NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 30 of 69

itama tafashe da kuka tace “Safeerah yakikeso nayi eh? Ina kikeso nasa kaina naji dadi? Ni yar rikoce banmasan iyayena ba Babana yarasu kafin ahaifeni mahaifiyata wajen haihuwana tarasu yar rikoce wajen yan uwan Babana, wahalan danasha wajensu bana shan kalansa anan, mahaifinki shiya ceceni ya aureni sukace sun yafeni banda kowa sai mahaifinki duk inda zaisa kafa zan saka tawa sabida yabani gatan daban taba samun kalansa aduniya ba, wannan shine hallaci duk runtsi duk wahala ina tareda shi, dagani har mahaifinki sabida ke muke zaune anan nothing is important arayuwanmu face ke da Waleed as long as zaman mu anan zaisa ki cigaba da samun education Waleed na samin abinci da kulawa fakat mu karmu samu mun hakura bakomi, stop crying we are doing this for you, no condition is parmanent watarana sai labari, zagi da cin mutunci baya kari, dan Salma ko Shamsu ko mahaifiyarsu sun zageni it’s okay, watarana ko ance suyi bazasuyi ba, abinda nakeso is just focus on school naki, kigama IT dinki and become somebody, as for Waleed zan kula miki dashi as long as I’m alive kinji, please karki bari Babanki yaji maganganun nan kar BP sa yatashi ya isa zo nan yarinya na nasan badadi ana zagin miki iyaye amman kiyakuri kinji Feerah na” Mama ta rungumota zuwa jikinta lamo tayi jikin Mama haka shima Waleed yayi lamo yana kallon mahaifiyar tasa dake kuka Baba yadade gaban dakin tsaye dan yaji komi sai kawai yawuce yakoma waje yabuga tagumi, yasan watarana sai labari shi bayajin kyashin yima yayarsa Kubra komi sabida takula da lafiyarsa, tasaka yarsa a makaranta da sauransu, kawai baitaba sani yayarsa Uwa daya Uba daya zata iya maidashi mara daraja dan aiki mai wanke mota ba da gadi tana zaginsa da cimasa mutunci gaban iyalansa ba, shi yasan da shine mai hali Kubra tazo garesa bazai taba maida rayuwanta haka ba, zai iya kwashe iyalansa sunbar nan ba but tunaninsa shine aikin me zai samu baya gani? Tayaya zai rikesu? Mama Kubra ta cutar dashi sosai kawai baiso yayi magana ne sabida zumunci amman bazai taba mance lalata yaruwan yarsa datayi ba ta auramata dan shaye shaye mai duka. Basu dawo gidan ba sai wajen 12 tuni Safeerah tai bacci anan falo shima Waleed haka, Baba yafito daga uwardaka yafito yazo yabude musu gate, driver ke tuka Momma da Salma dake baya suka shigo ya maida gate yarufe yabiyo motan Momma ta sauko yace “sannu da zuwa Mama Kubra” kallonsa tayi sannan takalli driver ta tace “kai zaka koma BQ yanzu” cike da girmamawa yace “toh Hajiya” Salma tayi gaba batare data gaida Baba ba tace “ka daukomin kayan dinki na a boot” Momma tace “ka tsaya kana kallona bakaji abinda Salma tace bane” ahankali yace “naji” bude booth yayi yadauki jakan dinki yawuce flat Momma biye da shi har bene yashiga hawa Momma tace “nasan ba hankali gareka ba ka ijiye agaban dakinta baka shigo ba” daga ciki Salma tai kwafa tace “yashigomin daki bana gaura masa mari ba hmmmm” Baba baice komiba yawuce ya ijiye gaban dakin Momma tayi dakinta tace “ka kashe wutan ko’ina” anatse yace “toh” Yasauka yakashe wuta yawuce yafita. EPISODE 1️⃣5️⃣ Washe gari da sassafe Safeerah ta tashi ance ba’ason latti bayan tai salla ta taho flat tas tashiga share share tana azkar ahaka ta gyara ko’ina tasa turare 7 har yayi Mama tace “maza jeki wanka” wucewa tayi taje tai wanka wani black abaya tasaka yau is simple abaya babu wani kwalliya ajikinsa dan stones dake jiki sun dade da fita tun na akwatinta ne shima rigan, closed abaya ne black but a goge, tasaka wasu hook earings farare masu kyau Mamane tasayo mata su a kasuwa, batama tsaya gyara gashinta ba gyalen kawai tayafa aka tadauki jakan bayanta ta goya tafito she smells good very mild, Mama tries dasai mata yan turaruka da khumra haka da yan kudinta tasaka flat shoe black tafito, wucewa tayi zataje flat Baba dake shigowa gidan baiso yauma takara tafiya da bakin ciki yace “wuce kitafi” dasauri tajuyo tace “Baba ina kwana” hannunsa yasa a aljihu yaciro 10k yamika mata yace “gashi ki hada da wanda mamanki tabaki ki sayoma Waleed abinci da pampers saiki cire na mota kisai abinci kuma kici” murmushi tayi tace “toh Baba nagode Allah kara bude, jama’a Babana yafi nakowa principal Baba” dariya Baba yayi yace “uhmm Principal da ba idanu yanzu” murmushi tayi tace “da nazama Nurse dana maka magani” yanayin fuskan Baba chanzawa yayi sabida burinsa kenan Safeerah tazama Nurse, wucewa Safeerah tayi tafice yabita ya tsaya a kofar gida tafiya tayi harta fita wajen layinsu tasami keke tahau yakaita bakın junction tasami mota yakaita har layin wajen aikin sannan tatako daga junction zuwa company 8:05AM tashigo kampanin kafin takai ciki was 8:09 zatai hanyar office nasu receptionist tace “you need to sign in Miss Safeerah” gyadamata kai tayi tazo tai signing receptionist din na kallonta ahankali tace “you’re very pretty Miss, I love this plenty hair on your forehead” kallonta Safeerah tayi sai kuma akunyace tace “thanks” ta
🏠