NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 29 of 69

a” wucewa tajuya zatayi karaf suka hada ido hakan yasa ta duka tadauki paper bag din ahankali, Baba yace “wani Salim ne bawan Allah me kake nema wajen Safeerah ince badai cutar da ita zakayi ba ko? Koko fada ta nemo”? Dasauri Salim yace “a’a Baba, narage mata hanya ne kawai, wajen aikin mu babu abin hawa” dan ijiyan zuciya Baba yasauke yace “owooo toh Alhamdulillah, nagode Allah maka Albarka, mantuwa nayi dayake Yayanta yakaita ban ganta kafin ta tafiba so ban bata kudin mota ba, nagode nagode” gyadamai kai Salim yayi yay shiru yana kallon Baba he felt very very terrible and responsible for condition nasa saiya kasa motsi, ahankali Baba yace “Salim” tashi yayi daga duken dayake ahankali yabawa Baba hannu yace “sai anjiman mu Baba” Baba yayi murmushi yace “mujima lpy, nagode Allah yayi Albarka”. BQ dinsu tawuce ga mamakinta saitaga furnitures na ciki na nan but kayan sawansu babu badai da gaske an maidasu wajen masu gadi ba, ko saisa taga Baba ma awaje har an sallami masu gadin? Wucewa tayi flat din tana bude kofa taga Waleed shi kadai yana wasa a falo ga remote a hannunsa duk sanda taga Waleed ahaka only means yan gidan basanan yana ganinta ya washe mata baki yataho da gudu itama haka tace “oyoyooo Waleeeeee” tawani daukeshi sama yace “Ummyyyyy ayoyoooo” fitowa Mama tayi tace “an dawo yan IT”? Dariya Safeerah tayi tana sauke Waleed tace “Mama nadawo ya kuke”? Mama tace “baki ganmu ba lafiyanmu kalau, jeki wanka, muna gate yanzu” kallon Mama tayi dasauri zatai magana Mama kawai tajuya takoma kitchen alamun batason maganan, shiru tayi saikuma ta kalli Waleed tace “kawo remote din muje daki muci abinci ko” bata yayi ta ijiye tadauki jakanta da paper bag din tafito tawuce gate tabude dakin tashiga falo ne da uwardaka sai bayi falon ga katifar Baba da Mama sai falo katifarta ga gwangwanayen abincin Waleed awajen ga kayanta a ghana masgo dan babu wardrobe anan jin ranta zai baci yasa kawai ta zauna tare da Waleed tashiga bayi ta wanke hannunta tace “at least I’m grateful for this food ko Waleed” yaron yace “eh” murmushi tayi tabude Chinese rice ne sai Nan bread, humus da curry soup, sai turkey, salad da pinacolada murmushi tayi tace abincin yan gayu debo rice tayi takai bakin Waleed tace “ci” kin ci yayi ya kauda kai sai ta gutsuro Nan bread tabasa ya karba yahauci tafara ci ba wasa yunwa takeji, ita da Waleed suka shanye juice din dadi tabar ma Mama Nan bread da soup din tawuce bayi tayo alwala tazo tai la’asar ta chanza kaya tadauki Waleed suka fito sukazo kitchen ta taya Mama aiki suka gama komi suka kara gyara ko’ina sukasa turare, sannan suka fito suka koma flat dinsu tace “Mama ganaki” kallon abincin Mama tayi tace “waya siya miki abinci?” Ahankali tace “Oganmu” anatse Mama tace “mesa? Yasanki ne”? Girgizama Mama kai tayi tabata labarin yanda batada kudin mota da komi, Mama tace “inada 20k idan zaki tafi gobe saina baki saiki hada da 15k dinki ki samowa Waleed dan abincin daya sawwaka da pampers ko irin me guda goman nan ne” shiru tayi ta tsare Mama da idanu tana kallonta, Mama tace “menene kike kallona haka?” Hannun Mama takama ta jujjuya tana kallon uban shedan yanka wasu sun warke wasu basu warke ba, takai hannunta ta taba kashin wuyan Mama, da fuskanta da duk yayi wrinkles, sai hawaye yafado idanunta dasauri Mama takai hannu ta share mata tace “zaki fara yauma ko? Kina wani duddubani kaman patient, duk randa kike neman kuka abinda kikeyi kenan” Lips dinta ne suka fara rawa tace “Mama na tambayi wajen IT ko zasu bani aiki parmanently na tara albashina na kama mana gida mubar nan?” Tsareta Mama tai da idanu sai kuma tai murmushi ganin yarinta tace “yaro man kaza, shi aikin dakike magana akai ba su suka samo miki ba”? Ahankali tace “eh dudda haka amman ai basune masu kampanin ba” Mama tai murmushi tace “ko dubu dari ake biyanki bazaki iya rikemu ba Safeerah mubar maganan ma dan Allah, kinyi tunanin makarantan ki? Mahaifinki duk wata wata yake zuwa checkup na idanu da hawan jini, ga Waleed very soon zai shiga 3yrs za’a sashi makaranta dole, abincin sa fa, pampers waye waye, I know kin damu but u can’t do this Safeerah!” Rushewa da kuka sosai Safeerah tayi dayasa Waleed yazo wajen da gudu yana leko fuskanta Mama tace “wai me haka Safeerah kinga zakisa yaron nan kuka ko zo Waleed” Mama ta daukeshi yafashe da kuka yana kallon Safeerah data kasa daina kuka, Mama tace “wlh banson wannan halin kawai saiki tasani agaba kina kuka ba’a miki komi ba eh” cikin kuka Safeerah tace “Mama nagaji da ganinki ahaka nagaji, kullum daga safe har dare aiki kike, kin zama yar aikin wasu da ba’a miki godiya sai zagi da cin mutunci, while Baba an maidashi mai gadi da wanke mota ana zagin mahaifina kullum agabana, Mama mubar nan ko barane muje muyi yafimin da this life we are doing here, school din banaso lets leave Mama dan Allah” Safeerah kuka Waleed kuma Mama tama rasa wazata lallasa sai kawai
🏠