sauke kanta kasa, ahankali yace “okay” yanuna mata table din yace “have breakfast, take drugs that are here sai ku shirya, call me when you’re ready to go” gyadamai kai tayi ahankali tace “thank you” wucewa yayi wajen kofa yasa hannu yabude yafice saikuma yajuyo hada ido sukayi dasauri ta sauke kanta kasa, ahankali yace “zanje wajen Baba and talk to him you need to go back to your parents” da sauri ta sake kallonsa sai kawai tafashe da kuka sosai tana goge fuskanta da bayan hannu batare datai magana ba, ya tsaya jimmm yana kallonta kafin yasa hannu yazare key tabaya yajawo kofan yasa key cus ya lura gidansu ne batason komawa something is definitely going on, yanda yace zaije yaga Babanta karyazo kafin yadawo tagudu tabar nan what if tafada in the wrong hands ga yaro karami tareda ita, dasauri tai wajen window tana kuka taga yaja mota yabar wajen.
Rolex din hannunsa ya kalla is 11AM, he needs to help his helper whatever it takes, yarinyar that helped him a death row he will go to the end of the world just to see that smile in her face not cry or sorrows. Cikin 20min yakai kofar gidansu yakashe motan wuraren 11:30, babu kowa a kofar gidan yayi jim sai yafito a natse yazo wajen yakai hannunsa ahankali yayi knocking ya dakata shiru, sake knocking yayi na biyu ya tsaya shima shiru, yakai hannunsa yasake knocking akaro na uku, karan bude kofa yaji hakan yasa yadan koma baya kadan sai yaga an dan daga wani marfin lekowa yaga idanu hakan yasa yace “Assalamu Alaykum” ganin ba yan gidansu bane yasa anatse Mama da duk tayi wani iri tabude kofa tafito kallo daya Salim yamata yagane itane mahaifiyar Safeerah, Safeerah really looks like her but tanada haske Baba though Baba yafita haske, Mama kuma baka ce, saisa Safeerah is not black she’s caramel, anatse yadan duka cikeda kunya dakuma girmamawa yace “ina kwana” calmly Mama tace “lafiya lau wa kake nema?” Dagowa yayi yakalli Mama dake kallonsa ganin bata sansa ba calmly yace “Abba nake nema, Baban Safeerah!” Dasauri Mama takara kallonsa tana tunani dan unguwan nan ne? Tasan Baba na gaisawa da yan layin ko zaman dayake awaje saisa ma yake dan samin kudi sukan masa kyauta once in a while, ahankali tace “bayajin dadi ne yana kwance, waza’a gayamasa”? Dasauri Salim yace “meke damunsa Mama”? Kallonsa Mama tayi da kyau jin yanda yakirata Mama, hakan yasa Mama tace “wayekai bawan Allah?” Dan shiru yayi kafin ahankali yace “sunana Salim nine Ogan Safeerah a inda take aiki, jiya tazo company mu da daddare da signs na duka toh daman maganan nazo yima Abba kenan, zan iya dubasa Mama in yaso sai nayi maganan dake” sosai Mama ke kallonsa tanajin wani natsuwa dashi especially natsuwansa sannan ba yaro bane irin su Shamsu, babba ne kuma kamili wanda yasan kansa, ganin batai magana ba yasa ahankali yace “Abba yasanni mun hadu so daya” dan ijiyan zuciya Mama ta sauke, sannin Momma bata nan hakama Shamsu Salma ce kadai agidan kuma tasan tana bacci war haka yasa tace “shigo Bismillah” tajuya yabi bayanta a natse, ga mamakinsa dakin dake gefen gate na masu gadi yaga sunyi a babban gida haka da base on the little info he daya samu jiya this house na yayar Abba ne cus ance Shamsu yakawota yaron sister kenan, and mahaifin Shamsu is tsohon gwamnan Jigawa he’s late, why will her own blood brother be living a side na masu gadi?
Bude kofan Mama tayi tashiga ciki saiya tsaya agaban dakin, juyowa Mama tayi tace “shigo” ahankali ya shiga dan karamin falo ne ga yar katifa awajen dake a gyare tsaf ga ganamasgo da jakan school din Safeerah ke kai, ga gwangwnayen abincin Waleed a wajen sai few kayan wasan yara da ball, babu komi falon, dadduma Mama takawo ta shimfidamai ya zauna ahankali tace “bari nafito dashi” tawuce ciki taduka gaban Baba da baya gane wanda ke kansa idanunsa ganin ya bace gaba daya, ahankali tace “Malam Malam” motsi yayi yace “na’am Mamana na dawo? Waleed fa”? Shiru Mama tayi tun jiya kawai Safeerah yake tambaya ahankali tace “kayi bako sunansa Salim, yace ka sansa shine Ogan Safeerah, kampaninsu Safeerah taje jiya” dasauri ya yunkura zai tashi yakasa kamasa Mama tayi suka fito tazaunar dashi Baba yace “ina Safeerah Salim”? Ruwa Mama tasa a plate mai kyau pure water ta ijiye masa ta zauna gefen Baba, anatse Salim yace “ina kwana Abba” da kyar Abba yace “lpy lau ina Mamana Salim”? Shiru Salim yayi he’s feeling very sad seeing how sick Baba is yace “she is safe Abba, namaso nataho tareda ita nadawo da ita amman taki yarda, meya faru, waya daki Safeerah haka?” One thing about Salim is bayida tsoro ko kadan kokuma irin kunyan nan da jin nauyi bai iyaba unless idan bai damu da abuba shi ba yaro bane he is here for something and he will sure do that.
Kafin Baba ya bada amsa Mama tace “rashin kunya tayi da dambe” da dan sauri Baba yace “Salim kasan kowani family nada one or two issues haka, yar matsala aka samu jiya, one thing da Safeerah shine dan banzan zuciya ne da ita inha