tashiga mota zuwa area su tashiga Keke daya kaita bakin GRA din aka sauketa abakin layinsu sannan ta sauka tashiga tafiya tana goye da jakan bayanta sai ledan hannunta da pampers ke ciki da abincin gwangwani tana tafiya taga an bude gate na gidansu motan Ramla yafito wuceta Ramla tayi fit da mugun gudu, Safeerah ta tabe baki aranta tace “aikin kenan” tawuce gida abinsu awaje taga Baba tai murmushi tabude ledan tadauki tomtom guda uku tace “Baba na sayo maka tomtom a kasuwa” murmushi yayi ya karba yace “ke Mamana kudin dazamu lallaba mu siama Waleed abinci kike sayamin tomtom, yanzu abinci guda nawa kika iya kika saya da kudin”? Murmushi tayi tace “madara da cerelac sai pampers, karka damu Baba zamuyi managing su kuma namayi tunani Baba mudena biyewa Waleed ya koyi cin abinci gaskiya lokaci yayi Baba, idan yawuni bai sami abincinsa ba zaici abinda aka dafa agida” hade giran sama da kasa Baba yayi yace “dako na sassaba miki karki kuskura kiyi haka, yaro ne nan gaba aka basa abincin yaran ma bazai karba ba, komi lokaci ne karki takura sa” dan murmushi tayi tace “ni shikenan Waleed ya kwacemin Babana” dariya Baba yayi sosai yace “Mamana daban ne araina, Safeerah na yar albarka, Allah ya haska rayuwanki” ahankali tace “Ameen Baba nagode” “shiga gida toh” wucewa tayi tabude gate ta shiga,
Baba da Mama na mugun son Waleed, dakinsu na gate tashiga ta ijiye ledan tarage kayan jikinta tafada bayi wanka tayi dayake yau batajin yunwa ba abinci tafara nema ba, fitowa tayi ta shirya cikin wata simple gown na atampa saita dauki hijabinta dake nan kan dadduma dark blue har kasa tasaka tafito tasaka slippers tawuce cikin gidan tabude kofa tashiga flat dinsu, Momma ne kadai a falo tana waya tanacin fruits ko kallon Safeerah batayi ba, wucewa gabanta Safeerah tayi ta duka har kasa murya kasa kasa ganin tana waya tace “Momma ina yini sannu da hutawa” da hannu tamata alamu tabar gabanta hakan yasa ta mike tawuce kitchen, Mama tagani tana aiki ga kofan backyard a bude, Waleed na wajen yana wasa da ball kagansa a tsaftace fess yasaka wani short green da riga yellow, ga takalmi akafansa mai igiya yana wasa abinsa tace “Mama sannu da aiki” Mama tace “ya aiki an dawo, ga kulan abincin ki dauka kije kici” gyadama Mama kai tayi tasa hannu tadauka tadauki spoon saita wuce itama tafita Waleed na ganinta yayi ihu yana sakin kwallon yace “Ummyyyy” hannu ta budemai tana murmushi sosai tace “oyoyoo Waleed din Ummy” tahowa yayi da gudu ya rungumeta ta daukeshi tace “yau kwallo ake bugawa, zomuci abinci” ta zauna kan tabarman dake wajen ta sanyashi akan kafanta tabude kulan taliya aka dafa tadebo takai bakinshi juyar da fuska yayi yaki amsa saima yashiga kokarin tashi daga jikinta tace “zamuyi fada fa Waleed” tasakesa tashi yayi yacigaba da ball abinsa tanaci tana kallonsa tana cewa karage gudu Waleed, tass tagama tamike tadawo kitchen ta ijiye ma Mama kujera murya kasa kasa kar ajiyosu tace “zauna ki huta nadawo Mamana” babu abinda bata iya dafawa ba ita tai abincin dare fried rice, grill fish, sai salad da juice takawo dinning tsaf, suka fito nan backyard sukai alwala sukai salla a tarbarman dan saura goge kitchen duk zatayi, tana idarwa tadawo kitchen ta wanke komi ta goge komi tashiga mopping Mama tadauko Waleed suka shigo ciki cus sauro awaje ta maida kitchen tarufe. “Safeerah! Maryama!” Sukaji Momma takirasu faduwa sosai gaban Mama yayi tace “na’am” tawuce tabude kofa Safeerah taja hijab dinta daga kan kofa tasaka suka fito, Momma suka gani a falon tahada rai sosai kaman bata taba murmushi aduniya ba, ga Salma zaune kusada ita tana murmushi saiga ledan kasuwa na pampers da madara da cerelac agaban Momma, ran Momma abace tace “tashi kije ki kiramin Shu’ibu Salma” tashi Salma tayi tawuce tafita, Waleed yayi lamo jikin Mama dan da Momma da Salma da Shamsu tsoronsu yakeji baya sonsu ko kadan sabida they’re not nice to him, karamin motsi zaiyi agabansu su mammakesa, shigowa Salma tayi Baba biyeda ita yaga Mama da Safeerah tsaye charko charko gabansa yafadi yataho da dan damuwa yace “gani Mama Kubra meya faru”? “Ubanka ne yafaru Shashasha kawai! Solobiyo!” Salma ta tuntsire da dariya sosai abinta dan zagin da Momma ta zubamai ya mugun mugun bata dariya, ran Safeerah yafara zafi ganin zagin da akama ubanta Salma na dariya amman dai tayi shiru bataso tai abinda za’a kara musu zagi, strictly Momma ta kalli Safeerah tace “nasan rabonki da d’a namiji tun kina shekaru shashida aduniya, watanki shidda gidan Abbati ya sakoki, so nasan jiki da jini kin fara bukatan abun ne”? Ahankali Baba da maganan batamai dadi a kunne ba yace “Subhanallahi wace kalan magana ce wannan Yaya Kubra”? Momma hayayyakowa tayi tace “wlh ka kara magana anan wajen saina tashi na yanka mata mari wawa kawai langahuhuu!” Kwashewa da dariya Salma tayi harda faduwa akan kujera tana rike ciki tace “Momma Innalillahi kin iya well deserved zagi, this ur brother kam yayi ka