NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 37 of 69

a tai shewa tace “time up yau zamuga karshen fitsararra” Momma tadaga wayanta takai kunne tace “kuzo gidana yanzun nan” while Mama na faman jijjiga Baba daya sume sukaji ana bude gate wasu maza na shigowa guda biyar dasauri Mama ta ijiye Baba ta taho kawai takama hannun Safeerah taboyeta abayanta tana kallon mazan dasuka shigo dakin yan shaye shaye Momma tace “idan yarki batabar gidan nan ba wlh saina bawa yaran nan ita sun gamamin da ita ke kuma ba inda zaki zauna ki kula da mijinki dan kinsan babu wanda zai muku wahala” hankalin Mama na atashe tace “kimana rai Mama Kubra, ina Safeerah zata, ke Safeerah bata hakuri” cikeda rigima da taurin kai tace “ko wuka za’a samin a wuya bazan bata hakuri ba” make kanta Mama tayi tafashe da kuka tace “Safeerah ni kikema haka iyyee ni”Momma tace “kucimin uban yarinyar nan in bata fita ba” dasauri Mama takama Safeerah dake kuka gam abayanta tace “zata fita” tafito da ita waje mazan na biyosu tayi kofar gida da ita takalli yarinyar sai tace “mesa kikemin haka Safeerah? Yau kin batamin rai i will not forgive you easily”? Cikin kuka tana shesheka da zuciya tace “Wlh wlh Mama saina cireku daga gidan nan, bazan taba yadena Matar nan ba she’s very wicked” shiru Mama tayi tana kallonta tace “yanzu ina zaki? I can’t live Babanki haka baida lpy, kinada kawa a hostel na school dinku ne?” Girgiza mata kai tayi alamun a’a sai Mama tace “toh ina zaki dakiketa fada yarinyar sai shegen zuciya irin na su mutanen farko”? Shiru Safeerah tayi tana shesheka sai chan tace “zanje company danake IT akwai masallaci zan shiga na kwana awajen, Mama don’t worry babu abinda zai sameni just take care of Baba, Allah zai bani yanda zanyi, I will arrange something mukoma Kano” Mama tai shiru tana kallonta kaman ta rungumeta taita kuka, saita warware zaninta tamika mata 2k tace “kije Allah ya tsareminke babu abinda zai sameki, Allah ya kareku keda Waleed, kafin gobe Babanki ya farfado zamu lallaba Momma kidawo” girgizama Mama kai tayi tace “Wlh bazan dawo ba Mama nagaya muku, kuma kuma saikunbar gidan nan” hannuwanta Mama takama saita shiga dukan hannuwan bada wani zafi ba tace “taurin kanki da zuciyanki yayi yawa fa Safeerah kina mace, mehaka iyye kalli matsalan dakika sake sakamu ciki again” “Malama ana nemanki ciki”gardawan suka tsaya kan Mama, daya cikinsu ya kalli Safeerah yace “bar unguwan nan” goge fuska Mama tayi tajuya takoma ciki Safeerah tajuya dasauri tashiga tafiya kirjinta bugawa yake sosai, tanayi tana share hawaye today is one of the saddest day of her life, take cewa company su inda just jiyan nan tafara aiki how sure is she ma za’a barta ta shiga ciki? Jijjiga Waleed dake kuka abayanta tadinga yi harta fita tahau keke zuwa junction ta tare mota tashiga sannan Waleed yayi shiru kaman yayi bacci . Around 8:30 tasauka bakin junction tashiga takawa da kafa tana addu’a Allah sa abarta ta shiga, Allah daurata kan koma waye ke gadin, hartakai company wani dattijon security ne ke gadi ya tsareta agaban gate yana ganinta ya ganeta yace “Hajiya me kike nema? Me kikazo nema”? Ahankali tana saita muryanta daya koma kaman ta kamu da mura sabida kuka tace “na manta da key na a office namu dan Allah inaso na shiga na dauko” kallonta yayi ga goyo dayagani abayanta yace “can I see baby dake bayanki”? Gyadamai kai tayi ta juya ta daga hijabinta sama tace “d’ana ne” Waleed ya kalla dake bacci yana kara haskasa da touchlight yace “okay zaki iya shiga” yabude mata gate tawuce ciki yabita da kallo yana tunani, rayuwa sai ahankali mutane are fighting one battle or the other, ba yaune farko da zakaga wani ma’aikaci yadawo company ya kwana ba, people are facing problem, from face nata yaga alamun mari ga kumburin baki harda dan jini idanu sunyi jajir hawaye ma basu gama bushewa ba, maybe mijinta yamata duka tazo nan ta kwana kafin gobe ta nemi option, if he can help her by letting her sleep why not, she’s just lucky shine on post da abokin aikinsa ne da bazata shiga ba. Wucewa reception tayi tabude kofa ahankali akwai wuta awajen tawuce kofar mosque tabude ahankali ta shiga ta taba bango ta kukkunna wuta tashiga masallacin tawuce bangaren mata shima ta kunna wuta tashiga daga hijabinta ta kwanto Waleed dake bacci sosai ta rungumeshi a jikinta ta zare zanin ta shinfida awajen sannan ta kwantar dashi ahankali tana sauke ijiyan zuciya tana kallonsa hawaye na cika idanunta yanzu zuciyanta ke kara breaking sabida Waleed, wat is she gonna do yanzu? Ta ina zata fara? Yaya zatayi da Waleed? Sai kawai ta rushe da kuka tana yaushe bakinta cus Waleed na ji zai farka. Wuraren 8 yayi parking motarsa a compound dinsu yayi shiruu batare daya kashe motan ba ya lumshe idanu kawai, yakai sama da 20mins ahaka sai kawai yabude idanunsa yadan gyara zamansa yasa hannu yadauki wata iPad dake dayan seat na gaban motan kawai yayi logging in portal na company su yashiga CCTV to be honest baimasan mesa yayi ba wlh, ya
🏠