifinki na asibiti” dawani irin sauri Safeerah tajuyo jikinta na rawa tama kasa magana sai hawaye, calmly yace “he is stable for now, mahaifinki was saying he is ready to support you shima bazai kara komawa gidan ba kuje wherever you lead them to, ina zakikai mahaifinki dakeda serious BP kuje kuna bara? Ina zaki kai small little Waleed? How will you manage ki rikesu? Are you trying to jefa kanki a halaka? Idan karban gidan nan dana baki for free hurts your ego so much then ki karbi gidan a matsayin sadaki and marry me that way ba kyauta bane and it’s yours kinada right akansa kisa Abba da Mama anan, ke da Waleed i will take responsibility naku, you have from yanzu zuwa dare to give me an answer, let’s go to the hospital” kawai yajuya yasa hannu yadauki Waleed yawuce yabude kofa yafice Safeera ta kankare a wajen kanta kaman zai fashe maganganun sa were to heavy for her to chew ta fahimta kuma.
EPISODE 2️⃣3️⃣
Kusan 7mins yana zaune a mota shida Waleed yanama yaron wasa Waleed sai wannan hausan da yar turenci kadan dayakeji yake masa yana amsasa gogar bata fitoba, kofa yaji an bude hakan yasa yadago kansa dayake tinted ne glass na motan tsareta da idanu yayi bakinta is still showing signs na kumbura, idanun nan sunci kuka sunyi suntum but she still looks very pretty, zanin goyon Waleed ne kawai a hannunta, ganin key jikin kofan ta gaba yasa ta murza ta zare, bakinsa ne yayi motsi yana kallonta yace “stubborn girl!” Zagayowa tayi tabude motan Waleed yayi wani ihu akan jikinsa yana murna yace “Ummyy kalle” yajuya sitarin mota ta dauke kai batare data kulasa ba tamaida kofan tarufe, reverse yayi abinsa baice mata ci kanki ba Waleed sai murna yake yana tayasa tuki, saida suka shiga major road yasa hannu daya ya rungumesa gently ajikinsa yace “be good okay” gyadamai kai Waleed yayi yay lamoo ajikinsa, suna shiga asibitin Safeerah tashiga bin ko’ina da kallo idanunta suka ciko da hawaye sosai, parking yayi yabude motan yafito ko’ina a hospital din sojojine yana fitowa few sojas dake wajen suka kame suna saramai, da hannu yamusu alamu su bace yahade fuska Waleed sai kallon sojoji yake da uniform ajikinsu, fitowa Safeerah tayi ahankali ta maida kofan tarufe hakan yasa yawuce rikeda Waleed, lurada bata biye dashi yasa ya tsaya yadan juyo ya kalleta hada ido sukayi kiris take jira tafashe da kuka tana kallonshi idanunta suka kara cika da kwalla, anatse yajuya yacigaba da tafiya hakan yasa da kyar tadaga kafafunta dasukai sanyi tacigaba da binsa harciki wani daki taga yayi knocking ya dakata aka budemai kofan Mama tafito tana ganin Waleed a hannunsa yayi kyau sosai sanye da tufafi masu kyan gaske tace “laaaa Waleed ayoyo taho” tamika hannu c