u Mama takeji kuma harda bataso taja musu fitina dasaitama Salma dukan da akace ta zagi Baba bazata karaba, marasa tarbiya kawai da girmama na gaba dasu, she hated gidansu na Kano sabida yan daban anguwansu but yanzu she rather lives there sau dubu da wannan rayuwan gidan na Abuja wani kalan kaskanci iyayenta ke facing? Zata nemi aiki da zai taimaka mata tarike iyayenta da danta, saikuma tai shiru nawa ne kama haya? Nawa abinci? Asibitin Baba, abincin Waleed? How can she do all of those? Itada batada any qualification, takai almost 20min kuka take sannan ta tashi ahankali ganin seven yayi tawuce dakinsu tabude kofa ta kalli gado Waleed na bacci abinsa zuwa gaban gadon tayi ta duka takai hannunta tashafa kan Waleed murya chan kasa tace “Waleed pray for Ummy kaji! I don’t want this life for you my Baby” tai maganan ahankali takai dayan hannunta ta goge fuskanta sannan ta mike tawuce bayi ta watsa ruwa a gurguje tafito Vaseline nata ta shafa ta warware gashinta da sauri gashin yazubo saura baifi 2inches yakai waist nata ba gashin baki sosai ta shafa man kitso tadan taje sannan tasake packing tai donut da bakin sannan tabude sip din tanada tufafi ba laifi tun na akwatin ta na zamanin aurenta ne, wani blue atampa tadauko gown aka maga ta saka sannan ta dauki sky blue gyale mai duwatsu masu kyau babba taciro sannan tayi dauri taciro file na credentials nata datai photocopy tadauki bagpack nata tasaka sannan tasaka flat shoe tafesa body spray nata mai dadin gaske tafito, tajuyo ganin Waleed na bacci still tafito tabude kofa tafito tsakar gida tayi kyau sosai wlh gata da tsayi ba sosai ba dai, she looks so good, flat din tawuce tabude kofa ahankali Momma tagani da Shamsu suna zaune a dinning suna breakfast ya shirya tsaf cikin kananun kaya duk suka kalleta karasawa wajen tayi tace “Ya Shamsu ina kwana” wayansa yadauka da car key yamike yace “muje ke I have somewhere to be kina batamin lokaci” gyadamai kai tayi Mama tafito daga kitchen rikeda kula Safeera tace “natafi Mama” Mama bata kalleta ba gudun kar ace tai laifi tace “adawo lpy” Safeerah tajuya tabisa suka fito compound Baba ya wanke motarsa tsaf yana kara gogewa sai sheki motar take suka taho wajen, yayi murmushi yace “an fito sannu da kokari Shamsu nagode sosai, Safeerah sai an dawo ko, ayi addua, Allah bada sa’a” Ameen Safeerah ta amsa ciki ciki dan fushi take da Baba, Shamsu bai tankaba yashiga motan itama tashiga gaba yaja motan aka bude musu gate suka fice, saida suka shiga kan titi cikeda isa Shamsu yace “saura mukaje ki disgani! This is number one biggest construction company a Nigeria kaman irin su Julius Berger haka suke, suna gina titina, railways, estate etc, this people are bastardly rich, the Maradis kenan! Kudinsu gado sukayi tundaga zamanin kakannin kakanni and gasu all of them are bless, Babansu shine Maradi Jet co yana harkan jirage he’s the only person a Nigeria dake kawo jirage yana saidawa yana bada shatter, sai dansa shine mai Maradi construction din nan Babban Soja ne kaman wasa yabude this construction company boom sun zama global, bama ya iya managing abokina dawani Indian Man Paresh ke mishi managing company, sai kanwarsu Layla tana auren dan shugaban kasan Nigeria sai sisters dinsa biyu da basuyi aure ba lemme even tell u I’m trying to see yanda zan samu daya na aura sabida family mu yazama so powerful but that big brother nasu baya wasa and seems he doesn’t like me, nafara magana da Lubna yahanata tacemin school zatayi she blocked me so dan haka banso ki kofsani, mind your business kiyi aikinki kibar wajen kidawo gida, wlh if you do anything dayasa aka kirani I will kill you Safeerah u hear me” yadaka mata tsawa gyadamai kai tayi tace “naji Ya Shamsu” company sukakai yanada girma tsaresu akayi a gate saida Shamsu yakira Auwal yasa aka barsu suka shiga company is so big ga manya manyan motoci na goni daban daban parked a big space din, parking yayi inda ake parking sannan yafito ahankali Safeerah tabude motan tafito wani iri jikinta yamata saitaji wani irin tsoro da anxiousness irin wanda kakeji din nan idan kaje sabon waje tafiya Shamsu yafara hakan yasa tabisa tana tafiya ahankali suka shiga building din, receptionist ne a lobby din saiga wani status na ginin gida da titi anyi komi me kyau is just a work of art ta tsaya tana kallo Shamsu yafara tafiya jin shiru yasa yajuyo ganin ta tsaya tana kallon abun yasa yaji kaman ya dura mata ashar amman ba dama a kufule yace “Safeerah!” Firgigit Safeera tajuyo da kanta ta kallesa yamata wani mugun kallo ta taho da sauri kanta akasa suka wuce 2nd floor wani office da aka rubuta CEO suka wuce secretary tace “are you Mr Shamsu?” Dasauri Shamsu yace “yes yes” murmushi tayi professionally tace “welcome Sir, Mr Auwal is expecting you” tayi maganan tana bude musu office
Shamsu yace “thank you” ya shige Safeerah biye dashi ta shiga tana zaro manya manyan idanunta tana kallon office din da bata taba ganin me kyau dinsa ba ga wani mutumi