na kallonta, tashi tayi har lokacin goge hawaye take yana kallonta tawuce tabude jakan school nata ta zazzage komi, tanada gauze, bandage, spirit, hydrogen da auduga, kwasowa tayi tazo wajen wardrobe din tace “kafito” ahankali yafito tanunamai kullin kayan wankinta dake wajen daure a zani zama yayi ahankali yana sauke ijiyan zuciya, tajuya tafita daga dakin tadauko zuma tadawo tazo dan nesa dashi takallesa da idanunta da sunyi ja sabida kukan datayi suka hada ido, hannunta tadaura a kirjinta tace “kagani farin uniform na nurses ne ajikina ko, ina zuwa makarantan Nurse ban kware ba, zanyi jamb nashiga asalin nursing a university abinda nakeso nazama kenan” tai wani murmushi daya bayyana dimples nata masu kyau da fararen hakoranta, takallesa tace “ban kware ba but na iya abubuwa kadan amman zaka bari nasamaka magani a haka?” Kallonta yayi na kusan 3secs sai murmushi takemasa hakoranta yan kanana kaman na children saiya dauke kai baice komiba, dasauri tace “dan Allah ina ganinka ahaka kuka kake sani” tai wani rau da fuska zata fashe da kuka kallonta yayi ganin hawaye yataru a idanun nata sai ya gyadamata kai kawai alamun eh, da sauri tabude spirit da auduga ta dangwala ta dan taho dab dashi but saitaji gabanta na fadi takasa komi sai wani firrr take da idanu yakalleta ganin takasa kana gani kasan bata tabayiba, ijiyan zuciya ya fuzar ahankali yace “do it” yanuna mata gefen goshinsa dake jini, gyadamai kai tayi ta kai hannunta dake rawa ta goge ciwon goshin ya runtse idanu da sauri sauri ta tsaya tace “dazafi ko sannu” saita matso dab dashi tacigaba da goge blood din tana kallon black face nasa daya runtse idanu yanda yabata tausayi yasa kawai saita huramai iskan bakinta a goshin wani irin bude idanu yayi yajuyo yace “wat are you doing?” Kasa magana tayi tai fiki fiki da idanu yace “ki barshi banso” dasauri tace “yakuri baram karaba wlh tausayi kabani naga kanajin zafi” akufule yace “namiki kala da abin tausayi?” Girgizamai kai tayi sai ta turomai baki ta kwabe fuska zatai kuka dauke kai kawai yayi yace “cigaba” dasauri tacigaba tai maza tagama ta manna bandage awajen sannan tazo wajen hannunsa takalla ya kone sosai a hannun yama fara bororo, bala’in tausayi yabata, tasan kawai dan shi namiji ne yasa yadaure amman a konaka haka da bala’in zafi gashi yayi bororo, sheshekan kuka dayaji yasa yajuyo da fuskansa gently, yarinyar yaga ta tasa hannunsa agaba tana kallo tana kuka batare data taba hannun ba, sai yayi shiru kawai yana kallonta sai kuka take tana gogewa da bayan hannu, calmly yace “ahaka zaki zama Nurse?” Kaman jira take tafashe da kukan da kyau cikin kukan tace “banson naga anacin zalin mutum, sabida sunga bakada karfi kai kadaine su sunada yawa saisu azabatar dakai haka, kaga nataba konewa akafa” dawani irin sauri ta gyara zama ta daga kafar damanta tazare white sock na kafan da sauri tanuna mai wata yar karaman tabo haka na kuna, kafanta very clean ga dogayen yatsu looking damn beautiful dan akwai ragowan jan kunshi akansu tace “lokacin Mama na koyamin girki tace na tafasa wake naje zan juya ruwan ya zubemin akafa saida nayi kwana bakwai ina kuka sabida zafi, kaiko wuta fa suka samaka nasan kalan azaban wlh, is not fair sai Allah ya sakamaka” he’s in extreme pain da maybe da wanine da yanzu yasume sau uku, but shirme da surutun this little girl is diverting attention nasa, on a scale of 10 tasa he’s only feeling 4% azaba, ganin da gaske kukan take yasa gently yace “stop crying and treat me Miss Nurse” washemai baki tayi tace “kaika fara kirana Nurse amman Nurse Safeerah zakace, sunana Safeerah Shu’ibu idan na girma na bude asibiti na ai zaka dinga zuwa ina dubaka ko, nine nurse dinku ko”? Gyadamata kai yayi kadan alamun eh, zuman ta dauka tace “dana gama school danayi admitting naka ma ni, but bakomi zan gayama Mama yau nasami first patient” tabude zumansu tashiga shafawa ahankali kai tsaye batare dataji wani tsorobae idanunsa a lumshe amman hakanan yabude kadan yadan kalleta tana shafamai zuman hawaye na ciko mata a idanu, kasan the thing is hurting her, saikuma ta turo baki irin na yara dake jin tausayin abu tasake fashewa da kuka mara sauri, for the first time sai yayi murmushi dudda yanajin azaba yace “abinda aka koya muku a school din kenan, kina treating patients kina kuka”? Dasauri ta kallesa saitakai bayan hannu ta goge fuskanta tass tace “banso naga an zalinci wani, kaji proper hospital duk sai an cire skin dinnan, hannunka zai zama mai tabo, kayakuri kaji”gyadamata kai yayi yamike tsaye dasauri ta mike tace “ina zaka?” “Zan tafi” ya amsa batare daya kalleta ba dasauri ta shiga gabansa tana zaro idanu tace “suna nan ko’ina su Anas Magu, dan Allah karkaje kabari Baba yadawo saiya fadi yanda za’ayi ya fitar dakai batare da an ganeka ba” shiru yayi yace “aramin wayanki i lost mine” ahankali tace “banda waya Baba yace naci jamb zai siyamin nafara university da waya” kallonta yayi sai yadan