a murmushi sosai samin kansa yayi da sakinma Waleed full smile Waleed ya washe baki yana nunama Salim cheese balls, daukan masa cheese balls yayi yabude yabasa ya karba yafara ci sannan Salim yakalli matan dake wajen yace “I want kids food for him” hadomai abinci akayi daban daban, yasayamai sweet da cheese balls pack, juice da biscuit yabada card yabiya, ma’aikatan wajen na fitowa da kayan yazo yabude motan aka samai komi a back sit sannan ya shigo yazauna, Safeerah takalli su adan hankali tahada ido da Waleed dakecin cheese duk ya batama Salim rigansa kayansa masu haske amman duk orange orange na cheese ajiki, tama Waleed alamu da hannu dayazo yawani kankame Salim abun yabata mamaki, Salim ya rufo motan yadan kalleta maida kanta kasa tayi, ahankali yace “why were u at the company this night?” Dan shiru tayi sai chan murya chan kasa tace “bakomi” ijiyan zuciya yasauke yace “alright bari na maidake gidan na tambayi Baba meya faru aka miki duka haka a fuska basusan ke mace bace” ya kunna motan dasauri tace “ni……ni bazani gidan nan b…..” takasa karasa maganan sabida rawa da bakinta yafara kuka na neman kufcemata hawaye yazubo mata takai bayan hannunta ta goge fuskanta da sauri muryanta na breaking tace “ni….nidai kabani Waleed nayi tafiyata thank you for everything” takai bakin hijabinta ta daura kan fuskanta sabida bataso Waleed yasan she’s crying yahau kuka shima, dan ijiyan zuciya Salim ya sauke yaja motan dasauri tasauke hijabin takalleshi ahankali tace “ina zaka kaini” shiru yamata bai cemata kala ba takai hijabin tana goge idanunta, Silver garden estate taga sunje yana horn aka bude yashiga estate din yahadu sosai, parking yayi agaban wani gida number 17 dan gidajen duk iri dayane yabude motan rikeda Waleed batare daya kalleta ba yace “when you’re ready come inside” yazaga bayan motan yadauko ledan abincin yawuce yabude kofan yashiga tabisu da kallo a bude yabar mata kofan gidan yahadu na bala’i.
Takai kusan 10mins a motan kuka take, kawai yamata hijacking yaro yakawota wani gida an gayamai ita yar iska ce? She’s not even understanding wats happening, yanzu idan mutumin nan yamata wani abu fa? Dudda he doesn’t look like a bad person but yanzu yazatayi? Inane nan ya kawota ya shige da danta? Meyakema Waleed? Idan shi maye ne ya cinye mata kuruwan d’a fa? Ganin tana tunanin Waleed sosai yasa ta goge fuskanta tass idanunta harsun kumbura tabude kofa tafito tamaida kofan tarufe tashigo gidan, tsoro yahanata kulle kofa, babu kowa a hadadden falon, muryan Waleed taji ta around wajajen dinning datake kyautata kitchen ne hakan yasa tawuce wajen asanyaye jikinta yayi sanyi duka tabude kofan hakan yasa ta hangosu yadaura Waleed kan island na kitchen din shi yana tsaye yana basa abinci Waleed naci sosai yanamai murmushi tabi kitchen din da kallo garin abincin duk ya zube a kasa da kwalayen abincin, kitchen din looks so messy kana gani kasan bai saba yi ba maybe ma this is the first time yake bama yaro abinci, for the first time ta tsaresa da idanu tun shekaran jiya data fara ganinsa he’s so gentle with Waleed, kaman yasan Waleed from somewhere, you Waleed means something to him, is not easy kabama stranger this care, who is he? Bata taba ganin Waleed ya yarda da stranger easily ba sai shi, yana basa yana goge masa kumatu yana masa murmushi hakan yasa Waleed nata murmushi, fresh hawaye taji sun zo mata dasauri takai bayan hannu ta goge su, ruwa yadauka na gora yabude yabama Waleed ya sha ya ijiye komi yasa hannu yadaukesa yajuyo ganinta yayi tsaye jikin kofa tana share hawaye da bayan hannu bamata san yana kallonta ba, wani irin radadi yaji zuciyansa namasa ganin the happiest girl daya sani back then is the saddest girl today and someone dares hit her, there’s this thing he feels about Safeerah he feels kaman ya maida problems nata kansa and just solve everything for her, shafa bayan Waleed yashiga yi yaron yayi gyatsa tareda yin lamooo ajikinsa bacci yayi awon gaba da shi daman yunwa yasa ya farka, dagokai tayi ta kallesa suka hada ido dauke kanta tayi dasauri, tahowa ya shigayi hakan yasa ta matsa gefe wucewa yayi yafito tabiyosa yahau staircase saita kasa hawa kawai saita fashe da kuka dan at this junction takasa rikewa. “Please kabani d’ana mutafi, I’m not one of those girls dake kwana gidan maza, ni kabani Waleed natafi ni ba yar iska bace” dudda yaji all she said but ko alamun tsayawa baiyiba yakarasa hawa tafashe da kuka da kyau tabisu da kallo takasa hawa benen karya mata wani abu, kwantar da Waleed yayi kan lafiyayan gado yaja bargo yarufa masa sannan yafito tareda rufo kofa har lokacin tana tsaye awajen tana kuka, saiya shiga saukowa akarshen stairs din ya tsaya yadan kalleta yace “I’m going home you can stay here as long as you want” ahankali tadago kanta ta kallesa hada idanu sukayi kasa jurewa tayi ta maida kanta kasa, anatse yace “idan na fita kizo ki kulle kofa ki sa key da sakata” yazaro wani phone daga aljihun wandonsa y