ama shi take kallo yawani kara kyau looking damn fresh weather China yamai kyau, so take yazauna kusada ita abakin gadon amman yana tsaye kaman soja oh sojan ne fa, ahankali tace “kazauna Babe” girgiza mata kai yayi yace “no I’m okay like this” zuciyanta bai mata dadi ba ahankali tace “sorry I know kana wajen aiki i made you worry” calmly yace “just focus on yourself ba matsala” gyadamai kai tayi tai lamo she’s just thinking of mezatayi that will make him come to her she wants to somehow cire veil nata atampan data saka ana ganin boobs nata sosai dan wuyan rigan yasauko kasa sosai, ringing wayansa yayi hakan yasa yakai hannunsa aljihun wanda yaciro wayan ganin KB ne yasa yakai wayan kunnensa yace “wats the outcome KB”? Dan ijiyan zuciya tasauke jin da namiji yake magana ba mace ba takai hannunta tadan ja gyalenta yafadi awuyanta tana wani serious juyawa gyalen zai rabu da ita yafice daga jikinta, gashinta a tsefe ba laifi tayi parking nasa an tsaga an raba biyu tasha relaxer abinta jin yana magana kaman he’s ending the call yasa tawani kama cikinta ta tashi zaune ta kifa kanta a guiwa tayi wani nishi datasa ya katse wayan yadan duko da kansa gently yace “Nan……” bai karasa kiran sunan nataba sabida yanda Nanah tadago kawai tayi hugging nashi gyalenta na fadawa gefe kawai tafashe da kuka sosai tace “Babe zan mutu ciwoooo” shifa wani irin mutum ne bayason any form of body contact da matan daba muharraman sa ba even though Nanah zai aura batariga tazama matarsa ba hannayenta yakama yacirota daga jikinsa yace “just lay down hold on lemme get the doctor” ya kwantar da ita duk tana kallonsa ko sau daya bai kalli kirjinta ba, da kyar ta kwanta yajuya kawai yafice daga dakin ran Nanah yamata ba dadi instead of yayi hugging nata back and pet her mtsww waje yafita yakira Doctor da kansa sannan yadaga waya Mom yakira tana dauka yace “Mom can you call Maman Nanah she’s in the hospital sick no one is here” dasauri Mom tace “ohh no how is she wait bari na fara kiran Mamanta tukunna” ya katse wayan bai kara komawa dakin ba har saida wata mata tashigo asibitin, Lecturer ce tana sanye da lace ubansu tana ganin Salim tace “ohh sannu da kokari Salim yanzu kana tsaka da aiki ta dagoka” sauke kansa kasa yayi yace “bakomi yanzu zan koma zan dawo anjima idan ba’a sallameta ba Allah kara sauki” kafin tayi magana yawuce John yabisa abaya murmushi matan tayi tawuce dakin tana bude kofa suka hada ido da Nanah dasauri tace “ina mijina Mommy”? Maida kofa tayi ta taho wajen gadon tace “yatafi yace idan ba’a salameki zuwa anjima ba zai dawo” dan tsaki tayi ta cisge drip din Mamanta na kallonta saikuma kai tsaye tace “bangane ba Nana Khadija me kikeyi haka?” Dan turo baki tayi tace “ni lafiya na kalau da Besty nahada baki” “and why did u do that Nanah”? Akufule tace “Toh Mommy tun yaushe yadawo yaki zuwa yaganni, Mommy he’s not romantic at all, baya nan nan dani, kullum nike kiransa, he acts so cold towards me, kawai i just wanted his attention and affection saisa” ran Mommy baci yayi tace “to dan you wanted his attention sai kibi ta route din rashin lafiya? Are you okay kuwa at all Nana?” Kaman zatai kuka tace “Mommy baya rawan jiki akaina fa saini” dakuwa Mommytamata tace “kinci ubanki kaga yarinya kin dauka kowa ya iya shirmen hauakan nan nan da mata? Akwai abinda kika rasa? Kin taba cemai kinason abu baiyiba”? Nana ta girgiza kai, Mommy tace “bada baki daya kikace kina asibiti yazo ba kafin yan uwanki ma suzo yabar aikinsa jibesa da uniform ajiki akwai care and affection dayafi haka? Ku yaran zamani sai kunga maza na kawo flowers yana tura that long epistle of love message shine so ko well guess wat Nana? Men like Salim don’t have that time, he’s rich I mean wealthy with a successful career, sannan shiba yaro bane dazai dinga wasting tima nasa unnecessary nonsense, kawai, yau duka duka bikin naku saura 14days, kika kara gwada abu haka saina saba miki wlh tashi mutafi wawiya kawai” tashi tayi ta yafa gyalenta suka fito sukaje office na Besty ta Rahama itama Mommy ta wanke ta tass sannan tace “nawa bill din”? Rahma tace “ai yabiya komi” Mommy takalli Nanah datai smiling tace “you see harda boba tea yasiya miki” tanuna hannunta dake rike da Boba tea tace “you don’t know how lucky u are nonsense girl” suka wuce suka tafi.
EPISODE 1️⃣6️⃣
Karfe 4 na yamma daidai suka tashi Safeerah tafito yau saida ta tsaya tai sallan la’asar sannan tafito tasa kafa ahanya, tana fita bakin express tasami motan Wuse market ta shiga da sauri suka tafi she knows Wuse Market sabida itada Mama suna zuwa chefanen kayan abinci duk karshen wata, shiga tayi tafara tsayawa tacire kudin account nata tass sannan taje shagon yaran just cerelac ta iya siyamai da Aptamil sai tasaimai pampers mai guda 24 kudin yakare tass sai 3k dazatayi transport komawa gida dashi dakuma zuwa aiki gobe ko 30min bata bata a kasuwan ba tafito